FOUR

1K 27 0
                                    


"Ciki kuma?"
Inna ta ƙara faɗa tare da riƙe haɓarta cikin Zallar tashin hankalin daya kasa ɓoyuwa a saman fuskarta ta.

Cikin kuka tare da narke fuska Salame ta ƙara duban Mahaifiyar ta tace.

"Nasan bazan wanye lafiya ba, idan baki haife min ba, Ciki ne dani, amma dan Allah Inna kada ki ƙwace ɗan ki bari nayi taimako na shayar da shi dan Allah Inna kinji, Innata Baiwar Allah!?"

Ta gumi Inna ta zabga, tama kasa tantance wanne irin abu ne yake damun Salame, Hauka ne ko kuma zallar ƙuruciya da kuma tarin wawta? Domin Abin nata ya huce tunanin dukkan mai tunani, ta fahimtar dukkan mai fahimtar abu na hankali da kuma hikima, zuwa yanzu tafi yarda cewa, eh Tabbas da gaske aljanu ne suka shafi jikarta ta!

"Inna yaya kikai shiru, wallahi daga wannan cikin bazan ƙara wani ba, wannan tsautsayi ne, da kuma rabon nayi Taimakon rai na shayar da wannan jaririn nono na"

Girgiza kai Inna tayi saboda Zallar jimami da kuma ta'ajjujin da yayiwa zuciyarta yawa kafin a hankali kuma ta sauke ajjiyar zuciya cikin damuwa dake damun zuciyarta tace.

"Salame ciki fa kikace? Kin san mene kike faɗa kowa? Kin san irin faɗuwar gaban da kalamanki suka haifar a Zuciyata kowa? Ko kuma so kike ki kashi ni da raina? Ko kuma ta ƙamarki cewa ina sonki bazan iya yi maki komai ba, wallahi da ance iyayanki suna raye a yau saikin bar gidan nan, dan butar Ubanki, kuma ki faɗa min inda kika samu ciki a irin wannan lokacin?"

Washe baki Salame tayi tana mai tattare rigar Jikinta tare da ɗagata zuwa sama, tana mai nunawa Inna lafaffan cikin nata tace.

"Wallahi Inna, a makaranta ne naga Malam Ɗalha yana kashi, kawai sai naga Maciji shine naje zanyi taimakon rai, shine fa yace wai ba Maciji bane, wai Ɗalhar sa ce, kuma Inno tace idan aka taɓa abar ciki ake, dan Manzon Allah ki yafe min wallahi tsautsayi ne, kuma kin Sanni da imani da kuma tausayin da yayiwa zuciyata yawa, shiyasa naje na taimaka masa, amma saboda rashin tsoran da kuma mugunta irin na mutane ya bari ciki ya shiga cikina da wannan ƙatuwar abar!"

Hannu ina ta shiga tafawa kafin ta riƙe haɓa tace.

"Allah ya bani ƴar bai bani halinta ba, wacce iskanci da wulaƙancin naki harya kai mutum yana  tsuguno kije ki leƙa sa??"

Turo baki Salame tayi tana faɗin.

"Ohhhu! Nima na sani, naga dai shine ya daken, yawwa Inna dan Allah yaya sunan abar saboda gaba na riƙe sunanta, kai amma Malam Ɗalha yaji daɗin sa, yana da sanda duk wanda zai dakesa sai dai kawai ya ɗauko ta ko Inna?"

Tashi Inna tayi domin lamarin ya farara gigita dole ta nemuwa Saleme taimako wajan Malami, kafin a hankali ciki kuma ɗan ɗaga Murya tace.

"To wannan cikin badai ki haifi Mutum sai dai ɗan Maciji, shasha!!! Mara kamun kai, zanyi maganinki wallahi bari na kira Karime tazo ta tafi dake birni kije can dangin Ubanki bazan iya da wannan lukutar masifar ba"

Kuka Salame ta sanya tare kwanciya a ƙasa ta shiga birgima kafin ta zabura tayi waje tana sakin kuka.

*****
A hankali yake driving cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda ruwan samaniya, mai man yan zane, ya ɗura hula zanna bukar a saman lallausar sumar kansa!

Dugwayen gashin idanunsa (eyes lashes) yaja zuwa ƙasa kafin a hankali kuma ya lumshe gajiyayyun idanunsa, wanda sukai masa nauyi.

A hankali ya fara danna (horn) ƙarar mota, domin ƙara suwarsa kenan, bakin gate ɗin tafkeken gidan nasu.

Da sauri Gate keeper (mai gadi) wanda yake zaune saman bench ya tashi yana mai ajjiye Redio hannunsa, a saman bench ɗin gefen inda ya tashi.

Buɗe gate ɗin yayi, Zannur dake zaune cikin mota ya ɗan gyara zamansa tare da sauke ajjiyar zuciya, yana jin yadda gajiye duk tafi ta saukar masa.

Kai tsaye ya tura hancin motar cikin katafaran compound ɗin gidan, yana shiga kuma ya nemi parking lot, bayan yayi parking kuma slowly ya fito da ƙafafuwansa zuwa Wajen motar.

Kai tsaye kuma yana ɗan sauke ajjiyar ya nufi cikin gidan nasu, a Parlo ya tarar da Hasenat, tana ganin tace.

"Wlcm back bro"
Kai kawai ya jinjina mata, yana mai taka strains ɗin da zai kaisa part ɗinsa, yana shiga kai tsaye bathroom (ɗakin wanka) ya shige bayan yayi wanka ya fito ya shirya cikin wata dark blue ɗin Armless da long sleeve jeans mai santsi.

Marai-raice fuska yayi yana mai ɗan kwaɓe fuska, kafin ya kwashi wayoyinsa ya nufi downstairs (ƙasan bene) tun daga sama ya fara faɗin.

"Ummi! Ummi I'm back yunwa"
Ya faɗa yana mai zama a ƙarshen stairs ɗin, tare da langwaɓar da kansa gefe.

Ummi dake can dinning area ta fito fuskarta ɗauke da Murmushi kafin tace.

"Babana baka girma, nasan tsirfa gareka, shiyasa nake maka abinda zaka iya ci"

Jinjina kansa yayi kafin ya miƙe zuwa dinning area yana faɗin.

"Barka da gida Ummi"
Kansa ta shafa tace "yawwa Babana, yanzu Abbi yake tambayar ko lafiya? Ya jika Shiru"

Lumshe idanunsa yayi lokacin daya sanya meet shawarma a cikin bakinsa, yana faɗin.

"Allahamdulillah, Ummi ki samin albarka na samu wata primary a ƙauyen Burbuwa"

Kallonsa tayi da Mamaki kafin tace.
"Outhman mene ka rasa a rayuwarka? Iya compound ɗinka na 9ja sunkai 10, mene yasa kake son kanka a super ne? Wannan abun naka is too much"

Ya ƙare maganar cikin Emotional sound wacce take nuna damuwar dake ranta, Shiru yayi dai daya gama cin abincin kafin ya dawo kusa da ita yace.

"Ummi idan ban san wahalar da ma'aikata suke sha ba, tayaya zan iya fahimtar halin da suke ciki harna kyautata masu? Please Uwa ta gari, kawai kisa albarka 2weeks kawai zanyi na dawo kinji Momma"

****
Salame tafe da sanda a hannunta tana ta tsalle tare da faɗin.

"Ƴan Makarantar bukoko, ba karatu ba Sallah sai yawan....,"

Maganar ce ta sanya saboda gano Malam Ɗalha da tayi, cak shima ya sanya tsoro da fargaba duk sun cika masa zuciya, kafin wane wani abu tuni ya sanya hannu ya riƙe gaban wandonsa.

Da sauri Salame ya ƙarasu wajan tana faɗin.

"Allah Sarki Malam Ɗalha bawan Allah, yaya kake da Matarka da uwarka??"

Zare ido yayi saboda zagin da yaji tayi masa, da bakinsa na rawa yace.

"Suuuu, suuuuu! Suna lafiya ƴar nan ya gida"

Washe baki tayi tace "to Allah yayi baka albarka, yawwa daman nace yaya sunan wannan abar mai kama da Maciji???"

Girgiza kai yay yace "mekenan?"
Harara ta watsa masa kafin tace.
"Wanna abar mana..."
Bakinsa na rawa yace "ohhhhoo Sunanta Ɗalha.......😂.

More comment
More share
More typing

Very short story😛

KWAILA CEWhere stories live. Discover now