27&28

110 10 0
                                    

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

     *WANDA BAI JI BARI BA...*🧕🏻👹
     ( _Wankan Abaya Dole_)

       BY
*AMEERA ADAM*
      *AmeeraAdam60*
                    *@Wattpad*

DAGA MARUBUCIYAR
*MARWAN*
*ASEELA*
*SANADIN RAGON LAYYA*
*YAWON SALLAR HJY IYA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*ƊAN BA ƘARA...*
*INDO SARƘA*
*AND KNOW*👇🏼
*WANDA BAI JI BARI BA...*

          SADAUKARWA GA ƊAUKACIN MUSULMAN DUNIYA, INA MANA FATAN ALHERI ALLAH YA MAIMAITA MANA.👏🏼

                  27&28

         Wannan karan Malam Liman haushi ne ya kama shi cikin fusata ya tattara ƙarfinsa guri guda ya fisge rigarsa yana cewa, " Kaiiii wai saboda Allah mai yake damunku ne sai wani irin Abu kukeyi kamar ƙananan yara? Wallahi na gaji tun ɗazu kuke wahalar dani akan abu guda, bari inwuce gida inyaso sai kuyi duk yanda zakuyi " Malam Babba na gama faɗa ya ƙarasa fisge babbar rigarsa zai ƙara gaba.

     Mai Unguwa cikin borin kunya ya haɗe fuska ya cewa Malam Liman, " Ina zaka tafi bayan Masarauta bata sallame ka ba, Malam Liman kafi kowa sanin hakan Laifi ne " Malam Liman a ƙufule ya juyo ya ce, " Dama aiba masarauta ce ta gayyace ni ba, kuma Idan Laifi nayi idan ƙura ta lafa a hukuntani, ina dalili tun ɗazu ɗurka-ɗurka daku sai turmusheni kukeyi ina fama da kaina "

      Malam Babba ne ya ce, " Da gaskiyarka Malam Liman amma ai hakanma arziki ne " Malam Liman yayi farat ya ce, " Ku riƙe wannan arziƙin na yafe da shi "

      Wannan ƴar hatsaniyar da suke yi ce tasa suka manta da Abaya mai yawo, suna cikin haka Abayar ta kuma kaɗowa wajen Mai Unguwa, Sauri Mai Unguwa ya janyo Malam Liman suka dawo kan tabarma Daɓass.

    Duk yanda Mai Unguwa yaso kaucewa Abayar nan haka ta shige jikinsa zuruf, gaba ɗaya mutanen gurun kowa zuru yayi aka rasa mai bakin magana, Mai Unguwa cikin sarewa ya fashe a kuka mai tsuma zuciya, Abba da ke gefe kallan Mai Unguwa yayi ya ce.

     " Wallahi sai kayi ƙoƙarin barin wasiyya domin wannan Abayar ba ta arziki ka sa ba " Alhaji Babba dake gefe yace, " Sadaƙallahul-Azeem Ranka shi daɗe Allah ya fitar da kai "
 
    Yusra wata uwar tsawa ta buga musu sannan ta fara magana, " Ku rufe mun baki inba haka ba duk zan saka muku taku Abayar, daga yanzu duk wanda Ya saka wannan  Abayar idan muka tafi dashi bazai dawo ba. "

      Mai Unguwa na kuma jin haka ya ƙara fashewa da kuka, gurin tsit yayi babu wanda ya ƙara magana, Mai Unguwa hannu biyu ya haɗa ya tsugunna akan gwiwarsa yana roƙon Yusra, idan kaga Mai Unguwa Zaka ranke kurma ne bai taɓa magana ba.

      Malam Liman Kallan Abba yayi ya ce, " Shikenan iya abinda zamu iya ji daga gurinka? " Abba da sauri ya hau gyaɗa kansa yana tsoron ya yi magana Abaya ta kuma hawa jikinsa.

      Malam Liman na kallan Yusra ta juyar da kanta gefe, kallan tsaf yayi mata sannan ya fara magana.

