*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
( _Wankan Abaya Dole_)BY
*AMEERA ADAM*
*AmeeraAdam60*
*@Wattpad*DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼
17&18
Malam Liman duk yanda yaso gimtse dariyarsa abin yaci tur har sai da ya murmusa, wannan guguwar ba ƙaramin tsoro ta basu ba, gaba ɗaya sun rirriƙe junansu gudun kar iskar ta tashi sama da su.
Matan da suke gurin gaba ɗaya suma sun rirrike junansu sun cunkushe guri ɗaya, tazararsu da mazan babu yawa sosai.
Malam Liman zubawa sarautar Allah ido cikin zuciyarsa yake ayyana tabbas wannan ba komai bane illa shaiɗancin Aljanu.
Abu kamar wasa Mai Unguwa na takure jikin Liman yaji alamun kamar yana barin ƙasa, jin ya fara tashi sama yasa shi fasa ihu cikin tashin hankali, gefe da gefensa ya fara kalli domin yaga wanda zai janyo su tafi tare.Jama'ar gurin suna ganin haka suka kuma kwantar da kansu, wasu daga cikinsu harda rufda ciki.
Allah ne ya bawa Mai Unguwa sa'a carab ya janyo babbar rigar Alhaji Babba, aikuwa yana jin anfara jan rigarsa Alhaji Babbar ya fara cewa.
" Ka dubi girman Allah ka sakeni karka jani mutafi tare da sauran lokaci na wa'adina bai cika ba, wayyo Malam Liman ku tausaya mun ku taimakeni " Malam Liman baiyi wata-wata ba ya fara karanto Ayatulkursiyyu yana tofawa musu, kamar waɗanda aka saki ji kake gijiiiiiiiiiibbb Alhaji Babba ya faɗo ƙasa, cikin jin zafin faɗuwar yace, " Wash Allah naaaaaa"
Bai gama hucewa ba sai ga Mai Unguwa ya faɗo kansa yuuuuuffff, Wani uban nishi ya saki daga nan basu ƙarajin maganar Alhaji Babba, Mai Unguwa yana jin ya faɗo ya zabura ya ɗafe bayan Malam Liman.
Malan Liman da ƙyar ya samu ya yakice Mai Unguwa daga Bayansa amma yana nan ya maƙale hannu da ƙafar Malan Liman, Malan Liman kallan buhun nan yayi ga fara ƙaranto Ayatulkursiyyu da Amanarrasulu tare da sauran ayoyin Alƙur'ani yana tofawa.
Take suka ga buhun ya gungura gefe, cikin wahalalliyar murya Abba yake sumbatu, " Ya Allah ka kawo mun ƙarshen wahalar nan da nake ciki, jama'a ku taimka mun ko ba a duniyar mutane nake bane? Jama'a wai babu kowa a duniyar ne? "
Umma zaro idanu tayi tana kasa kunne, sosai muryar tayi mata kama da ta Abba, gaba ɗaya mutanen gurin kasaƙe sukayi cikin ta'ajibi, Malam Liman miƙewa yayi da niyyar zuwa gurin buhun da ganin mutumin dake ciki, Malan Harisu ne ya kalli Malan Liman ya ce, " Malam Liman nifa inajin tsoro baku lura da halin da Alhaji Babba yake ciki ba, tun da suka faɗo fa yana nan yanda yake, ina tsoron karfa ta Allah ta kasance " sai a lokacin hankulan mutane ya koma gun Alhaji Babba da ke sharɓe a gefe yayi rufda ciki.
Mutanen dake kusa dashi ne sukayi ta maza suka ɗago shi, wahalallan numfashi Alhaji Babba ya sauke, kallansu yayi ɗaya bayan ɗayan sannan ya ce, " Malam Harisu Allah wadaran halinka ashe Allah-Allah kake na mutu, to ban mutu ba wahala ce kawai nasha " Malam Harisu cikin jin haushi yace, " Kai ka sani kaida ba'a maka gwaninta idan ka so ka zauna gadin duniya "
Suna cikin haka sukaji Buhu ya kuma cewa, " Al'ummar Annabi babu mai ji na ne? " da sauri Malan Liman ya ƙarasa gurin ya jima akan buhun yana addu'o'i yana tofawa sannan ya kallesu yace, " ko zan samu reza agurinkun " kamar haɗin baki suka ce masa babu, Ɗan Tani ne yayi farat yace, " Ga ƙaramar aska nan a gurina " Malam Liman karɓa yayi sai da yayi bismilah sannan ya fara yanka gefen buhun, yana gama yankawa sai ga mutum kwance ɗaure da guru a ƙugunsa da wasu wuri a hannunsa ɗaya da ƙafarsa ɗaya, girgiza kai yayi sannan yayi bismillah yasa hannu ya juyo da Abba.
Ganin Abba ba ƙaramin mamaki ya basu ba gaba ɗaya zaro idanu sukayi wasu daga ciki suna rafka salati.
Tofi Malam Liman yayi ya tofa a fuska Abba take ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya sharɓa gumi duk yayi zuru-zuru, idanunsa ne suka kai kan Alhaji Babba cikin kewar ɗan uwansa yace, " Yaya Alhaji kazo ka agazamun "
Alhaji Babba matsawa yayi baya har tuntuɓen harshe yake ya ce, " Kai waye yayen naka Ka roƙi Allah ya agaza maka domin ni babu abinda zan iya yi maka "
🤣🤣🤣🤣🤣🤣 MU HAƊE A COMMENTS, WAI TUN DAGA FARKON LABARIN NAN ZUWA WANNAN SHAFIN WANE GURI NE YAFI BAKI DARIYA??🤣🤣🤣🤣
KACOKAN WANNAN SHAFIN NAKI NE MUM AMNASH ( MARUBUCIYAR SO KO WAHALA ) KIYI YANDA KIKE SO🌚🌚🌚🌚
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
YOU ARE READING
WANDA BAI JI BARI BA....
Short StoryIska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin...