7&8

161 16 1
                                    

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

     *WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
     ( _Wankan Abaya Dole_)

       BY
*AMEERA ADAM*
      *AmeeraAdam60*
                    *@Wattpad*

DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*

          SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼

                  7&8

   NOT EDITED

        Cikin tsuke fuska Abba yace, " Malam Haruna kasan bama irin wannan wasan da kai dan haka karmu fara " Sototo Malam Haruna yayi yana kallan abokin nasa yanda yaga ya ɓata fuska sosai yana faɗa guntun tsaki yayi yace, " Malam Auwal ni ƙaramin yaro ne da zan zauna ina yi maka irin wannan wasan, ni babban abinda ke ƙara ɓata mun rai ji yanda ka wani sarƙafe wuyanka da mayafinta, saboda Allah yau ko Musa na guri na kaga yayi irin wannan shirmen ai kai mai tsawatar masa ne "

       Abba jikinsa ne ya fara sanyi saboda yasan Malam Haruwa bai taɓa masa koda makamancin irin wannan wasan ba, murya sanyaye ya kallai abokinsa yace, " Abokina wallahi ni bansan maganar da kakeyi akai ba dubi fa ka gani shaddata nasa wacce muka siya da kai agurin Ya'u Ɗan kasuwa " Abba ya ƙarasa maganar yana ɗago cen ƙasan rigarsa yana nunawa Malam Haruna.

       Takaici ne ya ƙara rufe Malam Haruna ganin Abokinsa ya haƙiƙance har yana nuna masa da hannunsa wani abun haushinma gurin wata ƴar totuwa mai haɗe da stones yaga ya kamo ya nuna, guntun tsaki yayi yace, " To shikenan Allah ya kyauta ni bari na ƙarasa dama Omo zan ƙarɓa a kantin Lawan " yana gama faɗa ya gegare ta gefe ya wuce Abba dake tsaye cikin sanyin jiki.

     Kamar wanda aka zarewa laka haka Abba ya dinga ɗaga ƙafarsa a sanyaye ya ɗau hanyar gida, abun da yake daɗa bashi mamaki duk inda ya wuce sai yaga mutane na binsa da kallo tsairarun cikinsu har nunashi suke a fakaice.

        Lokacin da Yusra ta koma gida fuska ba walwal ta samu Umma, aikuwa lokaci guda ta rufe ta da faɗa, Yusra tura baki gaba tayi ta ce, " Ai ni dama Umma ba ƙaunata kike ba wallahi dama nasan Abba ne yake so na amma akan mage zaki zaune kiyi tamun faɗa ai faɗa yazo ƙarshe tunda har munje mun jefar da ita " suna cikin haka Abba ya shigo ya samesu da yake maganar Abaya na zuciyarsu shiyasa baibi ta kansu ba ya kalli Umma ya ce.

   " Saratu ƙare mun kallo da kyau wane irin kaya ne a jikina? "

      Da mamaki ta kalleshi ta fara duba shi tun daga ƙasa har sama sannan ta ce, " Shadda ce mana Malam " kallan Yusra yayi itama ya tambayeta, ƙaremai kallo tai tace, " Yoo Abba ba gashi nan Umma ta gaya maka ba nidai Shadda idona ya gane mun "

      Shiru Abba yayi cikin mamaki Umma ta ce, " Malam lafiya  wai ? "

      Duk abinda ya faru tsakaninsa da Malam Haruna ya kwashe ya gaya musu, Umma murmushi tayi ta ce, " Kai wacce irin abaya a zaune ƙalau kawau dai zolaya ce yake maka " daga haka ɗakinsa ya wuce itama yusra ta wuce nata ɗakin.

          *DA DADDARE*
       Abba na zaune abin duniya ya dameshi Umma ce ta shiga gurinsa ta fara tambayarsa, cikin yanayin damuwa ya fara mata magana.

