29&30

129 8 2
                                    

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

     *WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
     ( _Wankan Abaya Dole_)

       BY
*AMEERA ADAM*
      *AmeeraAdam60*
                    *@Wattpad*

DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*

          SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼

                  29&30

         Malam Liman tsam yayi da tunaninsa ya gama sauraren Marwan cikin dakiya da ƙwarin gwiwa yace, " A cen ɗinma Allah ne ya ara maka lokaci amma a nan cikin ikon Allah dole mu ɗauki mataki akanka, Insha Allah yanda aka hallaka mahaifinka kaima sai mun hallaka ka "

       Yusra kafe Malam Liman tayi da idanu sannan Marwan ya cigaba da cewa, " Malam Liman naga kana ji da taƙama ina tunanin bakasan waye ni ba, amma tunda kace haka mu zuba mu gani "

    Marwan na gama magana Malam Liman yayi Auziya ya fara karatu, tunda Yusra ta sunkuyar da kai ƙasa bata ƙara ɗagowa ba, duk yanda Ayar Allah take ratsa cikin jikinsa baisa ya karaya ya furta ko da uffan ba, banda gumi babu abinda yake haɗawa saboda tsabar wahala, Malam Liman ko kaɗan bai sarara ba.

       Marwan tun yana daurewa har yaji Azaba ta fara mamaye jikinsa, a zabure ya ƙwalla ƙara sannan yace, " Dakata Malam ina da magana "

    Malam Liman yace, " Faɗi ina jinka "

     Yusra miƙewa tayi tsaye tana maida gashin kanta baya sannan ta kalli bishiyar dake gefensu ta fara motsa baki, take wata irin iska mai kama da guguwa da turniƙe gurin, nuna mutanen gurin tayi da hannunta tana hura musu wata baƙar iska daga bakinta.

     Gaba ɗaya su Mai Unguwa kwanciya sukayi agurin suna ƙanƙame junansu, Ƙurar na lafawa  Marwan da ke Yusra ya ƙyaƙyace da wat irin dariya bai amsa kuwwa a kunnuwan al'umma.

     Lokaci ɗaya mutanen gurin suka fara ɗago da kawunansu dan ganin abina yake faruwa.

      Suna ɗagowa suka nemi Malam Liman sama da ƙasa suka rasa, gaba ɗayansu tsorone ya kamasu cikin suɓutar baki Mai Unguwa ya ce, " Yau mun shiga uku ina aka kai Malam Liman kashinmu ya bushe..."

      Mai Unguwa bai kai ga rufe baki ba yaji wannan Abayar ta shige jikinsa zuruf, Dafe kansa yayi cikin faɗuwar gaba ya kurma Ihu yana cewa su Alhaji Babba, " Alhaji Babba dan girman Allah ku taimaka ku ciremun Abayar nan " Yusra dake tsaye kallan Mai Unguwa tayi ta fara cewa, " Furkus Furkus Furkus " ( Ku xane shi, ku zane shi, ku zane shi ) bata ƙarasa rufe baki ba Mai Unguwa ya fara jin bulala a tsakiyar kansa, ihu yake tun ƙarfinsa babu wanda ya tanka masa bare suyi masa sannu.

      Malam Liman tun bayan da Ƙurar nan ta tashi ya zubawa sarutar Allah ido, abu ɗaya ne ya bashi mamaki da yaji Mai Unguwa na kururwar bai ganshi ba, abun mamaki shi yana ganinsu har yana iya yi musu magana amma babu mai jin bare ganinsa.

       Marwan kuwa a cikin ƙurar iskar nan ya shafe idanun mutanen nahiyar da kunnen jinsu ga Malam Liman, Alhaji Babba tunda ya ga ana zane Mai Unguwa yayi tsumi jikinsa yayi sanyi, fakar idon Yusra yayi ya cire Babbar rigarsa ya ajiye a gefe, tun ƙarfinsa ya taƙarƙare ya sheƙa a guje tun baiyi nisa ba Yusra ta sa hannu ta Zuni shi baya.

     Alhaji Babba gudu yake amma a guri ɗaya ya kasa barin gurin sa yake, ya gaji sosai so yake ya daina gudun amma ya kasa, cikin sarewa ya juyo ya ce, " Dan Allah ka dubi girman Alla ka tsaida ni na daina gudun nan haka "

       Mai Unguwa tun yana magiya yana bada haƙuri har ya galabaita ya kasa magana, banda fitsari da yake ta saki da tusa ba abinda yake yi, jikinsa gaba ɗaya yayi laushi a take ya yanke jiki ya faɗi a sume.

      Suna cikin haka suka ji ƙarar dira harsai da gurun ya girgiza, da sauri Yusra ta juya gefen damanta, Wani mutum ta gani mai sufffar Malam Liman suna haɗa ido murmushi yayi wa Yusra.

       Yusra bata bi ta kanshi ba ta nuna Alhaji Babba, Mai Unguwa da Abba take ya zuƙosu da hannunsa suka bi ta jikin Bishiyar dake gurin suka ɓace.

      Mai Siffar Malam Liman Murmushi yayi shima ya taka ƙasa na nutsa ciki ya ɓace.

    TAMMAT BIHAMDULILLAH👏🏼

*ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN NAN NA ƊAYA, INSHA ALLAH ZAN ƊORA DA LITTAFIN NA BIYU MAI BUƘATAR KARANTAWA ZAI TURO DA KATIN MTN NA 100 TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 KUMA ZAI TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 KOFA A BUƊE TAKE GA DUK WANDA YA SHIRYA.*

INA GODIYA KWARAI MASOYA BISA YANDA KUKA NUNA KULAWARKU GA WANNAN LITTAFIN NAGODE KWARAI ALLAH YA BAR ƘAUNA.❤️❤️

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

WANDA BAI JI BARI BA....Место, где живут истории. Откройте их для себя