9&10

161 15 9
                                    

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

     *WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
     ( _Wankan Abaya Dole_)

       BY
*AMEERA ADAM*
      *AmeeraAdam60*
                    *@Wattpad*

DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*

          SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼

                  9&10


             Cikin bacci sama-sama Umma taji ihun Abba tana yunƙurin tashi ya rirriƙeta da ƙarfin gaske, a tsorace ta tashi domin lamarin ba ƙaramin tsorata ta yayi ba wai ace yau Abba ne yake ihu har yana riƙeta.

     Niyyarta ta jingina da bango aikuwa Abba na jin tana niyyar matsawa daga jikinsa da sauri yasa hannuwa biyu ya riƙe ƙafafunta, cikin tashin hankali ta kalleshi ta fara magana.

      " Malam yau me nake gani ne cikin daren nan? Malam anya lafiyarka kuwa mai yake faruwa? " Kansa sunkuye cikin zanin gado yace.

    " Saratu Aljanu ne wallahi da idona na gansu kuma ba kowa bane magen nan ce, Aljanu masu ban tsoro har ture suka mun Dan Allah karki bari su cutar dani " Umma ɗan dube-dube tayi sannan ta ce, " To Malam ko mafarki kayi ne shikuwa sharrin mafarki yawa gareshi, kayi Addua sai ka koma "

      A harzuƙe ya ce mata, " Babu wani Mafarki gata nan fa tsaye akanmu dan Allah ki taimaka mun " Umma shiru tayi tana nazari sosai abin ya ɗaga mata hankali, ada ta ɗauka wasa ne amma ganin Maigidanta na niyyar zaucewa abin ya bata tsoro.

     Ayatulkursiyyu ta fara karantawa atafin hannunta tana shafawa Abba ta jima tana haka sannan Allah yasa ya ɗan samu nutsuwa, a hankali ya yunƙura ya tashi zaune ilahurin fuskarsa zuwa jikinsa gaba ɗaya sun jiƙe wuyan rigarsa duk yayi sharkaf da gumi.

     Ganin ya ɗan samu nutsuwa Umma ta kalleshi ta ce, " Malam ni abun nan ya ɗaure mun kai jiya mukayi maganar nan fa nidama jikina ya bani nace maka anya ba ruhanai ne suke niyyar shigarka ba? "

    Abba tashi yayi yana daga kan gadon ya cire rugar jikinsa saboda zafin da yake ji da gumin da yake ta haɗawa, komawa yayi ya zauna sannan ya kalli Umma yace.

      " Leƙa ƙasan gado daga cen ƙarshe-ƙarshe akwai wannan jakar fatar damisar ki ɗauko mun ita. "

     Sakin baki Umma tayi ta ce, " Malam yanzu kayan tsibbun nan zaka ɗauko babu mai yi maka abinda Allah bai maka...." katseta yayi cikin ƙaraji yace.

       " Kayan gadon Mahaifin Kakan nawa kike kira da kayan tsubbu? Wallahi ki kiyaye Saratu "baki taja ta tsuke har ya gama faɗansa, fullo ta janyo ta koma ta kwanta.

     Abba tashi yayi saɗaf-saɗaf da ƴar fitilarsa ya leƙa ƙarƙashin gado, a hankali ya zira hannu ya ɗauko jakar fata ya hau buɗewa, wani zabgegen wuri ya ɗauko ya ɗaurashi a ƙugunsa mai haɗe da layu a jiki da wasu tarkashen guraye, wani ƙoƙon kan kura ya ɗauka ya dasawa kansa tare da wani garin magani ya dinga ɗiba yana shafawa jikinsa, wani irin turare ya ɗauko mara daɗin kamshi ya dinga yarfawa a kusurwar ɗakin daga ƙarshe ya shafe a jikinsa, ya jima yana saka abubuwansa sanannanu ya kammala.

   Tsayawa yayi cikin jarumta yana kalle-kalle kamar wanda yake neman wani abu, da alama acikin shirin kota kwana yake, Umma kuwa tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita.

       Yana nan tsaye yaji abu ta bayansa ya sureshi sama a zabure Abba yake niyyar  fisgewa amma sai ji yayi yana yawo akan iska, kamar haɗin baki lokaci guda kayan aikin nasa duk suka zubo suka faɗo ƙasa, haɗewa sukayi guri guda suka cure sai gashi sun rikiɗa sun koma Luccy.

