5&6

178 12 5
                                    

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

     *WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
     ( _Wankan Abaya Dole_)

       BY
*AMEERA ADAM*
      *AmeeraAdam60*
                    *@Wattpad*

DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*

          SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼
https://chat.whatsapp.com/L7dj60ptcAV3Oe1X6hAyBT
                  5&6

         A zabure ta fito daga ɗakin da gudu tana ihu hankali a tashe da sauri tayi bayan Umma ta maƙale ta, Umma itama maƙalewa tayi a bakin kitchen tana leƙen abinda Yusra ta ke wa ihu, ganin shiru ba abinda ya biyo baya yasa Umma ta fara ƙoƙarin cire Yusra daga jikinta tana cewa.

      " Yusra lafiya wai me kikewa ihu? Amma har yanxu banga wani abu ya biyoki ba "

    Nuna ɗakinta ta shiga yi tana faɗin, " Wallahi Umma Luccy ba mage bace Aljana ce yanzu nan naga tana yi wani irin abu harda fuffuke ajikinta kuma a gaba na ta nitse ƙarƙashin ƙasa. "

        Sototo Umma tayi tana kallan Yusra sannan ta ce, " Yusra yau shekararki nawa da Luccy a gidan nan inace aƙalla ta tafi shekara ta shida, kice dai ƙiyayyar taki ce ta motsa dama nasan keda mahaifinki akan dole take zaune a cikin gidan nan "

        Daga cen ƙofar ɗakinsa ya fito yana cewa, " Yusra ya akayi ne naji ihunki daga ɗaki " abinda ta gani ta sanar dashi aikuwa kamar dama jira yake ya dinga faɗa ta inda yake shiga ba nan yake fita ba, Shiru Umma tayi masa ya kalli Yusra ya ce.

       " Kyaleni da ita da magen ayau basai gobe ba zata bar gidan nan dan Ubanta, maza jeki ɗauko mun buhu dama naƙi jinin magen nan haka kawai ki jawo mana Alaƙaƙai dama zaman haƙuri nake da ita. "
      Yana ƙarasa maganar kamar mai jira Yusra ta tashi da sauri ta wuce store ɗinsu ta hau dube-dube, bayan wani lokaci sai ga ta ɗauke da buhu a hannu ta fito, gaba Abba ya wuce tana biye dashi a baya har sunje bakin ƙofar ɗakin Umma ta ce, " Yanxu Malam kaima biyewa yarinyar nan zakayi shekara da shekaru muna tare da magen nan amma rana tsaka a ɗauketa a yar, yanzu kasan wane  hali zata shiga? "

      A zafafe ya jiyo ya rufe Umma da faɗa, " Duk halin da zata shiga ta shiga man wato mage tafi ƴar da kika haifa ko Saratu? Wallahi kin bani mamaki baki damu da halin  da ƴarki zata shiga ba sai wata banzar mage "

     Murya a sanyaye Umma ta ce, " Nifa ba manufa ta ke nan ba abi abun a sannu Malam " Abba da takaici ya kamashi kasa magana yayi kawai ya watsawa Umma harara yana wucewa gaba abinsa.

        Suna shiga ɗakin Luccy na kwance a dai-dai gurin da Yusra ta ga nutsewarta ƙarƙashin ƙasa, Abba cikin masifa ya fara magana, " Wato ke ga sheɗaniya har zaki fara taɓa mun ƴa da siddabarunki na iska, dama ai ance yawanci maguna iska ne to ta Allah ba taki ba " yana gama faɗa ya miƙa hannu ya ɗauko Luccy ga mamakinsa wani irin sanyi yaji yana ratsa jikinsa gaba ɗaya, da sauri ya sake ta yana mamakin wannan al'amari , wani nazari yayi ya kuma kai hannu zai ɗaukota aikuwa da gudu ta haye kan gado.

      Abayar Yusra ya hango akan ƙyaure ya janyota cikin dabara a hankali ya taka zai rufe ta dashi amma ta zille, ta jima suna wasan tsere da Abba har Allah ya bashi nasara ya bugata da bango, tana ƙoƙarin tashi yasa Abaya ya rufeta ya ƙudundune ya ƙarɓi buhun hannun Yusra ya turata a ciki.

      Yusra ɗan zumɓura baki tai tana cewa, " Abba kuma ka rasa da me zaka ɗauke magen sai da Abaya ta? " Kallanta yayi yace, " Haba Yusran Baba ai ba wani abu bane kuma naga rannan kika sa ta tayi datti " ƙunƙuni ta fara yi ƙasa-ƙasa cikin ɓacin rai badan ta so ba.

       Fitowa sukayi Umma na tsaye jiki ba ƙwari take binsu da kallo, Abba har yayi gaba ya jiyo ya cewa Yusra, " Yusran Baba zo muje ki rakani man cen Bolar bakin kasuwa zan kaita na wurgar " Yusra ba musu ta wuce suna tafe suna hira har suka ƙarasa.

       Suna ƙarasawa basuyi wata-wata ba Abba ya cirota ta wurga cen, gaba ɗaya jikinta yayi laushi saboda wahalar da ta sha, suna jefarta suka juyo gida suna gabda ƙarasawa Abba ya lura da kallon da mutane suke ta binsu da shi tun barowarsu bakin kasuwa, cikin ƙosawa da kallan nasu Abba ya cewa Yusra.

     " Wuce gida Yusra ni bari naje na ƙarɓo mana kayan breakfast a shagon Lawan " ita ɗinma ta lura da kallon da ake musu haka ne yasa ta wuce gida.

      Tun daga nesa Abba ya lura da irin kallon da ƴan magajalisar Lawan mai kanti suke masa amma sai ya basar, sallama yayi musu kowanne baki a sake ya bishi da kallo haka nan shi kansa mai kantin, Biredi da kayan Tea ya siya amma duk a tsarge yake haka ya baro shagon jiki ba ƙwari saboda wasu ma har dariya suke masa, sosai abin ya bashi mamaki da haushi

      Yana cikin tafiya ya haɗu da Abokinsa Malam Haruna, tun daga nasa Malam Haruna ya riƙe baki da mamaki yake kallon Abba yana ƙarasowa kusa da shi ya ce, " Malam Auwal me ya sameka haka dan Allah "

       Da mamaki ya kalli jikinsa yace, " Malam Haruna ban gane ba "

      Malam Haruna dafe kai yayi ya ce, " Wai Abokina ko ɓatan kai kayi ne baka ganin Abayar mata ce ajikinka wannan doguwar rigar da suke sawa, ji dan Allah harda wani mayafinta a wuyanka "

      Abba kalle-kalle ya shiga yi yana duba Shaddar jikinsa yaga sam baiga wata illah ba, shi dai yasan shaddarsa ya ɗauka ya sa amma yaji ana masa wani zance na abaya.

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

WANDA BAI JI BARI BA....Where stories live. Discover now