"Rigar nono?"
Tsohon ya ƙara tambaya yana ƙarewa Salame kallo.Gira ta ɗaga masa tana ɗan girgiza ƙirjinta irin yaga how big they are! Kafin kuma tace.
"Eh! Ita zaka ban, Allah yasa kana da irin manyan nan, bana son na ƙana nan yara, maza ɗauko"
Jinjina kansa mutumin yayi cikin son yin abinda tace yace "To wacce ta aiko ki wacce number tace maki? Kada a mata wacce zatai mata yawa ko kaɗan ko yarinya?"
Hannu tasa ta riƙe ququnta tana masa kallon tara saura kwata kafin tace.
"Kamar yaya? Kaga Malam kada ka ɓatan rai, dai-dai nono zaka ɗauko, idan ba zaka gane a haka ba sai na nuna maka"
Zare ido tsohon yayi, wani matashin saurayi dake gefensa kowa, kashe Redio yayi domin yana son yaga ƙarshen wannan Chapter.
"Haba yarinya guda nawa kike? Allah ya tsare ki dayin Mama yanzu"
Cikin sauri harda kumfar baki tace "Ba'a min ba ɗan baƙin ciki, saboda matarka tana dashi shine ni kada nayi, to ai na daɗe dayin nonon Saude riƙen kuɗin na nuna masa"
Ta faɗa tana miƙawa Saude kuɗin hannunta tare da sanya hannunta ta tattare rigar ta jata can sama, nan take fatar nononta ya bayyana har wani ya mushewa yake yana tattarewa waje guda saboda rashin shafa wadataccen mai a jiki, babu komai sai ɗan gun tun fatar nan.
Habawa mai saurayin nan zai idan ba dariya ba, hadda faɗuwa daga saman benci, dry yake sosai yana nuna Salame da hannu kafin yace.
"Ina ruwan Yawale, kan uba"
Sai ya ƙare ɓarkewa da dry.Tsohon kowa girgiza kansa kawai yake yana Murmushi kafin yace.
"Ƙuruci kenan dangin hauka, haba ƴarta ina abin yake? Kiyi haƙuri ba sauri ake ba ai, yanzu kam babu abinda zaki sawa riga a nan"
Hannu tasa akai tana zunduma ihu kafin ta kalli mutumin tace.
"Dan Manzon Allah a ina zan samu Nono, ashe ina munafurta tayi, Malam tunda kana sai da rigar dan ka faɗa min inda ake sai da Nonon ina da kuɗi da yawa"
Dry ce ta kama tsohon ya daure ya hana kansa dryar, kafin yace.
"To shkknan zan tambayo maki, idan sun kawo irin naki zanzo har gida na faɗa maki"
Da sauri Salame tace "Yawwa dan Allah, ka zaɓo min irin manyan nan kaji, kuma rigar nonon ma ka ajjiye min wannan ƙatuwar"
Shidai Tsohon jinjina kai kawai yake yana binta da to, har zata juya kuma sai tace.
"Yawwa rigar akwai irinta nonon Inno kowa bari ka gansa"
Baya Inno taja tace "a'a ni bana so dan Allah ba sai an nuna ba"
Tsaki taja tace.
"Dan ma zan taimaka maki? Idan baki saka masu riga ba to yanzu mai Nonon kwance wa zai yi""Nidai bana so, dama zai ɗauke nifa bana son Nonon"
Ta gumi Salame tayi cikin jimami tace "to dan Allah ko zaki barmin naki? Kinji Aminiya ta"
Inno idanunta sukai rau rau kafin tace "to ai basa ciruwa"
Rangwa shi ta sakar mata kafin tace.
"Duk wani mugun abu a gindinki ya tare"A haka dai suka bar kasuwar zuciyar Salame fal farin ciki za'a siyo mata nono.
Suna tafe a hanya lokacin ana ta sallar Zhur Salame ce ta hango Mai gari yana jan sallah, ga shi sai riƙe wando yake saboda wandon yayi masa yawa.
Murmushin jin daɗi tayi kafin a hankali cikin Sa'a idanunta ya sauka akan wani ƙaton Jangwala gwada sai ɗaga kai sama yake.
Hannu tasa ta kama Jangwala gwadan ko tsoro babu, a dai-dai lokacin kuma Mai gari yakai sujja tana zuwa ta cilla Jangwala gwadan a cikin wandon Mai gari.
Wani abu Mai gari yaji ya faɗu masa, a hankali kuma abun yake karce masa Mai gari ɗinsa wacce take lilo a wando,
Hannu yasa ya rufe bakinsa, saboda wani ihu daya tawo masa, gumi ya shiga yanko masa,
Ɗagowa yayi Daga Sujjadar maimakon aji yace "ALLAHU AKBAR!"Sai ji akai Mai Gari ya fasa ihu tare da faɗin.
