*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
( _Wankan Abaya Dole_)BY
*AMEERA ADAM*
*AmeeraAdam60*
*@Wattpad*DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼
15&16
NOT EDITED
Mai Unguwa da sauri ya sauke kansa ƙasa jikinsa har tsuma yake, yana cikin wannan yanayin yaji Saminu ya ce, " Allah ya taimakeka ya baka yawan rai yanzu dai ance buhun na ƙofar gidan Wali Mai wanki "
Mai Unguwa tun da ya sunkuyar da kai ƙasa tsoron ɗago kansa yake yana gudun yaje ya kuma cin ƙaro da mugun gamo, ta gefen ido ya fara ɗagowa yana satar kallon gefen da ya hango Jakin nan maganar Alhaji Babba ce ta ƙatse shi yace.
" Ranka shi daɗe ni ina ganin a sanya su Malam liman cikin wannan lamarin domin lamarin akwai rikitarwa ina ganin kamar aikin shaiɗanu ne "
Cikin Sauri Saminu yayi farat yace, " Hattara Alhaji Babba, ana nufin Mai Unguwa ya gaza kenan? " Mai Unguwa shi kansa yaji daɗin magana Alhaji Babba amma idan yayi na'am da ita kamar ya muzanta kansa gaban al'umma ne, shi kuwa a duniya yaƙi jinin wani ya gano lagwansa gwara duk yanda zaiyi ya kare ƙimarsa kar mutane su lura da tsoronsa ƙarara.
Fuska a tsuke Mai Unguwa ya kalli Alhaji Babba ya ce, " Alhaji Babba yaushe aka ga makwancinmu haka? Wato mu bazamu iya aiwatar da komai ba sai su Malam Liman, ashe kallan jahilai ake ...." Maganar Mai Unguwa ce ta maƙale lokacin ya kai idanunsa kan wannan jakin, suna haɗa ido yaga Jakin ya buɗe baki zai kaiwa Alhaji Babba cizo.
Da sauri Mai Unguwa ya zabura yace, " Alhaji Babba gasu nan zasu cinye ka " Ba Alhaji Babba kaɗai ba hatta sauran mutanen dube-dube suka shiga amma basu ga wani abu ba " Mai Unguwa kunya ce ta kamashi ya koma ya zaune yana ɗauke kansa gefe.
Alhaji Babba da har lokacin tsoro bai gama sakinsa ba tsumu yayi cikin halin firgici yace, " Shikenan nikam tawa ta ƙare abun yazo kaina " Mai Unguwa cikin borin kunya yace, " Mai kake faɗa haka ne Alhaji Babba nifa tsokanarka nakeyi " Shiru ne ya biyo baya sannan Saminu ya ce, " Allah ya taimakeka ai sai mu ƙarasa gurun ko "
Mai Unguwa amsawa yayi afili amma cikin zuciyarsa banda lugude ba abinda take yi, yana yunƙurun tashi Alhaji Babba ya ce, " Yanzu zuwa gurin za'ayi ranka shi daɗe? " Mai Unguwa yace, " Ƙwarai ma kuwa domin muje mu ganowa idonmu "
Alhaji Babba Yace, " Jama'a ku gafarce ni amma wallahi babu inda zani, a take gurin ya yamutse da hayaniya ashe ba Alhaji Babba ne kaɗai bayasan zuwa ba, sai yanzu sauran suka bayyana, wasu suna zasu wasu suna cewa bazasu ba.
Suna cikin haka Munkaila ya ce, " Jama'a ku duba cen ga buhun da muke magana nan ya taho "
Gaba ɗaya hankulan jama'ar gurun ya tattara ya koma gurun da buhu ya ke tahowa, Ahaji Babba shi da Mai unguwa lokaci ɗaya suka zabura zasu tashi, rawanin Mai Unguwa tuni ya faɗi gefe.
Malam Liman da ke gefe murmushin takaici yayi sannan ya ce, " Haba Mai unguwa ya kuke neman ku manta da Ubangiji a cikin lamuranku, ku samu nutsuwa mana " Mai Unguwa da ya dawo ƙasa kusa da Malam Liman yace, " Malam Liman Allah muka sa gaba amma ga dubi wannan lamarin "
Saminu da ke gefe ne yace, " Kai Lauwali miƙomun rawanin ranka shi daɗe " Ana shirin ɗauko rawanin Mai Unguwa suka ga ya tashi sama ya haɗe bishiyar tsamiyar da ke gefensu.
Take Mai Unguwa ya hau tsuma yana faɗin, " Ka gani ko? Wallahi tunda suka ɗauki rawani na nima suna iya yin sama da ni jama'a ku taimaka mun " Gurin gaba ɗaya yayi tsit su Umma sai muzurai suke saboda tashin hankali, Malam Liman ne ya ce, " Cikin kudurar Ubangiji babu abinda zai sameka ka sa Allah a ranka " Mai Unguwa na shirin Magana suka ga buhun nan ya ƙaraso gurunsu ya tsaya, tsakaninsu da shi baifi taku biyu ba, atake mutanen gurin suka fara matsawa suna naniƙewa Malam Liman.
Buhun Bai jima da zuwa gurin ba ɗaya bayan ɗaya suka far gani anayin sama da hulunan mutanen da ke gurin, tsoro ne ya fara kamasu da tashin hankali kowanne tsoronsa tunda anɗauke hularsu kar afara ɗaukan su ana ɗorawa akan bishiya.Mutanen da aka barwa huluna akansu basu fi mutum bakwai ba daga Malam Liman sai wasu mutum shida.
Alhaji Babba hularsa nayin sama ya janyo babbar rigar Malam Liman yana tura kansa ciki.
Daga cikin Buhun ƙafar mutum suka gani ta leƙo take wata iska mai kama da guguwa ta fara tashi a gurin.
_IDAN NAJI RUWAN COMMENTS ANJIMA KU GA WANI SHAFIN_🤣
TEAM ABBA KUSHA KURUMUNKU YA KUSA FITOWA SHI DA KAYAN AIKINSA🤣🤣🤣🤣
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
KAMU SEDANG MEMBACA
WANDA BAI JI BARI BA....
Cerita PendekIska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin...