*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
( _Wankan Abaya Dole_)BY
*AMEERA ADAM*
*AmeeraAdam60*
*@Wattpad*DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼
23&24
Babu wanda ya lura da haka sai shi kaɗai da sauri ya zura kansa bayan Malam Liman yana cewa, " Dan Allah kuyi haƙuri na tuba " gabaɗaya kallo ne ya koma kan Alhaji Babba, Aramma abin ba ƙaramin dariya ya bashi ba, kallan Malam Liman yayi yace, " Allah gafarta Malam ina ganin Idan zakayiwa Yarinyar nan ruƙiya ko zakz haɗa da Alhaji Babba? "
Malam Liman na shirin magana Mai Unguwa yayi karaf yace, " Kwarai kuwa domin alamu sun nuna shima Aljanu sun shige shi..."
Mai Unguwa shima anan maganarsa ta tsaya lokacin da kai idanunsa kan Yusra, sunkuyar da kai ƙasa yayi bai ƙara cewa uffan ba, Malam Liman ganin suna daɗa ɓata lokaci yasa ya fara magana.
" Assalamu alaikum, Dan Allah muyi abinda yake gabanmu tunda dukkanmu ba yara bane mu, Malam Auwalu muna jinka "
Abba gyara zamansa yayi sannan ya fara cewa, " _Kamar yanda kowa ya sanni a gurin nan nidai Ainihin sunana Auwalu Musa ni haifaffen garin Kano ne cikin Unguwar wailari, ina zaune cikin mahaifata nida sauran ƴan uwana, gabaɗayan ku kunsan Allah bai nufeni da haihuwa da wuri ba, ina tunanin sa'annina da mukayi aure atare suna da aurarrun ƴaƴa kusan uku ko huɗu ma, dan Aƙalla sai da muka shekara kusan goma da aure amma babu haihuw, sai daga baya Allah ya axurta mu da Yusra._"
Abba kallanYusra yayi sannan ya cigaba da cewa, " _Murna gurinmu bata musaltuwa, haka muka ɗauki soyayyar duniya muka ɗora akanta, musamman ma ni da ko ƙuda banasan ya taɓa ta, mahaifiyarta na nuna mata ƙauna ta daidai misali amma ni gani nake kamar bata ƙaunarta, saboda idan ta mata laifi tana mata faɗa wani lokacinma harda duka, sautari duk faɗan da zamuyi nida mahaifiyarta sai dai muyi akanta, tun tana biya mun muyi babu daɗi ganin Yusra ta girma yasa ta daina biye mun, yau da gobe itama yarinyar tun bata lura har ta ankare ya zama tafi so saboda ni nake goya mata bayan koda kuwa itace da laifi._
_A kanta na ɓata da ƴan uwa da abokan arxiki hatta malam makarantarsu ban bari ba zuwa nake gurinsu idan wani ya dake ta, duk abinda Yusra take so nima shi nake so ko da kuwa abin nan ba mai kyau ba._"Numfasawa Abba yayi ya cigaba da cewa, " _Duk wanda yasan Yusra yasan ta taso a sangarce ba kwaɓa hatta mu iyayenta bata raga mana ba, bata ganin girman kowa duk girmanka bata ƙi ta gaya maka magana tayi wucewarta ba, tun abin baya damuna har ya fara damuna a cikin zuciyat sai dai babu yanda zanyi tunda ance icce tun yana ɗanye ake tanƙwra shi, har iya yau Mahaifiyar yarinyar nan bata gajiya da mun nasiha akan makauniyar soyayyar da nake nuna mata_"
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
ƊANƊANO DAGA SABON LITTAFI NA
PAID BOOK
Littafin nan na kuɗi ne da naira 200 ki zaki karanta shi cikin nutsuwa, game buƙatar ƙarin bayani zai iya mun magana ta wannan number 0706 206 2624ANYA BAIWA CE?
NA
AMEERA ADAMFree page 1
Tafe take tana ɗan waige dan gudun karwani ya ganta ko taci karo da wani a hanya saboda abinda ta gano take san zuwa ta isar da shi, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayin ta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.
YOU ARE READING
WANDA BAI JI BARI BA....
Short StoryIska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin...