ONE

2.9K 71 14
                                    


ƘAUYEN BURBUWA DAKE ALBASU A KANO

Tsaye take a gaban wani gadon ƙarfe, ta jawo bakkon kayanta, wanda duk rabi atamfa ce, gaba ɗaya kuma sun kuɗe,
Wata kuriyar atamfa ta zaro daga cikin bakkon kafin ta nemi waje ta zauna a saman gadon ƙarfen ta rafka uban ta gumi,
Inna ce ta ɗaga labulan ɗakin ta shigo tana faɗin "Saleme!! Saleme!! Ke Salame!!"
Cak ta tsaya baki buɗe saboda arba da tayi da Salame a saman gado, anci uwar ƙwalliyya bakinta ya sha kantakile, abarka da baƙar mace, Jambakin ya fito yayi raɗau dashi,
Ga wata baƙar jagira da tayi tun daga saman girarta har zuwa wajan kunanta,
Salati Inna ta saki tace.
"Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa ni Karimatu, mene haka kin ɗauki kaya kin sanya su a gaba? Ko kuma dandalin ne ba zaki ba?"

Hawaye ne ya sakkowa Salame a hankali ta sanya bayan hannunta ta share, kafin cikin tura baki gaba tace.
"Inna gaskiya na gaji na fara gajiya, haaa saboda Allah ni kaɗai ce a ƙauyen nan banyi ba, ko dai baki kikai min ne bani da labari? Wannan ai mugunta ce"

Baki Inna sa saki saboda lamarin Salame ya fara bata tsoro yarinya kamar mai aljanu, gyara tsaiwa tayi tace.

"Yau ni naga Abinda ya ishe ni,Ni zan maki bakin dan gidanku? Tukunna ma me akai maki kike kumfar bakin nan? Kin wani lafta jambaki sai sheƙen baƙi kamar bayan tukunya"

Zubbur Salame ta miƙe tsaye tare da cire zanin jikinta tayar, cikin tarin damuwa tace.

"Haba Inna, kalli ki gani, ace duk ƙauyen nan nice kaɗai bani da nono, gaskiya na gaji kawai ki faɗa min yadda zanyi na sami nono Nima, yooo wannan ai baƙin ciki ne, naga dai ke gana ki nan a jikin ki sai ace ni ba zanyi nono ba"

Baki Inna ta saki, mamaki kuma da tarin Al'ajabi ya hanata faɗin komai, ganin yadda Inna tayi ne yasa Salame matasa kusa da Inna tana sakin kuka tace.

"Wallahi ina nono na keso Nima, jiyan nan Inno take faɗa min ta fara nono ba kigani ba, kamar tumatir abin sha'awa, gashi har ankawo kuɗin auranta, wallahi kiyi min nono Nima"

Waje Inna ta samu ta zauna domin ta fahimci abin na Salame babba ne, Yarinyar ƙarama da jarabar tsiya, wacce kalar lukutar masifa ce wannan? Muhammadur Rasulullah (S.A.W) wani Numfashi ina ta sauke tace.

"Kowa kika gani da nono Allah ne ya bashi, gaba ɗaya shekarun ki nawa a duniya? Da zaki tsauwalawa kanki akan wani nono"

Hannu Salame tasa a kan fatar nononta tana ja sai kuma ta saki tare da kwanciya a wajan ta shiga zunduma ihu tana faɗin.

"Wannan ai mugunta ce, gari kowa da nono nice za'a ace babu, wallahi bazan yarda ba"

Ganin abun Babba ne, ya sanya Inna cewa "nono kike so?" Da sauri Salame ta ɗaga kai tana share hawaye, Inna tace "Shikenan za kiyi Nono kwanan kinji ko, na maki al'ƙawarin amma sai kin nutsu kin kama kanki" da sauri ta sanya hannu ta kama kanta tana faɗin "wallahi Inna indai zanyi nono komai kikace zanyi ni ko fita tsirara ma zan iya indai kince nayi"

Haɓa Inna ta riƙe tace "ohhh yau na shiga naga abinda yake shirin fin ƙarfina, cewa nayi ki daina haukan da kike gashi nan ko makaranta kin daina zuwa idan kuma kina son yin nono dole kiyi karatu"

Da sauri ta Miƙe tare da ɗauko wasu kurayen Uniform ta sanya tace "Uhm kin tuna min da wani abu ba, wallahi zai yaci uwar data kawo uwarsa duniya, zai sani dani yake zan can"

Wasu kurayen Uniform ta sanya a saman baƙar fatar jikinta, kafin ta ƙara lafta jambaki, tace "Inna samin Albarka"

Girgiza kai Inna tayi kafin tace
"Allah ya tsare ya kiyaye dan Allah kada ki ɗauko min magana"

"Uhm"
Kawai Salame tace ba tare data ƙara cewa komai ba ta nufi Burbuwa primary school tana zuwa ta samu Malam  Ɗalha yana dukan makara, ihu ta fara tana faɗin.

"Dan manzon Allah kada ka daken, dan makarantar gaban Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, dan soyayyyar da kakewa Uwarka"

Jin zagin data Rafka masa ne yasa ya shiga dukanta tana sakin kuka, bayan ya gama ya kurata Aji.

Babu laifi tana ganewa Malamin na cikin karatu inda yake cewa "Grammar is the art of putting the right word in the places"

Ɗaga manyan ɗuwaiwanta tayi ta saki tusa ji kake Fuuuuuuuu dummmmm fittttftt

Gaba ɗaya suka juya suna Kallonta harara ta makawa ƴan ajin kafin tace.

"Haaa Meye aka tsare ni da idanu? Tusa nayi idan ɗuwawun wani sai a faɗa min"

Girgiza kai kawai Malamin yayi yaci gaba da karatu, bayan an tashi ne suka fito a gajiye Salame tace
"muje bayan makaranta mu samu mangwaro"
Gaba ɗaya suka nufi bayan makaranta suna zuwa idanun Saude ya sauka akan Malam Ɗalha da sauri tace.

"Kalli Malam Ɗalha yana kashi wai baho ji ɗuwawu"

Gyara tsaiwa Salame tayi tace
"kuzo muje yau zaici uwar tada haifi uwarsa"

Gaba ɗaya suka bi bayanta zare ido Salame tayi tace "kan Uba Maciji"
Jin ta ambaci Maciji ne ya sanya Inno kallon wajan da sauri taja baya saboda ganin Zabgegiyyar abar Malam Ɗalha tana lilo a ƙasan wandonsa, ita kam tasa ba Maciji ne ba.

Saude ce tace "mun shiga uku Zai saresa fa"

"Bari na taimaka masa badan halinsa ba"

A hankali ta nufi inda Malam Ɗalha yake tsugune yana kashi, kafin Saɗaf saɗaf ta mika hannu Zaraf ta cafke kan Abar Malam Ɗalha wacce take lilo a ƙasa Saboda zame wandon da yayi.

Ihu ya kurma tare da faɗin
"wayyoooo na shiga uku Za'a cire min Ɗalha ɗita"
Salame kan ƙara riƙe wa tayi gam ganin zata cille tace "Saude nemu min Sanda yanzu nayi akin Allah na sare kan Macijin nan😂...

   IDAN AKAI COMMENTS AKAI WATSA BOOK ƊIN A MEDIA TABBAS AKWAI POSTING KULKUM.

YAYA KUKA JI LABARIN??
MENE RA'AYINKU AKAI???

SHARE SHARE💃🏽

KWAILA CEWhere stories live. Discover now