_😂 Sadaukarwa ga dukkan jama'ar da suke karanta wannan book ɗin, billahi har raina ina matukar ƙaunar ku, ga shawara idan kun amince yau da posting gobe babu to zanna readmore 3 zuwa sama, idan kuma kullum😂 to aje a wanke hannu a sanya face mars sai abinda kuga gani😛_
"Ɗalha??"
Ta maimaita sunan baki buɗe, kai ya ɗaga mata Jikinta duk rawa yake, cikin kwaɓe fuska kamar zai kuka yace."Wallahi ni ban san sunanta ba, kiyi hqr Salame kinji?"
Dariya ta saka kamar cikinta sai ƙulle, saboda yadda taga jikin Malam Ɗalha na rawa kafin tace.
"To amma mene yasa kai kaɗai kake da wannan jelar? Allah dama zaka ban aro ni daman yau zani dandali nai wata yarinya dukan tsiya"
Kwaɓe fuska Malam Ɗalha yayi tare da ƙara damƙe gaban wandonsa yana Shirin ɓarkewa da kuka ne kuma su Inno suka ƙarasu wajan.
Ganin hakan ne kuma yasa Malam Ɗalha arta ana kare, cikin rashi sani kuma ya saki fitsarin wahala wanda shi kansa bai san dalili ba.
Saude ce ta kalli Salame tace
"Salame anyi baikon Inno yau, dan kiji auranta za'ai"
Dafe ƙirji Salame tayi sai kuma ta zube a wajan tana sakin ihu tare da faɗin.
"Shikenan, daga mai nono sai wacce za'aiwa Aure, wallahi sai na kai Inna ƙara"
Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye tare da kallon su Saude da Inno tace..
"Muje ku rakani wajan Mai gari"
Gaba ɗaya suka ranka ya tare da nufar fadar mai gari inda yake amsar korafin jama'ar garinsa.
Suna zuwa wajan Mai gari suka zube, da mamaki Mai gari yake kallonsu, kafin yaja numfashi yace.
"Lafiya ko kuma? Kuke ta zare ido menene?"
Saude ce ta zare idanunta kafin tace.
"Daman....Daman.."
Wani dake gefen Mai gari ya kalli Saude yace."Daman me??? Bana ma son shirman banza fa"
Bakin Saude na rawa saboda Maganar da akai mata mai kama da tsawa ta shiga nuna Salame da hannu tace.
"Daman Salame ce ta kawo ƙara"
Ta ƙare maganar tana nuna Salame.
"Daman na kawo ƙarar Innata ne"
Da mamaki gaba ɗaya suka kalleta tare faɗin.
"Kakar taki kikawo ƙara? Akan wanne dalili to?"
Kai ta jinjina sai kuma ta fashe da kuka wiwi tare da nono Inno da hannu tace.
"Don Manzon Allah mai gari duba kirjin Inno"
Gaba ɗaya mutanan wajan suka kalli Inno, cikin rashin sani da kuma rashin Fahimta Mai gari yace..
"Na gani,mene ya faru?"
Kuka ta ƙara fashewa dashi tace.
"Ba kaga yayi ɗan tudu gwanin sha'awa ba? Ni kuma ya kalli nawa a shafe kamar naka"
Haɗe fuska mai gari yayi tare da cewa.
"Hattara yarinya kiyaye bakinki"
Kuka ta ƙara sawa tana faɗin.
"To ita saboda Babarta tana sonta ne yasa ta siyo mata nono gashi nan gwanin sha'awa kamar tumatir, nayi nayi da Inna ta siya min amma taƙi, wannan ba mugunta bace dan Allah? Yanzu dan Allah dame zan shayar da jariri na?"
Gaba ɗaya mutanan wajan suka saki baki suna kallon Salame, dake magana da dukkan zuciyarta da kuma gaskiyar ta"
"Ke tashi kiban waje shasha!!!"
Mai gari ya ƙare maganar yana dakawa Salame tsawa.Da sauri ta miƙe jiki na rawa, ta juya baya kuma ta sakar masu wata tusa ji kake Fuuuuuuuu dummmmm fittttftt!!!!! Gaba ɗaya suka toshe hanci suna kwashe wa Salame Albarka.
***
Zannur ne tsaye sanye cikin wani lallausan baƙin yadi, mai kyau sosai wanda ya ƙara fito da kyan surarsa, idanunsa ya Lumshe yana cizon bakinsa kafin ya marai-raice fuska yana mai buɗe idanunsa tare da kallon Ummi yace."Ummi I'm full, Allah zanyi maki amai idan na ƙara"
Ya faɗa yana tsotsar laɓɓansa mai danshin yawo, Ummi dake tsaye hannunta riƙe da Mug tace."Yanzu Babana haka zaka tafi garin mutane baka son cin abinci? Gashi baka da yarda"
Ya motsa fuska yayi kafin yaja numfashi yace.
"Ummi Allah yana tare dani fa, U don't have to be worry Kinji Ummina"
Ya ƙare maganar yana ɗan yi mata ƙyakƙyawan murmushi, kafin ya cire hular kansa ya sunkuya Hannu Ummi tasa a saman sumar kansa tace.
"Allah Ubangiji ya baka nasara Babana, ya kare ka, ya kaika lafiya ya dawo dakai lafiya cikin Aminci da kariyarsa"
Ajjiyar zuciya Zannur ya saki tare da Miƙewa ya rungome Ummi, sakinta yayi yana kallon Abbansa daya haɗe fuska sosai alamar yayi fushi kafin yace.
"Sai rungumar tayi sanyi ni za'a Rungome Ni? Shikenan kuma tunda baka son addu'ar tawa"
Hannu Zannur ya sanya ya ɗan bugi kafaɗar Abban nasa kafin yace.
"Stop it Abba"
Murmushi Abba yayi yace
"ok give me a beautiful hug my friend"
Rungome juna sukai kafin Abba yayi masa addu'a, Hasenat dake gefe ta sanya kuka tare da faɗin."So! Know one's care of me, daga me rungome sai mai addu'a Allah Abba Ina kishin Yahyaaa"
Dungure mata kai Zannur yayi kafin yace
"Ohyyyah come closer dear"
Rungome ta yayi kana tai masa addu'a, waje yayi yana faɗin "Bye Ummi,Abba, sweet sister"
A haka yayi waje ya shigar motarsa kai tsaye kuma ya fice daga cikin gidan tare da nufar Ƙauyen Burbuwa dake ALBASU.****
Zaune suke cikin Asibitin ƙauyen, Inno da Saude sai Salame,
Inno ce tace.
"Layi ya kusa kanmu, Salame mene zaki faɗawa likitan"
Murmushi Salame tayi kafin tai magana an kira sunanta,
Da sauri ta miƙe tana ya tsuna fuska, mai kiran ne ya bita da ido ita kam ta maka masa harara, kana ta shige cikin ɗan ƙaramin wajan da ake duba mutane.Tana shiga likitan ya kalleta kafin yayi magana ta kwanta saman gado tare da yaye cikinta tace.
"Likita Awo nazu😂......
Sorry nifa nayi sa bisa sauke damuwa, wanda yake neman ingantaccen littafi, na zallar sarauta da zazzafar soyayya mai narkar da zuciyar mai karatu ya nemi ABU MALEEK akan 500 book 1 2 3, Soyayyar data fi ta Laylerh da Majanun kana ta huce ta TAITAINIK, uwa uba ROMOE DA JUILET🥰🥰 wannan littafin is the best musamman ga matan aure 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616
Muje zuwa💃🏽Ga Zannur zai sauka mene harshashen ku???????