FREE PAGES

150 11 0
                                    

*WANDA BAIJI BARI BA*
       ( _Wankan Abaya Dole_)

AMEERA ADAM

BOOK 2
           PAID BOOK

_WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DA NAIRA 100 KACAL ZAKI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI KI BIYA KI KARANTA ABINKI IDAN KINA BUƘATAR VIP WATO POSTING SAU BIYU A RANA ZAKI TURO KATIN 200, *DAN GIRMAN ALLAH ƳAR UWA IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI KARKI SIYA NA YAFE CINIKINKI* ZAKI TURO DA KATIN MTN NA 100 KO VIP 200 TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624 TARE DA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DA KIKA TURO._

Free page     7&8

          Mai Unguwa irin mutanen nan ne marasa jiki da tsayi tun tasowarsa abokin Alhaji Babba ne tare sukayi wasan ƙuriciya sai dai Alhaji Babba ya ɗan girme masa, tuntuni tun suna yara haka suke indai zasu haɗu guri guda to bazasu rabu ba sai wani abu ya shiga tsakaninsu, sai dai duk wannan faɗan nasu ba'a cika shiga tsakaninsu ba, saboda da sunyi faɗan zuwa wani lokaci zai wuce.

     Shi Mai Unguwa Allah yayishi da san girma tun yana ƙarami, sai kuma Allah yasa ya samu gadon Mahaifinsa ya riƙe sarautar Gargajiya ta Mai Unguwa, hakan ne yasa Izzarsa da san girmansa suka ƙaru agurinsa.

      Alhaji Babba irin mutanen nan ne masu tsayi sosai ga kuma jiki, sai dai shi mutum ne mafaɗaci ko da ka girmeshi idan ta haɗoku ba ruwansa yana iya balbalka da faɗa abinsa, sai dai ko kaɗan bashi da ruƙo da anyi abu idan ya amayar da abinda ke cikinsa shikenan ya wuce a gurinsa.
      Sai dai kuma mutum ne da yaƙi jinin raini da rashin mutumci idan kuma taku tazo ɗaya zaka fahimci mutum ne mai sauƙin kai.

     Mai Unguwa da ya gama ƙulewa da maganganun Alhaji Babba da bige masa bakin da akayi, kukan kura yayi ta ɗafe bayan Alhaji Babba saboda ransa ya gama ɓaci, a ganinsa kamar yanda yake da matsayi da sarauta amma ayi masa haka? Wannan ba ƙaramin cin zarafi bane dan haka a zafe ya kaiwa Alhaji Babba wata raruma yana ɗafe bayansa ya ce.

     " Wallahi Alhaji Babba yau ko ni ko kai a gurin nan tunda abin naka na harda rashin mutumci da raini " Alhaji Babba Murmushi yayi ya kauda kai gefe yana wani murmushi, juyowa yayi yaga yanda Mai Unguwa ya maƙale shi cikin kausashshiyar murya ya ce.

    " Kai Tanko wallahi ko ka cikani ko indamfaraka da ƙasa, ka ga tun da ragowar mutumcinka a idona ka sakarmin riga" Mai Unguwa ɗago da kansa yayi ya ce, " Ka daɗe bakayi ba, nace ka daɗe bakayi ba aina riga na gaya maka yau ko ni ko kai a gurin nan " Abba da tun farkon fara maganarsu yana jinsu tun surutun nasu baya damunsa har abun ya kaishi bango, cikin tsananin ɓacin rai ya kallesu ya buga musu tsawa sannan ya ce, " Wai meye haka kukeyi kamar wasu ƙananan yara, geme-geme da ku wannan ai sakarci ne haba, muna cikin wani hali anma ku ko a jikinku "

     Mai Unguwa sai a lokacin ya sauko daga jikin Alhaji Babba jiki ba ƙwari, Alhaji Babba ƙarewa Abba kallo yayi cikin mamaki, domin yasan yanda Abba ke bashi girma kamar shi ya haifeshi, a gefe guda kuma haushine ya kamashi yana ganin kamar antozartashi gaban mutane, ciki faɗa Alhaji Babba ya ce, "  Auwalu kaci Ubanka, nace kaci Ubanka kaji ni zaka tozarta a idon bare ka wulakantani har kake gayamun magana, Auwalu ko musu baka cika yi dani ba amma yau ni kake gayawa haka, so kake wasu banza bare su ji daɗin yi mana dariya " Mai Unguwa da ya gama tsarguwa ya cewa Alhaji Babba.

     " Wai waye baren da kake ta ikirari ne? " Alhaji Babba ya watsawa Mai Unguwa kallo ya ce, " Oho wanda ya tsargu "

      Abba da har lokacin zuciyarsa zafi take ya kuma buga musu tsawa  yana faɗin, " Kaiiii wai yau meye a kanku ne? Yaya Babba wallahi duk abinda zaka faɗa kaje ka faɗa ni yanzu tunanina halin da Yusra take ciki, ku duba ku ganta cen tunda muka shigo gurin nan take durƙushe tana kuka, shin ku abin bai baku mamaki haɗe da tsoro ba ace yariyar nan ko ta ɗago ta dubemu, jin kunnensu Mugun Aljanin cen yace indai ba shi ya bata umarni ba bazata taɓa kulani ba, ko dan ba ɗaya daga cikinta ne ya haifeta ba. " Alhaji Babba gyara tsayuwa yayi ya ce, " Zo ka rufeni da duka kaji Auwalu abinda ya dace kenan, dole ka ce bamusan zafin Yusra ba tunda bamu taɓa haihuwa munji ya ɗa yake agurin iyaye ba. "

WANDA BAI JI BARI BA....Where stories live. Discover now