      " Saratu wannan abu yana damuna yau naje makaranta kusan Malam uku ne suka mun magana wai sunga abaya a jikina, ke harda masu zolayata ɗazu na wuce aji shida inajinsu suna cewa Malam mai Abaya, ba shiri na bar makarantar na wuce shagona abun duk ya dame ni "

     Umma ɗan canja fuska tayi ta ce, " Gaskiya kam abun akwai ayar tambaya amma fa gaskiya ni Malam wallahi banga wata abaya a jikinka ba kuma inace kan kafita har mudubi ka duba, anya kuwa Malam ba ka haɗu da sharrin shaiɗanin aljanu ba? "

       Wata uwar Harara Abba ya watsa mata sannan yace, " Saratu sai muna maganar hankali ki fara sako mun sakarci aciki, ni angaya miki Aljanu na raɓar danginmu ne ke bari kiji kin yarinyar cen Yusra hatta jikokin jikokinta babu wani rauhani da ya isa ya shafesu bareni kuma ni, ko kin manta na taɓa baki labarin Mahaifin kakanmu da artabun da yakeyi a Aljanu, ke harsai da takai ta kawo ana kiransa da MAI BUKKAR ALJANU, dan haka ki iya bakinki akaina "

      Abba ya faɗa a zafafe ƙara kallan Umma yayi ya dunƙule hannu yana dukan katifa ya ce, " Ni da kike ganina babu Ɗan iskan Aljanin da ya isa ya kawo mun matsala ba tare na shata masa layi ba, saboda duk kayan aikin mahaifin kakana suna nan ɓoye a ƙasan gado ina iya tarwatsa ƴan iska dasu "

      Jiki a sanyaye Umma tace, " Amma Malam..."

    Katseta yayi da, " Ahir karki kawo mun wata maganar banza inba haka sai na bar miki ɗakin " Umma bakinta ta ja ta tsuke tana mamakin bauɗaɗɗen hali irin na mai gidanta.

       Kimanin ƙarfe biyu na dare Yusra na kwance tana bacci hankali kwance cikin baccinta ta fara mafarki kamar yanda tayi na jiya.

       Zaune ta ke acen gefen wata koriyar ƙorama samanta lulluɓe yake da ciyayu, daga cikin tsakiyar ruwan mutumin jiya ta gani ta keto ta ciki sai dai har zuwa yanzu ta gagara ganin fuskkarsa, lokacin da ya ƙaraso gurinta tana zaune ko tsawon gwiwarsa bata kai ba, kamar koda yaushe yau ma sanye yake da ƙatuwar abaya, zabgegen hannunsa ya kai ya ɗaukota a tafin hannunsa.

       Guduwa take sanyi amma ta kasa dariya ya bushe da ita har sai da iskar bakinsa ta wurgar da Yusra cen gefe sannan ya fara magana.

   "  Tarbi kilbasar wagatin mikasbinsar faragar simtani kijajuksa garfartifa farjigansi kilmantas wakajis bilami  kalmasbira watfarkinfa rarufat misaji " ( A yau shine cikar burina domin yanxu zan sadaki da ahalina wa'adin dawwamarki tare da mu ya cika kinyi bankwana da ahalinki sai dai mu tura wata a madadinki cikin jinsinki )

     Yana gama faɗa ya girgaza kansa atake fuskarsa ta bayyana, kusan mutuwar tsaye Yusra tayi mamaki ɗauke a fuskarta ta firta, " MARWAN dama kaine? " dariya ya ƙara bushewa da ita sannan ya hura mata wata iska take ya faɗa cikin ruwan suka nutse ciki.

       Cikin daren Abba sannu a hankali ya fara jin shafa tun daga tafin ƙafarsa har zuwa tsakiyar Kansa, cikin baccinsa yake faɗin, " Saratu wani abu ne yake damunki haka? " ba rufe baki ba yaji an buga kansa a jikin katakon gado a zabure ya miƙe yana murza idanu, acen gefe ya hango Luccy ta kafeshi da ido, yana shirin magana tayi wata girgiza ta zama wata ƙatuwar hallita mai siffar dorinar ruwa, wani abu tayi mai kamar atishawa lokacin guda wasu irin gajerun hallita suka fito daga hancinta kai tsaye suka faɗa kan Abba.

    Abba na ganin tahowarsu da sauri ya faɗa bayan Umma dake bacci ya rirriƙeta yana zabga ihu.

*COMMENTS ƊIN JIYA YA SANI NISHAƊI SHIYASA NAYI POSTING YAU FATAN ALHERI GAREKU MASOYA.*

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

WANDA BAI JI BARI BA....Where stories live. Discover now