Chapter 2

173 12 2
                                    

The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
               
BOYAYYIYAR ALKARYA(the hidden island )🌄🌄🌄🌄

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  chapter[02]

  bayan yagama surutunne kana ya tuna da inda yake,juyawa yayi da sauri a firgice kana ya saki boyayyiyar ajiyar zuciya sakamakon rashin ganin mahaifiyarsa da bayyiba a wajen,mumushine yasubuce a bakinsa dayaga saka masa matashin kai maimakon cinyar ta dayayi bacci akai,hakan yatuna masa yanda take masa yana yaro in yayi bacci a cinyarta saita saka masa filo ta tafi,tunanin sane yadawo daga gurin mahaifiyarsa zuwa ga firgitaccen mafarkin dayake tayi kwanannan wanda hakan yafara bashi damar saka ayar tambaya akan hakan.tabbas dolene nagano menene maanar wannan abin dolene nagano wacece ke domin wannan abin ba iya mafarki bane kawai,duk wannan magana ya yitane acikin zuciyarsa,sannan yaciza gefen fatar bakinsa kana ya fita daga turakar mahaifiyar tasa.
    *** ***  *** ***   *** ***
    Acikin bakar nahiyar wadda take yamma da kasar khaisira kana kuma guri daya kasance tamkar harmataccen waje ga duk wani halitta daya kasance yana da wani da karamin imani ko tausayi acikin ransa wannan nahiya ba kowacce bace illa nahiyar  DHULKAM wacece take karkashin jagorancin JABALUL ASWAD.jabalul aswad wani tsauni ne acikin nahiyar ta dhulkam wanda idan hatsabibi yasamu ratsa dhulkam to ba tabbacin zaikai izuwa tsibirin jabalul aswad ba,idan kuwa kayi nasarar tsallakewa to ba lallai bane kakai ga fadar dake girke a tsakiyar bakin tsaunin ba.Al 'amarine mai girman gaske wanda yake faruwa tsakanin nahiyar mutane  dakuma nahiyar matsafa wacce take kunshe bakaken matsafa ,mayu ,bokaye da sauransu,haramtacciyar nahiyace wanda duk wanda kagani a wannan waje to yakasance gubane acikin al'umma,ko kuma ya gagara ta hanyar yin abinda doka tahana,sanadiyyar tara irin wannan hallitu a wannan waje sai yazamana nahiyar tazama waje mai hatsari wanda bakowane ke da ikon zuwa wannan wajeba sai yakasance shima shu'umi tamkar mazauna wajen.
Duk da hatsari irin na nahiyar dhulkam bai kama ko rabin karfin bakin tsafin dayake zagaye da tsibirin jabalul aswad ba,wannan tsafi kuwa bakowa yayi sanadinsa sai mamallakin fadar da ta wanzu a tsakiyar tsibirin wato fadar boka GAZAZA da ga shahararriyar mayyar bakanya URAI HILWA wacece ta wanzu kana ta shafe daga doron kasa shekaru da dama dasuka wuce,ita dai wannan fada ta boka gazaza an gina tane da wani irin bakain karfe dayake fidda bakin hayaki marar gushewa ,fadar takasance tana dauke da daula mai tarin yawa amma hakan baisa mai kallo ya kalleta a ta fusakar abun daya dauke masa tunani ba a bangaren burgewa.fadace data ke kunshe da kishiyar abinda ake samu a sauran fadar da muka sani wato (tana dauke matsafan hadimai kana kuma an tsaretane da abubuwa na tsafi dama sauran abinda zai bawa duk wanda ya kalleta.
