LAST FREE PAGES

153 12 0
                                    

*WANDA BAIJI BARI BA*
       ( _Wankan Abaya Dole_)

AMEERA ADAM

BOOK 2
           PAID BOOK

_WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DA NAIRA 100 KACAL ZAKI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI KI BIYA KI KARANTA ABINKI IDAN KINA BUƘATAR VIP WATO POSTING SAU BIYU A RANA ZAKI TURO KATIN 200, *DAN GIRMAN ALLAH ƳAR UWA IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI KARKI SIYA NA YAFE CINIKINKI* ZAKI TURO DA KATIN MTN NA 100 KO VIP 200 TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 TARE DA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DA KIKA TURO._

Last Free page     9&10

         Alhaji Liman ganin haka yasa shi ya koma gefe ya ɗauki buta yayi alwala ya shiga ɗakinsa ya fara gabatar da nafila raka'a biyu sannan ya buɗe Alƙur'ani ya fara karantawa, Harbatu bai tsaya a ko ina ba sai cen gaɓar kogin Gudaimin acikin wata ƙoramar inda a nan mahaifiyarsa ke zauen tana ganinsa taga yanayin daya dawo hankalinta ya tashi, take ta kwantar dashi kan gadon itacen bishiyar tsamiya bata yi wata-wata ba ki nutsa cikin ƙorama ta haɗo masa magungunan tana dawowa ta murza ta shafe masa jikinsa sauran ta bashi ya sha, take ya miƙe garau da shi har ji yayi wani ƙarin ƙwarin gwiwa ya ƙara kama shi, ko sallama bai mata ba ya fito daga cikin gaɓar taiku ya wuce gidan Malam Liman a zafefe dan niyyar ɗaukar fansa.

      Uwar gidan Malam Liman na daga ɗaki ta fara jin kamar muryar mijinsu sama-sama yana karatu, Salamatu ma hakan taji da sauri suka zaburo suka fito waje, kusan tare ma suka tako waje kamar haɗin bakin kowacce ta ce, " Ni kamar muryar Malam nake ji a gidan ko kunnena ne? "

     Ma'awiyya  da ta fito daga wanka ɗaure da ɗaurin ƙirji ta ce, " Wallahi nima tun ina wanka nake jin muryar Baba " Sautin karatun ne ya ƙaru daga wajen ɗakinsa da sauri suka juya zasu je ɗakinsa sai ji sukayi daga bakin ƙofa anje.

     " Ina zakuje bayan gani nan " da mamaki suka juyo suna kallansa, fara'arsu ce ta faɗaɗa cikin murna suka tarbeshi suna murnar dawowarsa, Malam Liman dake ɗaki yana karatu jin hayaniyar matansa da barka da zuwansa yasa ya rufe ƙur'anin ya fito tsakar gida.

      Marwan na ganinsa ya fakaici idanun matan Malam Liman ya ƙifta masa ido, Malam Liman baiyi mamaki ba saboda yasan kaidinsa ya zarce haka, a hankali ya fara takowa har zuwa wajen da suke tsaitsaye, yana zuwa ya ce.

    " Ma'awiyya ban hanaki shiga banɗaki babu ɗankwali ba? Wuce ki tafi ki suturta jikinki " Gaba ɗaya juyawa sukayi inda suke jin muryar Malam Liman amma ga mamakinsu ba wanda suka gani.

     Kafin Ma'awiyya ta juya ga inda take jin muryar Mahaifinta tuni Harbatu ya shige jikinta, kanta ne ya wani irin sarawa sai da ta dafe kanta sannan ta iya ɗago da kanta, gaba ɗayansu mamaki ne ya kamasu haɗe da tsoro ɗanja da baya sukayi saboda abun ba ƙaramin ɗaure musu kai yayi ba.

    Marwan na ganin haka ya ce, " Au na shigo cikin iyalina nan ma biyoni zakayi to ta Allah ba taka ba " juyawa sukayi ga Marwan suka ce, " Malam Hala labarin da akaxo aka sanar damu gaskiya ne " Marwan ya ce, " Eh gaskiya ne aljanin jikin yarinyar nan Yusra ne yaso illtamu mun samu mun kuɓuto shi ne yake so yazo nan yayi wasa da hankalinku " Malam Liman najin haka ya ce, " Ƙarya kake azzalumin ALLAH da sannu sai asirinka ya toni sai n hallaka ka da ayar ALLAH, Shamsiya karku yarda dashi karku amince yaudararku zaiyi "

     Gabaɗaya shiru sukayi babu mai bakin magana sai kallon kallo suke a junansu, Marwan ganin haka ne yasa yaga kamar sun fara aminta da Maganar Malam Liman shiyasa ya ce, " Tir da halinka da yaudararrun kalamanka ka bari na huta da sannu zan ƙoneka da Ayar Allah. " Marwan na gama faɗin haka ya ce, " Ku wuce muje ciki " basu da mafita haka suka wuce suna tafe Marwan na biye dasu a baya, ganin sunyi gaba yasa shi juyawa ya cewa Malam Liman.

WANDA BAI JI BARI BA....Onde histórias criam vida. Descubra agora