Kifa kansa a tsakiyar cinyoyinsa, ya shiga sauke ajjiyar zuciya, yana jin tamkar ya zunduma ihu..A wannan lokacin babu wacce yake so da kuma Muradin kasancewa da ita face Salame, idanunsa na mararin ganinta, yayinda zuciyarsa ta azabtu da rashinta.
A yanzu Salame ce kawai za iya bashi farin cikin da yake son samawa zuciyarsa, ita kawai zata maye masa gurbin daya rasa, ita zata bashi jin daɗi da kuma kwanciyar hankali ma daɗin Sunainerh.
Ya jima a wajan kafin ya tashi jiki a sanyaye ya nufi masaukin sa, kayansa ya haɗa kaf, kafin yazo wajan Mai gari ya ɗan durƙosa.
Da mamaki Mai gari yace "a'a Usmanu ya haka? Nace ya haka na ganka kamar kazar da aka silala???? Jiki duk ba ƙwari kamar an zubawa kifi gishiri, af badai har yanzun abin batun kadangaren bane ko??"
Girgiza kai Zannur yayi, idanunsa a ɗan Lumshe yana shaƙar iska daga cikin bakinsa kafin gently ya buɗe bakinsa yace.
"A'a, zani gida ne amma zan dawo"
Jinjina kai Mai gari yay cike da gamsuwa kafin yace...
"Ai duk wanda ya zuba maka wannan Jangwalen badai gantalalle bane, sai dai sallamamme, af akwai mugunta"
Miƙewa Zannur yay shi baya ƙaunar ma maganar, kuma wallahi da ace yanzu za'a faɗa masa wanda ya sanya masa Lizard ɗin da sai dai Court ta ra basu, mai taɓa tsanar mutum kamar yadda ya tsani wanda ya cutar dashi, ya sanya shi kuka a idanun duniya, rabon da yay kuka a rayuwa harya manta.
Kai tsaye motarsa ya nufa ya cilla ta saman titi ya nufi gida.
Salame
A nasarawa Kano! A nan su Inna da Salame suka sauka cikin wani ƙara faran gida na ƙarshe.Salame dake zaune tai zugun domin gaba ɗaya ta rasa wanne kalar daɗi dake ciki, wata mata ce wacce tasha ado cikin wani lemon green ɗin lace mai White ɗin Flowers.
Murmushi Hajia Zaitun tayi tana kallon tana sakin murmushi kafin tace.
"Lale! Barka da zuwa Inna, nayi farin ciki sosai da dawowar Salma nan, daman bana jin daɗin zamanta a nan yanzu sai ta fara zuwa makaranta...."
Da wani sauri Salame ta miƙe tare da nufar wajan Hajiya Zaitun tace.
"Dan Manzon Allah, dan soyayyyar Annabin rahama, dan ƙaunar da kikewa mahaifan ki bayan kin sani a makaranta ki siya min nono dan Allah!!"
Wata tsawa Inna ta sakarwa Salame hakan yasa taja bakinta tai Shiru.
Suna zaune suna cin lafiyayyan abinci Salame daɗin abinci tasa tai ta sakin tusa🤣 "wannan Abincin ko a Aljana ai sai haka, Wayyoooo su Saude kuna can ina nan ina kwasar kayan aljanna"
Sai kuma ta fashe da kuka Wanda yay dai-dai da shigowar wani haɗaɗɗan saurayi cikin nutsuwa ya shigo yana ɗan ya motsa fuska musamman lokacin da idanunsa suka sauka akan salame.
Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Zain ya sauke hakan yasa Hajiya Zaitun ta kalli ɗan nata tace.
"Ina kaje ne??? Daga dawowarka da New York sai yazo Zain"
Gaba yay a hankali idanunsa a Lumshe yana jin wani amai na tasu masa kafin yace.
"Mamy an kai Zannur hospital yanzu Ummi tace na faɗa maki, ciwon nasa yay worse amai jini fa"
Ya faɗa yana sauke ajjiyar zuciya tare da shafa cikin dake ihu yunwa.
Da sauri Mamy ta miƙe tsaye kafin tace.
"Subuhanallah, fito min da car key ɗin na, mene ya samu Babana?? Mene ya samu Zannur when ya dawo??"
Zain na watsa hannu yana shigewa part ɗinsa yana faɗin "how can i know?? Wai ko yaga Sunainerh?? Ya haɗu da Witch dai, yana faɗin yaga Sunainerh ita zai aura zai mutu idan ba ita, Mamy can you imagine wai Sunainerh a village???? Kawai yaga Aljana"
Da wani irin sauri Salame ta miƙe ta ida gaban Zain kafin cikin sauri tai....
Ga Zannur ga Zain ga Salame??? Abin zai bada onga ko🤣.
Tsaya kiji👇🏾
Upcoming book *TSINTACCIYA* Mutane Ashirin ɗin farko da sukai payment zan sanya su vip saboda Allah, Tsintacciya 300 kacal vip 500 amma idan kai payment yanzu akan 300 za'a sanyaka a vip💃🏽💃🏽💃🏽 garaɓasa via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 sai kunzo grp 1 is full mun shiga grp 2💃🏽💃🏽💃🏽