        *** ***   *** ***  *** ***
  A fadar khasira kuwa cike take da dumbin mutane ma abota daraja,savoda rana ce da duk sanda takewayo masarautar take cika da sauran hakimanta da suke mulkar wani sashe dayake cikin masarautar a bangare daban daban,domin sukawo wani abu daya faru wanda yafi karfinsu ko kuma wani abu dasuke bukata daga babbar masarautar ta khaisira.Wannan hali ko kuma tsari da sarki sharzaman yakafa a masarautar ta khaisira yakar masa farinjini tare da daukaka a duk nahiyar gabaki daya.Sanye yake cikin kaya na sarauta da suka fito da ainihin izzarsa wanda yake karawa al 'ummarsa ganin girmansa kana dakuma haibarsa.
  Bakin tsuntsun daya wanzu a tsakiyar fadar ne yazawo dukkan hankalin mutanen dasuke cikin fadar dama shi kanshi uban gayyar wato sarki sharzaman.Koda bayyanarsa a fadar bai zame ko inaba sai gaban sarki kana ya ajiye bakar takardar datake bakinsa a gaban sarkin,saida sarki yakaremasa kallo cikin nutsuwa"shidai wannan tsuntsu bakine sannan yanada jajayen idanuwa marasa shaawar kallo yanada matsakaicin girma sannan kuma da doguwar jela wadda take da launin ja a karshenta"koda gama hankalta da tsuntsun da mutanen waje sukayi sai sarki ya umarci maga takarda daya dauko sakon daga wajen da tsuntsun ya ajiye,daukar sakon keda wuya da maga takarda yayi sai tsuntsun ya bace a harabar fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a fadar,al amarine daya bawa daukacin mutanen wajen mamaki harma da ta'ajjubi,wanda hakanne ya tabbatar musu dacewa jakadan baya bukatar amsar sakon sa daga wajen wanda ya mika sakon.Saida kowa ya nutsu kafin sarki ya umarci maga takarda da bude sakon domin ganin mai bakar wasikar take kunshe da ita,razanace kana dakuma alamar tambaya a fuskar maga takardar alokacin daya dago yakalli dukkan ilahirin mutanen da suke zaune a fadar,bakomai ne yasashi razana ba illa arba dayayi da abinda wasikar ta kunsa,wanda yasha banban da abubuwan da aka kira da wasika ta kunsa.Dukkan mutane harma da sarki binsa sukayi da kallo na alamar tambaya wanda yasashi bayyanar da abinda shima yayi arba da shi aciki,wasikar nadauke da wani bakin gari wanda aka nannadeshi acikin bakar takardar wanda kowa ya saka ayar tambaya acikin zuciyarsa...tambayar dai itace menene wannan ......?
        *** ***   *** ***   *** ***
