*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
( _Wankan Abaya Dole_)BY
*AMEERA ADAM*
*AmeeraAdam60*
*@Wattpad*DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼
11&12
Umma har cikin zuciyarta take jin kukan Yusra saboda ganin yanayin da ƴarta ta take ciki ba ƙaramin tausayi ta bata ba, ƙara rungumeta tayi a jikinta tana shafa mata bayanta har zuwa wani lokaci.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka sannan Umma ta ɗaga da niyyar yakice ta aikuwa gam Yusra ta riƙeta tana faɗin, " Umma wallahi ni tsoro nake ji "
Umma shiru tayi sannan ta dafa Yusra ta ce, " Ki daina jin tsoro Yusra ba abinda zai sameki sai alheri kiyi addu'a babu abinda yafi ƙarfin ayar Allah " Gyaɗa kai Yusra tayi sannan Umma ta samu ta yakiceta ta fita domin gabatar da alwalar sallar asuba.
Umma na gaba Yusra na binta a baya tana ɗan waige, Umma alwala tayi itama Yusra tayi alwala sannan ta koma ɗakinta, Umma ɗakinta ta koma bayan ta shiga kayan aikin Abba ta gani a tsakar ɗakin a warwatse kowanne da inda yayi, girgiza kai tayi sannan ta ce, " Au Malam yanzu sai da ya fito da waɗannan kayan tsubbun " kallan kan gadon tayi taga baya kai ta kuma cewa, " Malam ko ya fita masallaci ina ɗakin Yusra? amma fa banji motsinsa ba ko ya rigani tashi ne " tana gama magana ta tattare su gefe ta ɗauko zani ta rufa musu akai sannan ta shimfiɗa dadduma ta fara sallah.
Yusra bata gama samun nutsuwa ba sai da ta idar da sallah sannan ta fara addu'o'i wani tunani tayi sannan ta miƙe ta ɗauko Kur'aninta da duk yayi ƙura ta gogeshi ta fara karantawa, izu guda ta karanta sannan ta ajiye carbi ta ɗauka tana ja daga haka bacci mai daɗi yayi gaba da ita.
Umma bayan ta gama laziminta komawa tayi kan gado ta kishingiɗa amma cikin zuiyarta tana mamakin rashin dawowar Abba daga masallaci har gari yayi haske, amma sai tayi tunanin ko sun tsaya ɗan tattaunawa ga me da da abinda ya shafi harkar masallaci.
Kimanin ƙarfe bakwai da rabi na safiya sukaji bugu a ƙofar gida har zuwa lokacin Yusra bacci take sai a lokacin bugun gidan ya tashe ta, Umma ce ta ce mata taje ta buɗe domin a tunaninta Abba ne.
Yusra na buɗe ƙofar taci karo da Yayan mahaifinta Alhaji Babba, tsuke fuska tayi saboda Alhaji Babba irin matanen nan ne masu faɗan gaske sau tari idan har ya tako yazo to sun san ba banza ba.
Ciki-ciki Yusra ta gaidashi tana ɗauke kai gefe, Alhaji Babba sakin baki yayi yana kallan irin gaisuwar da Yusra tayi masa cikin masifa ya fara magana.
" Ke kalleni nan kinga nayi kama da abokin wasan Ubanki? Nace kinga nayi kama da abokin wasan Ubanki? " Ƙara tamke fuska tayi ta ce, " A'a " Jinjina kai Alhaji Babba yayi ya ce, " To ko Ubanki Auwalu bazai yi mun irin gaisuwar da kikayi mun ba bare ke ƙaramar alhaki, ki shiga gida ki kiramin Ubanki zanji idan shi ne ya baki lasisin ki gaisheni cikin rashin ladabi " Yusra bata bashi amsa ba ta wuce ciki aikuwa kamar ta watsa masa ruwa haka ya dinga surfa ruwan masifa.
Yana nan tsaye Umma ta leƙo soron sanye da hijabi, cikin giramamawa ta tsugunna ta gaisheshi ya amsa sannan ya ɗora da cewa.