       Abba na shirin ihu yaji gaba ɗaya bakinsa yayi masa nauyi, baiyi aune ba yaji anfara wurgi dashi ta ko ina, Abba duk yanda yaso ya ƙwaci kansa abunya gagara.

       Sai da jikinsa yayi luguf sannan ta ƙyaleshi banda maida numfashi ba abinda yakeyi ita kuwa Umma duk abinda yake faruwa ba, Abba na nan zaune wani buhu ya dinga takowa har sai da ya ƙaraso gabansa, ja da baya Abba yake buhun na ƙara tunkaro shi aikuwa yana zuwa gurinsa kamar wani ƙwallo haka aka jefa Abba cikinsa a take buhun ya hau katantawa bayan wani lokaci ya ɓace.

      Yusra ba baka sai ido duk yanda taso tserewa abun y faskara, Aljanin nan ba shi ya bayyana ba sai a wata irin alƙarya mai Ɗauke da fararen duwatsu, yanayin gurin kamar sahara sai dai su kansu duwatsun fasalinsu me ban tsoro ne ɗauke suke da zanen wasu irin hallitu.

        Zama yayi akan wani katon dutse mai fasalin ƙare sai dai gangar jikinsa irinta mutumce da ƙafafunsa guda takwas, Zaunar da Yusra yayi a gefe sannan ya kai hannunsa ya shafa fuskarta, tana buɗe ido taga waɗannan halittun masu fasalin maguna da fukafukai masu yawan gaske, daga cen gefe wasu ayarin ta gani na wasu hallitu masu fuskar tawakai sai dai ƙafafunsu irin na zakaru ne guda biyu basu da hannuwa sai wata jela a bayansu wacce kamar ita ta zame musu hannuwansu da ita suke komai.

       Kallansu yayi sannan ya fara magana, " Huwasu jinkabtiga walgahar fartafkina wasbifa kadalsin barakunwa muntarkiba kulujub darfirminsat ungarwarti Harbastinga lalingar zargire, karjalminba barsugdifa tunasgirbaki markibatir warbastu unbargitaki asgibatriya " ( Ya ku ahalina wannan itace wacce na ƙaro muku matata ce, ku cigaba da sha'anin gida tare da ita, ke Hurbastinga ke ce babba ki nuna mata komai cikin nutsuwa kuma banasan jin wata matsala a tsakaninku )

     Wata ƙatuwa daga cikinsu ce ta motsa wacce aka kira da Harbastinga kanta mai ɗauke da kan doki duk yafi girma, wata irin haniniya tayi tana hura hanci sannan ta fara magana.

     " Hatribakin waris lahir kinbas harbinta kalminsa warki tarfik " ( Dukkanmu masu biyayya ne gareka domin kaine shugabanmu ) tana gama faɗa ya jinjina kai sannan ya Kalli Yusra yace.

    " Darfif fargit bansiyati  gir kal minsat warlima garbar warkinfa yarfi kahni warginsa tarfika manani walkibasti tarmika rarraf tinba " ( Waɗannan ne matana gasu nan su Sittin ne da tara kece cikon ta saba'in, waɗance ƴaƴana ne dama na nuna miki su gasu nan su Ɗari uku ne da goma sha uku )

   Hallitar dawakan nan ne suka taso da niyyar Ɗaukan Yusra zuwa cikinsu aikuwa cikin tashin hankali ta kwallah wata irin ƙara wacce har sai da ta razana Umma lokacin har anfara kiran sallah asuba.

      Umma har kusan tuntuɓe tayi saboda tashin hankali da gudu ta faɗa ɗakin Yusra, tana shiga ta sameta ta takure guri guda idonta arufe jikinta sai rawa yake, gumi ta ko'ina keto mata yake banda surutai ba abinda takeyi, Umma ce ta riƙe ta tana tambayar Yusra tureta ta shigayi tana faɗin.

     " Dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyakeni dan Allah ku barni na koma cikin dangina Marwam dan Allah kayi hakuri na shiga Uku, Umma ! Umma ! Abba! dan Allah kuxo ku ceceni. " ganin halin da take ciki yasa Umma take ta karanta addu'o' tana tofa mata, ta jima akanta sannan Yusra ta buɗe idanta tana ganin Umma ta faɗa jikinta ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

     INA LABARIN ABBA MAI KAYAN AIKI NE?🤣🤣🤣

NIDAI COMMENTS ƊINKU KAWAI NAKE SO 👌🏻

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

WANDA BAI JI BARI BA....Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt