Kafin ta kai ga ɗaga rigar jikinta Zain ya tashi rai a matuƙar ɓace ya sanya hannunsa tare da wanketa da wani mugun bari.
Kafin tai wani yunƙuri ya ƙara kifa mata mari a gigice tayi kansa tana kurma Ihun azaba ta wani dafe fuskarta.
Gaba ɗaya tayi kansa abokan nasa kuwa da idanu kawai suka bisa suna san ganin ikon Allah.Ƙanƙamesa tayi sosai kamar zata shige jikinsa tana wani irin fashewa da kukan azaba kafin tace.
"Wallahi ko zaka mutu ni matar kace sai ka aure ni, wannan cikin na jikina ina zan kaisa bayan sau biyu kana min ciki wayyoooo Allah Shikenan kuma sai duniya ta zagen bayan kai ne mijina"Wani kalar zare idanu mutanan wajan sukai suna shiga kallon juna, sun san cewa Zain yana kula mata amma ba ko wacce ba domin duk abinsa ko kiss bai taɓa yiwa mace ba, tsakaninsa dasu kawai ya samu nutsuwa maitarsa ta kwanta bai taɓa zina ba, kuma dukkan abinda ya zame sa mahaifiyarsa itane sanadi.
Zain kasa magana yay sai wani wuci da yake yana zuciyarsa na wani irin tafasa
Sakinsa Salame tayi ta kalli Bilyam tace.
"Dan Allah wake da gsky a cikinmu, Meye laifina dan nace ni matarsa ce, dan Allah ko taimakamin ya amshi cikin nan kada aimin dariya"Gyara zama Bilyam yay yana ƙunshe dariyarsa kafin yace.
"Gaskiya baki da wani laifi, Allah yay maki basira da hankali"
Wani kalar washe baki tayi daya sanya Salman toshe hanci tace."A toh! Kai dai uwakar tayi dacen haihuwa wallahi"
Zare ido Bilyam yay kafin ya kalli Zain yace.
"Abokina ka amshi cikin nan mana kaji? Haba yarinya tsaleliya haka"
Wani mugun kallo Zain ya watsawa Bilyam yana jin wani tarin haushi da tsanar Salame.
Wata ƙyakkyawar tsawa ya daka mata da sauri ta fice jikinta na rawa."Wallahi Zain kada reshe ya juye da mujiya Wannan Yarinyar tab" cewar Salam
Bilyam kuwa Miƙewa yay yace "Ai kayi mata kallon tsaf tana da kyan diri kawai haukan ƙauye ke damunta kuma jikina ya daɗe da bani cewa akwai iska jikinta"
Shi dai Zain ko kallon su bai ba daga ƙarshe fita ma yayi daga cikin parlon ya nufi cikin gida.
Yana zuwa ya tarar da Mamy zaune a saman table tana yin dinner fuskarsa babu walwala yace.
"Mamy who is she? Wacce Wannan mahaukaciya wallahi ko a fitar da ita daga gidan nan koni nabar gidan, ƙinƙi yi min aure tun ina ɓoyewa na faɗa maki abinda na keso, ina da kuɗi ina da hankali ina da ilimi dukkan abinda ake buƙata wajan namiji ina dashi, dan Mamy ki taimakamin kada kisa na ɓata yaran mutane ki amince Kimin aure na tabbatar da ace mahaifina na raye da yay min abinda na kedai wallahi aure na keso"
Ya faɗa kamar zai kukaMurmushi Mamy tayi kafin tace "Tun jiya nayi maka mata a takaice dai a jiyan aka ɗaura auran ku kai da ita be happy dear".
Wani irin lumshe idanunsa yay yana wani irin kalar daɗi bashi da damuwar ko Wacece burinsa dai kawai ya samu halaliyarsa cikin rawar murya yace."Mamy wa kika aura min?"
Ba tare data kallesa ba tace "SALAME🙆🏾♀️😳...*TSINTACCIYA*
love and romantic story masoya *KWAILA CE* show me some love ai payment book ɗin TSINTACCIYA akan fara shi mai sauƙi kada ko manta a grp ɗin Vip na Tsintacciya za'ai class ɗin We are all Women😍😍 manyan mata a shirya tafiyar ta musamman ce ehyee.Nrml grp 300
Vip 500 posting safe da yamma da class ɗin we are all Women via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 😇muje zuwa.Dan Allah babu dole wanda yaga zai sai littafina domin ya fitar na yafe kada ya siya please👏🏻👏🏻.
http://wa.me/+2348119237616