Ten

771 30 1
                                    


  _Nifa bana adding kowa a grp ɗin KWAILA CE, Idan Allah ya nufa kana ciki fine, Sannan bana turawa a prvt ko grp wannan book ɗin naga dama sunansa😂 a ɗan tsahirta min filissss_

Gabansa kafin tace.
"Kaji tsoran Allah Kai bature, tsabar ƙarya ta ina Mutum zaiga Aljana?? Amma kai dai ba haihuwar ƙasar nan bane ko"
Ta ƙare tana binsa da kallo yadda taga ƙwayar idanunsa blue.

Wani banzan kallo Zain ya watsa mata yana yin baya tare da kwaɓe fuska tamkar yaga kashi.

Yayinda ita kuma Salame ta ƙara matsawa kusa dashi tana ƙoƙarin ƙara cilla idanunta cikin nasa, saboda wani mugun birgeta da idanunsa sukai.

A ɗan hargitse Zain ya kalli Mamy kafin yace.

"Mamy who is she? Wannan mahaukaciya fa?"
Ya faɗa yana ƙara toshe hancinsa Mamy dake miƙewa tsaye tace..

"We'll talk about this later Zain, get me a key"
Ta faɗa tana ɗaukan Vail ɗinta yayinda take kallon Inna tace.

"Inna zo muje mana gidan ba kowa, kibar Salma a nan tai wanka ta shirya ko?"
Jinjina kai kawai Inna tayi kafin tace.

"To..toh babu laifi ai",
Zain na jan tsaki ya juya zuwa bedroom ɗin Mamy ya ɗauko mata key kana ya dawo parlon.

Kallon yadda yake ya motsa fuska Hajiya Zaitun tayi kafin tace.

"Lunch ɗinka baka son cin Zain? Wallahi zan ha ɗaka da Granny"

Marai-raice fuska yay kafin yace.
"Mamy yanzu zani wajan Dadda ban iya zaman gidan nan"

Sarai Mamy tasan dalili sai kawai ta share sa, Inna kam Murmushi kawai tayi.

Salame wacce ta kafe Zain da idanu da sauri tace.
"Amma wannan tsintar sa kikai wajan masu jajayen kunne ko? Lallai akwai kyau sai idanu"

Baki Zain ya buɗe da niyyar ci mata uwa ai da sauri ya toshe bakinsa saboda wata uwar tusa da Salame ta saki tana tura masa manyan ɗuwaiwanta.

Da wani sauri tai ɗiba zuwa ɗakin da aka sauke su, yayinda Zain kuma ya nufi bathroom ya dinga sheƙa amai.

Baki kawai Inna ta saki, Mamy kam dry tayi kawai sukai waje ita da Inna.

Sosai Zain ke sheƙa amai, ya fita hayyacinsa lokaci guda tsanar Salame ta zauna a ƙahon zuciyarsa, daga nan wanka yay ya sanya ɗan yan voyal fari tass  dashi, har farar fatar jikinsa ana gani.

Zuciyarsa cike da ƙuna ya nufi gidan Dadda.

A can Aminu Kano teaching hospital, Ummi ce zaune ita da Mamy har kawo lokacin kuma ba'a fito da Zannur ba.

"To Hajiya Zaitun yay zanyi? Kinfi kowa sanin zallar so da ƙaunar dake tsakanin Sunainerh da Outhman, an wayi gari babu Sunainerh, gashi kuma Munji daɗi a karo na biyu ya ƙara haɗuwa da mai kama da matarsa amma ta ɓace masa dalilin wata Yarinyar, he's critical condition idan Zannur ya mutu ya na shiga uku"

Ummi ta faɗa tana sakin kuka, Mamy shiru kawai tayi a ranta take jinjina ƙarfin soyayyar dake tsakanin zuciyoyi biyun.

Misalin 8 na dare Zain ya shigo cikin gidan, jin shiru yasa ya nufi part ɗinsa tun a Parlo ya fara sutale kayan jikinsa,
Kai tsaye ya nufi bathroom kasancewar kuma ɗakin da duhu yasa baya iya ganin komai, wanka yay sosai kana ya Fito ɗaure da towel, wani mugun bacci ne a cikin idanunsa yana zuwa gaban dressing mirror yay cilli da towel.

A hankali Salame ta ware idanunta wacce take kwace nashe nashe akan bed ɗin Zain, duk tsoron girman ɗakin ya cikata, motsin da taji ne yasa da wani sauri ta diro daga kan bed ɗin tana lalubar hanya.

A dai-dai lokacin ne kuma Zain ya juya ta nufin zuwa wardrobe babu zatu babu tsammani yaji an faɗo kansa, cikin sauri yay baya amma ina Salame ƙara riƙesa tayi tana sakin kukan tsoro yayinda cikin rashin Sa'a hannunta ya sauka bisa mararsa, a hankali tai ƙasa da hannun da wani mugun sauri ta damƙi Zain ɗinsa a gigice Zain yace.

"Auchhhiiii hyyyyyyyh"
Salame kam ƙara riƙewa tayi jiki na rawa tace "Wayyoooo Allah na shiga uku Inna Maciji yana feshi😂.

🙄Kwaila ce, Kwaila ce to bani da data ne idan kunji shiru😂 idan akwai mai turan kuma to😂😂🤷🏾‍♀️ bana son gantallan comment ai comment asha update aƙi kuma a zauna da tunanin Salame a rai.

Masu son shiga Class da zamu fara na matan aure da ƴan mata on 20/1/2022 su hanzarta magana domin mutane hamsin kawai zamu ɗauka.

Yi magana ta wannan number domin jin yadda tsarin Class ɗin *We are all Women* yake 08119237616

KWAILA CEWhere stories live. Discover now