Al'amarin yarima samhal kuwa tun lokacin daya bar turakar mahaifiyar tasa bai zame ko inaba sai lambun gidannasu wanda yake keban taccene daya haramta ga sauran mutanen dasuke cikin fada.Zaune yake akan wata kwawatacciyar kujera wanda dayace daga cikin kujerun dasuka zagaye lambun wanda yake dauke da furanni masu ban shaawa dakuma burgewa,duk wanda ya kalleshi a yanzu zai san cewa hakika hankalinsa yatafi ga wani gurine daban bawai tunanin wajen daya ke ba,menene yake damunane me yake faruwa dani wanda hankalina ya gagara gano menene?shin wannan yarinyar wacece?wacce yarinyar kuma ?shine abinda yafito daga bakin mutumin dayake bayansa,tambayar da mutumin da yake bayansa ya masa,shiya bashi tabbacin cewar duk tunanin dayake ko kuma maganar dayake acikin zuciyarsa to a fili yake yinta.
  Zagayo wa mutumin yayi ya zauna a gabansa sannan ya sake tambayarsa"wacece ita wacce kke magana akanta?tukunna ma menene damuwar ka kwannan duk ka sauya samhal.Babu komai FAHSIR(shine abokinsa kuda daya wanda suka tashi tun suna yara tare ,sannan kuma fahsir dane ga wazirin masarautar khaisira )ba abinda yake damuna kawai inaso nazauna anan ne"shine abinda yarima samhal yafada domin kawai ya shagaltar da fahsir ga barin sake masa wata tambayar wanda shima baida amsar ta a wannan lokacin,fuskantar hakan da fahsir yayi wanda dama ba bakon abu bane a wurinsa a game da halin amininnasa yasa shi cigaba da tambayarsa.Samhal mekke boyemin wanda yashafi rayuwarka sannan kuma bakaso nasani?hakika a wannan lokacin ka sauya fiye da tunanin mu ,bakason yin walwala dakuma shiga cikin mutane kafadamin me yake damunka idan nasani nabaka shawara idan kuma banda masaniya sai tayaka da addua akan hakan amma ganinka cikin wannan yanayin sam bashida wata masalaha,uuhm kokuma auren da su mai martaba matsama dakayi,shine yasaka ka cikin wannan halin?"a'a"shine abinda yarima samhal yafada tare da girgiza kai,"auren da mai martaba yasani bashi da alaka da damuwata amma kaman yadda ka bukata zan sanar dakai meyake faruwa dani watakil zaka iya bani shawara amma kaima ina hasashen bazaka samu masaniya akan al'amarin ba....uhmmm fahsir yafada tare da sauke ajiyar zuciya bayan gama jin duk bayanin dayayi daga bakin abokinnasa sannan yadora da cewa "ya kai dan uwana hakika wannan al'amarin abin dubawa ne duba da yanayin abin yake sakaka aciki wanda bayyi kama da yanayi na yau da kullum ba ,sannan kaman yanda kafada hakika banida masaniya akan wannan al'amari wanda nima a yanzu daure min kai matuka"koda gamajin jawabin da yarima samhal yayi daga bakin amininnasa sai koma ya jingina da jikin kujera kana yayi kaman ya tafi tunani narabin lokaci ,sannan ya dago ya dubi abokinnasa tare da fadin "yanzu yakke ganin zanyi da wannan al'amarin fahsir"shiru fahsir ysyi tareda ciza leban bakinsa nakasa kana ya dago yakalli abokinnasa tareda cewa "ina ganin abinda zaayi kawai kaje ga malam SHEHU NURUL ZAMAN,watakila bazai rasa samun mafita ba ko shawara a game da wannan al'amrarin"tohhh hakika ka kawao shawara wanda ni hankalina da bakai kan hakan ba sam "shine abinda yarima samhal yafa da.
         ***  ***  ***  ***  ***

  A fadar ta khaisira kuwa koda sarki sharzamamn yayi nazarin abinda ke cikin wannan bakar wasika ,amma vai gano komaiba gameda wasikar,sai hankalinsa yatashi matuka.Wand hakan yasashi mika takardar gayyata gasauran mabiyansa sarakuna guda uku wanda suke mulkar sauran kasashen dasuke yankinsu.
  Sarakuna guda hudu ne suke zaune a wani dakin na musamman wanda aka kebeshi a wani bangare na fadar khaisira,bayan gama shiryawar sune sarki sharzamamn yabude jawabinsa da sallama kana ya fara kamat haka :To yaku yan uwana kuma shuwagabanni a wannan alkarya tamu kuyi sani cewa tabbas akwai hasashen wata matsalar dazata iya fuskantar mu wanda idan ta tashi ba iya kasa daya zata shafa ba dukkanmu zaya shafa,wannan bayanin dana ke muku inayine a dalilin wata wasika da aka turomana wanda bata dauke da komai face wani bakin gari aciki,nakira kune domin mutattauna akan haka,shin ko acikinku wani yasan metake?TO kaman yanda kayi mana bayani akan wannan matsalat to kayi sani cewa kowa acikinmu ya samu aikan wannan wasika wadda bata dauke da sako a bayyane saidai duk mai nazari idan yayi tunani yasan akwai wani abu da wasikar take kunshe dashi,cewar daya daga cikin sarakunan,sannan game da masaniya kuwa duk cikinmu ba wanda yasan me hakan yake nufi,shima daya sarki yafada."hmmm "sarki sharzaman yaja ajiyar zuciya,"to naji dukkan bayananku amma game da inda zaa samu maslaha ko akwai wanda yake da sani akan hakan ? To masaniya akan wannan lamari duk cikinmu ba wanda yake dashi,amma inda zaa samu maslaha ne kaman zaa iya samu"shine abinda sarki HASHAM yafada nakasar khasmira ya fada.sarki sharzamanne yayi tambaya,to yanzu a ina kke ganin zaa samu mafitar ya sarki hasham ?shiru yayi na wani lokaci bayan ya gama jin tambayar da sarki sharzaman yayi masa,kana yace"A yamma da kasata akwai wani mutum wanda yake zaune a wani jeji ma abocin yalwa,shidai wannan mutum ya doshi shekara dari buyu a raye,sannan kuma masanine na abubuwa da dama a game da wannan duniya.TO inaganin mezai hana muje gareshi ko yana da amsar abinda muke dauke dashi.Koda sarakunan suka gama jin vayanin daya fito daga bakin dan uwannasu sai suka yanke shawara akan hakan,wanda kowa ya aminta da zuwa wajen masanin.
  Bayan gama shiryawarsune suka dunguzuma izuwa yamma da kasar ta khasmira batare da bata lokaciba,wanda suka shafe mako daya suna tafiya tare da yada zango a akan hanyarsu,wayewar wata safiyane ya bayyana inda sukayi arba da dajin wanda masaninn ke zaune aciki.Wajene daya kunshi kyawawan bishiyoyi dakuma tsutsaye masu dadin sauti,sun shafe kusan sa'a daya a wajen kafin wani mutum maabocin yalwar farin gashi ya wanzu agabansu,tsohone mai matsakaicin tsaho wanda ya manyanta a duniya.lale marhaba da sarakunan wannan kasa ,wanda sukayi tattaki izuwa wajena domin samun bayani game da BOYAYYIYAR ALKARYA shine abinda yafito daga bakin dattijon wanda fuskarsa take dauke da murmushi,sarki sharzaman ne ya ya kalleshi cike da mamaki kana yace"menene kuma boyayyar alkarya,sannan kuma abinda yakawomu ba abinda kke bayani akai bane?murmushinsane yakara fadada kana yace musu "yaku wannan sarakai kuyi sani cewa tabbas nasan abinda yake tafe daku amma wannan kalma data fito daga bakina itace abinda kuke nema sannan itace maganin matsalarku sannan itace silar wannan wasika da kuka samu bakoncinta"dukkan fuskar sarakan dauke take da alamar tambaya da kuma mamaki alokaci daya,wanda kuma ba wanda yasamu damar furta ko kalma daya daga cikinsu ,ganin hakan da dattijon yayine yasa yayi musu iso izuwa cikin bukkarsa wanda itace daya tilo a duk fadin dajin.
   koda zaman su a cikin bukkartasa sai yayi gyaran murya gami da cewar"nasan za kuyi mamakin abinda nafada ko kuma wanda zan fada amma kusani hakika akwai wani alamari dazai wakana a wannan nahiya tamu harma da nahiyar dhulkam,sannan abinda kuka taso har izuwa wajena dominsa ,abune daya ke nuna cewar lokacin da alamarin yake bukata ya matso kokuma yazo,sannan dukkan wannan abubuwan nada alaka ne da boyayyiyar alkarya da kuka ji na ambata a lokacin danayi arba daku"...to yakai wannan masani shin menene maanar wannan wasika ?sannan kuma menene zai auku a wannan nahiyar ?sannan wannan sunan da mukaji ka fada na boyayyiyar alkarya wace alkarya ce ?a ina take ?sannan meyasa ba musantaba ?kuma meyasa bamu taba jin labarintaba ?meyasa kuma ita ce sanadin dukkan abinda kafada wanda yake wakana ?wannan tamabayoyi dukka sun fitone daga bakin daya daga cikin sarakunan wanda tambayoyine dasuke bukatar amsa daga wajen duk wani mai sauraro daya ke da sani akan hakan.to menene amsar .........kukasance tare dani a chapter tagaba domin jin wannan amsoshi dazasu fito daga bakin dattijon.😊😜

        writer 💟sadi sakhna 💟(the legendary novelist)💝📖....

Boyayyiyar AlkaryaWhere stories live. Discover now