fifteen

1.1K 28 5
                                    

Gudu Salame take iya kar ƙarfinta har ta isa main Parlo gaba ɗaya ta shagala ta mance babu komai a jikinta, tana zuwa tsakiyar parlon taji an saka mata ƙafata.

Wata gigitacciyyar ƙara ta saki tare da ƙanƙame Jikinta waje guda gaba ɗaya ta tsorata, duk yadda takai da ƙoƙarin hana kanta faɗuwa amma ta gagara sai da taje har ƙasa.

Ta faɗi akan mazaunan ta, Zain dake tsaye bisa kan ƙafafuwansa hannunsa zube cikin aljihunsa fuskarsa babu walwala kusan Kullum tana kame kamar yadda ya saba.

Salame take zaune tayi saurin Miƙewa tsaye, tare da faɗin.

"Kai Bature mai duba nan kaga na fara nono, na samu nonon da zan bawa yaran da zan haifa na cikin da kayi min"

Wani irin fisgota yay tare da fara janta har zuwa part ɗin Mami wacce ke zaune akan kujera tana karanta sabon littafi Mai suna Tsintacciya.

Cikin ɗacin rai da kuma zafin zuciya Zain yace
"Mami rayuwata zaki kashe da Kanki, Tabbas kika tilasta min zama da wannan abar a matsayin mata wlh sai dai ki ɗauki gangar jikina ba dai ki samu numfashi, Mami ke uwa ce na ɗauka zaki fahimci kawai ci da kuma abinda yake ɓoye cikin zuciyar ɗan ki, na furta da kai na da baki na cewa aure na keso, amma mene Wannan village gal ɗin zata amfane ni dashi? Eh? Ba zan iya ba, bazan iya ba yarinya babu ilimi kullum hauka ki dubi yadda ta fito dake murna wai ta fara nono, how long I've been waiting for her? Eh? I'm so honey Mami ki tausaya min ki bari na auri dai-dai ni, ba KWAILA CE ba, ba zan iya rayuwa da KWAILA ba"

Jikin Salame na wani iri ɓari kyarma da maƙyarƙyata, ta miƙe tsaye at this time zaka ɗauka mai cikakken hankali ce, saboda yadda ta yiwa Zain ƙuri da idanunta masu kaifi wani suka kuma launin jaa kamar wacce bata hayyacinta tace.

"Mami wlh ina son Bature ko zai mutu sai ya auri ni Mami zan mutu"
Ta faɗa Idanunta na wani irin ƙafewa jikinta na rawa.

Wani babban hijab Mami ta sanyawa Salame kafin ta zaunar da ita tace.

"Zaka iya zama da wacce kake so kuma wacce zuciyarka ke muradi, amma ka ɗauki auren Salame matsayin ƙaddararka, jeka na yarje maka amma akwai ranar daza kazo da kanka"

Ta faɗi hakan tana kama Salame tare da shiga da ita bedroom ɗinta.

Tsaye tabar Zain yana haɗa wata uwar zufa, ji yay zaman 9ja ya damesa, cikin sauri ya shiga shirya kayansa ko takan Mami bai bi ba, ya fita kai tsaye kuma gidan su Zannur.

A Parlo suka zauna har lokacin kuma Zannur lafiya taƙi masa daɗi cikin dauriya yace.

"Zain kana ganin abinda kayi dai-dai ne?" Cikin ɓacin rai yace.

"Look Sannu banzo dan wani abu ba, nazo dan kayi supporting ɗina kan abinda nake shirin yi"

Murmushi Zannur yay yace "abinda kake ƙi wata rana shike wahalar dakai, shike zame maka ƙadangaren bakin tulo, accept this married as your destiny kamar yadda Mami tace"

Tsaki Zain yaja yace "wlh bazan iya ba, ƙarfe 1na dare jirgina zai tashi zuwa Massicow ina zuwa kuma zan turawa Mami, her divorce paper"

Ganin yadda Zain ya rikice yasa Zannur cewa.

"If a person is born or have destiny number 5, 6 or 7, they usually go for love marriage. These individuals can go against the wishes of their parents and society to marry a partner of their choice, ina ganin kabi abinda Mami tace zaifi maka sauƙi, soyayya  ba'a gane kanta sai taci ƙarfi a zuciyar mutum, ka kalli yadda nake neman ni ta ƙauyen ban samu ba, ina tunanin kuma ni soyayyarta itace nawa ajalin, ina faɗa maka Wannan as your friend childhood"

Miƙewa Zain yay shima Zannur ya miƙe suka rugume juna kafin yay masa sallama ya fita kai tsaye kuma airport ya shige....

Washe gari
Mami ce da Salame zaune a gaban wani babban Malami masanin jinnu kallo guda kuma yaywa salame ya fahimci, mutunan kanta sun shige tunanin Mutum domin ba Aljani ɗaya ne ke ɗawainiya da ita ba kallon Mami yay yace.

"In sha Allah komai zai dai-dai ta fara shan Rubutun nan har zuwa sati guda, duk abubuwan da kike faɗa ta nayi zata daina, hatta tusar da take bayin kanta bane"

Murmushi Mami tayi cike da jin daɗi tace "to Malam abin sadaƙa fa"
Cikin kamilewarsa yace "ki bawa mabuƙaci idan kin fita" amsa tayi ta fita tare da shiga motar ta, har lokacin kuma bata san Zain yabar ƙasar ba...
Tana zuwa gida motar Zannur na parking tsayawa tayi tana Murmushi har ya ƙarasu wajanta, dai-dai lokacin kuma Salame ta fito daga cikin motar wata kalar razananiyyar ƙara Zannur ya sanya lokacin da idanunsa ya sauka akan Salame...

*🌈NIMCY'S LIBRARY🌈*

_Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_

So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own...

Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
The new emir
Izzar so
Sai na aureta😍
Tsintacciya
E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny

Bunus ya fara 6/2/2022
Share fisabilillahi😍

KWAILA CEWhere stories live. Discover now