"Wayyoooo Zilla ziyyyata😂 Wayyoooo Allah an ciye min Hajiyayye!!"Kafin kace me tuni mutane an hau gudu, su Salame tuni sun mance da zuwa gida
_KUN TAƁA KARANTA LITTAFIN *NIMCYLUV* IRIN SU UNCLE NE, SIRRIN MU, THE NEW EMIR, MOON, AURAN FANSA??? TO A YANZU TANA NAN TANA BAJE BASIRARTA A LITTAFIN *ABU_MALEEK* WANDA A JIYA TA KAMMALA *BOOK 1* MUSAMMAN MATAN AURE KADA KU BARI LABARIN YA HUCE KU DOMIN AKWAI ƁANGAREN ZAMAN TAKEWA NA AURATAYYA NA MUSAMMAN, BOOK 1 2 3 SHINE 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616_
NASARAWA G.R.A KANO.
A hankali yake sakkowa daga saman strains cikin babban parlon nasu,
Yana sanye da wani dark blue ɗin voyal mai manyan zane wanda ya amshi fatarsa sosai,
Idanuna sanye cikin farin glass.Tun daga nesa yake kiran
"Ummi! Ummi! Ummi!!!"
Ya kirata wajan sau uku yana faɗawa saman 3seater tare da ɗan lumshe idanunsa.Hannunsa ya ɗura a saman cikinsa dake masa kukan yunwa, Hajiya Rahama (Ummi) dake kitchen ta fito hannunta na zubar da ruwa.
Kallo guda tayi masa tasan yau babu sauƙi musamman da taga fuskar a haɗe, Zama tayi gefensa tace.
"Zannur baka girma kai dai, wannan kira haka ko yaranka baza suyi min shi ba"
Kwaɓe fuska yayi tare da langwaɓar da kansa gefe yana sauke ajjiyar zuciya yace.
"Ummi yunwa"
Ya faɗa yana ɗura hannunsa a saman lafaffan cikinsa.Miƙewa tayi tace "Kai Babana yau kaga dama kenan ko, cin Abinci da sanyin safiya"
"Uhm"
Kawai Zannur yace yana mai langwaɓar da kansa gefe guda, a ƙalla zai kai shekaru 32 da Haihu amma sai abu yake a shagwaɓe.Fari ne tass kamar jini zai tsartuwa a jikinsa, duk kyansa bai kama ƙafar Abu Maleek ba.
Breakfast ta shirya masa a tray kafin ta jawo wani ƙaramin table ta sanya masa.
Tashi yayi zaune yana buɗewa yace.
"Ummi!!"Ummi dage gefensa tace "Ya akai Babana?"
Kwaɓe fuska yay yace."Ummi ƙaton ciki zai sani, i don't like it nama da safiya kamar maye"
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye tare da ɗaukan car key ɗinsa, kafin a hankali yace.
"Bye Ummi"
Baki ta saka kafin tace "to Breakfast ɗin ba?"Girgiza kai yayi yace "I'm full Ummi, sai na dawo"
Ya faɗa yana ficewa ta fahimci zaman ne bai so dan haka kawai ta juya tana faɗin."Allah ya shirya min kai Babana, Allah ya kiyaye ya kuma tsare"
Yana fita Isa driver ya miƙe key ɗin ya cilla masa kana ya nufi back seat ya shiga, yana shiga P.A na kiransa answering yay tare da gyara zaman bluetooth ɗinsa.
"Uhm kayi niyya kenan, ZANNUR when zaka fara zuwa company ɗin ka ne?"
Ajjiyar zuciya ya sauke a hankali kuma yace.
"Ina son naji yadda zafin nema yake P.A zan fara aiki ƙarƙashin wani, kafin ayi a ƙarƙashi na, what school nake son dubawa na kuyar a cikinta"..
A can ƙauye kowa Salame ce zaune a gaban Inna tana rusar kuka, kafin tace.
"Inna ki yafe min, wallahi naci amanarki, amma tsautsayi ne wallahi dan Allah kada Kice zaki daken"
Kallonta Inna tayi kafin tace
"kin daman da Shegiyar magiyar tsiya Uban me kikai kuma yanzu??"Salame tana ƙara sakin wani kuka mai cin rai kafin tace.
"Inna Ciki ne daniiii😂"
*Wallahi Wanda bai karanta Abu Maleek yana ruwa💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽 koya zata kaya tsananin Abu Maleek da Julde a daran yau???*
Nifa ba gantalalle bace ahhha! Idan ba za'ai share ba a faɗa min🤷🏾♀️🤷🏾♀️.