      " Bawan Allah inasan inji daga bakinka, ina nufun mai yasa ka shiga jikin yarinyar nan kake wahalar da iya harda wani nata, Mai yasa ka shiga rayuwa bayan kuma kuna da naku ƴanmatan a cikin jinsinku, baka ganin zalinci ne shiga rayuwarta da kayi? "

     Yusra Zaro idanunta tayi waje kamar zasu faɗo ƙasa gasu jawur ta ce, " Ita ta zaɓi haka kuma babu wanda zai rabani da ita tunda na riga da na biyata sadakinta, Abayar da na bata itace sadaki kuma taji ta amsa, ban tilasta ta ba da amincewarta muka ƙulla yar jejeniya "

     Malam Liman gingina kai yayi ya ce, " Inasan nasan kai ɗin waye kuma musulmi ne ko kafiri kuma a wane guri ka haɗu da ita? "

        Yusra gyara zamanta tayi sannan ta cigaba da cewa, " Sunan da kowa na cikin Jinsinmu ya sanni da shi shine HURBATU YANZULAK JALBALSIKAGO na fito ne daga masarautar GADBASGAJI, bari nayi maka gwari-gwari Ni ɗa ne ga wani gawurtaccen Aljani YANZULAK, Kakana JALBALSIKAGO shi ne sarkin nahiyarmu na gaji sarauta ne daga gurinsa sakamakon Mahaifina da baya raye.
         Na rayawa zuciyata zanyi ta bibiyar Matan Bil-Adam na dinga ɗaukan fansa, saboda ta sanadinsu ne na rasa mahaifina wanda yake laƙabin sunan mutane MARWAN (MY FANS NASAN KUN KARANTA LITTAFIN MARWAN WANDA BAI KARANTA BA ANYI BABU SHI ) Kuma na zaɓi amfani da sunan MARWAN ne saboda da wannan laƙabin Mahaifina ya bar duniya,  Kamar yanda Maihaifina shi kaɗaine agun Mahaifinsa nima ni kaɗaine agurinsa sai dai ni munsha banban dashi domin ni Allah ya azurtani da Iyalai masu yawa "

     Malam Liman kallan mamaki yayi wa Yusra ya ce, " Lallai kuwa ashe kaima zaka bi sahun mahaifinsa muddin bazaka rabu da ita ba "

       Murmushi Yusra tayi Marwan ya cigaba da cewa, " Malam kenan, yanzu da mutuwar Mahaifina ba'a fi ƴan watanni ba amma nayi tarayya da ƴan matanku na Bil-Adam babu adadi, karkayi tsammanin ni kaɗai ne sam ba haka bane Mahaifiyata na bani ƙwarin gwiwa ɗari bisa ɗari, saboda duk duniya babu wanda Mahaifiyata take so kamar mahaifina, saɓanin shi da har ya mutu baya jin sonta a zuciyarsa, tana masa biyayya duk abinda yake so to ko bata so dole tayi, hakan ne yasa Mahaifina ya kaimu cen tsuburin alƙaryarsa acen Mahaifiyata tayi rayuwarta ita kaɗai har Allah ya kawo ni, bayan haihuwata da wasu shekaru ne Mahaifina ya ɗauko mu ya maida ni cen masarautar GADBASGAJI a sirrance, saboda yace muddin ƴan uwan Mahaifinsa suka san yana da ɗa a raye sai sun hallakashi, kar injaka da nisa Malam liman kafin nazo nan munsha artabu da sauran Malamai "

🤣🤣🤣INA MASOYAN LITTAFIN MARWAN GA FA ƊANSA YA DAWO KU HITO KU ZUBO RUWAN COMMENTS, DAMA HAUSAWA SUNCE KYAWUN ƊA YA GAJI UBANSA🤣 MARWAN ƊAN MARWAN, HARBATU YANZULAK JALBALSIKAGO🤣🤣🤣🤣

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

WANDA BAI JI BARI BA....Where stories live. Discover now