" Saratu turomun Auwalu ina san ganinsa " Umma ta bashi amsa da, " Wallahi Yaya Alhaji tun asuba da ya fita bai dawo ba kuma ɗazu na kira wayar ashe ya barta a gida nikaɗai abin yake damuna a zuciya tun ɗazu " Alhaji Babba zame glass ɗin idonsa yayi kaɗan ya ƙare mata kallo yace, " Saratu ! Saratu ! ki kiyaye wallahi nasan halinki sarai bakyasan laifin Auwalu, idan ma ɓoyeshi kikayi wallahi ina gidan nan har sai ya dawo, mu zai maida ƙananan mutane haka kawai zai ɓata mana zuri'a wallahi zamu gamu dashi karonmu bazaiyi kyau ba "
Umma gabanta ne ya faɗi jin kalaman Alhaji Babba, musamman da taji yace zai ɓata musu zuri'a. Jiki ba ƙwari ta ce masa, " Yaya Alhaji bismillah ma ga tabarma ai baka tsaya a tsaye ba " Alhaji Babba kamar mai jira aikuwa yabi bayanta suka shiga ciki.
Tabarma aka shimfiɗa masa a tsakar gida aka kawo masa kayan kari, tunda Alhaji Babba ya shiga gidan banda surfa masifa ba abinda yake yi.
Lokacin da Buhun da Abba ya ɓace daga gurin basu ajiyeshi a ko'ina ba sai kan tsohuwar rijiyar gidansu dake ɗan lugun bayan banɗaki, rijiyar basa amfani da ita sai ajiye-ajiyen shirgi da sukeyi akai, Abba gaba ɗaya a ɗaure yake kamar wanda kayiwa ɗaurin huhun goro, duk yanda yaso ya motsa jikinsa abun ya faskara haka ya haƙura ya zubawa sarautar Allah ido, sai dai duk abinda su Umma sukeyi akan kunnensa duk yana ji daga ƙarshe da ya rasa madafa fashewa yayi da kuka mai cin rai.
Yana cikin wannan halin yaji shigowar ɗan uwansa amma ba damar magana hakan ne yasa ya cigaba da kukan ga rana ta dalle gurin da yake shi kaɗai yasan halin da yake ciki.Umma tana san tambayar Alhaji Babba abinda Abba yayi sai dai kuma tana tsoron faɗansa, hakan ne yasa ta ja bakinta ta tsuke.
Alhaji Babba yana daga gurin da yake gurin yana kallan saitin rijiyar, kamar ance yakai idons gurin ya hango ƴan yatsun ƙafa na mutum sun leƙo ta cikin buhu sai kuma bayan ƙeyar mutum, abinda ya tsoratashi da ya ga kofatan ƙafafun dokuna kusan kuda goma a gefen buhun daga sama kuma babu sauran gangar jikin dokunan. Murza idanunsa ya ƙarayi yana buɗesu yayi tozali da Maguna na bullowa daga jikin bango.
Cikinsa ne ya karta tsoro ya kamashi cikin hikima ya kalli Umma yace, " Saratu waccen rijiyar kuwa kuna gyaran kayan kanta ko " sai lokacin Umma ta lura da gurin kanta tsaye ta amsa, " Eh Yaya yanzu ma nake san rage kayan gurin " ta ƙarasa maganar tana bin hanyar gurin.
Umma na tunkarar gurjn yaga Magunan nan sun taso gadan-gadan zasu afko kansa, Alhaji Babba watsar da Takalmansa yayi da radio dake hannunsa yabi hanyar waje da gudun gaske.
_ƁARE GYADA YARINYA🎼🥁🎹🎷🎺🎹🎼 ƁARE GYARE ƊAN YARO 🎼🎺🎷🎹💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 HABA ƁARE GYADA YARINYA🎼🎼🎼🎼🎷🎹🎺🥁🥁🥁YASIN RUWAN COMMENTS ƊINKU HIYSANI SAKE WANI SHAFIN YANZU🥁🥁🥁🎼💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
YOU ARE READING
WANDA BAI JI BARI BA....
Short StoryIska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin...