Baki buɗe Likitan da Salame da yayawa ciki domin ya Auna mata yake Kallonta, kafin ya saki numfashi cikin zallar mamaki da kuma Al'ajabi yace."Ina matar da za'a na ɗin? Ohhhyahhh jeki ce mata ta shigo ba layi"
Ya faɗa yana tsare Salame da idanu, domin yana son ya fahimci gaskiyar dake idanun yarinyar, amma abubuwan da yake gani sun bashi mamaki sosai.
Salame dake bisa gado ta ƙara yaye ciki tare da turo sa gaba yace..
"Haba Ni ɗaya ce na kawo kai na yin Awo ɗin, kasan idan na faɗawa Inna ta kawo ni to wallahi ba zata kawo ni ba, baƙin cikin abinda zan haifa take, ƙilan bata son na taimaki jaririn nan ne, banda haka ban san nufinta ba, kuma ni Ubangiji da tashi ban zuciya sai ya bani ta Taimakon mutane, ina da tausayi sosai da imani, ba kuma da abin cike ba? To wallahi ka duba za kaga yadda nake da taimako abin sai ya baka mamaki"
Ta faɗa tana washe bakinta, saboda farin cikin da take ciki, kafin kuma ta ƙara zamanta tace.
"To kazo ka aunani mana? Kayi wani ƙigam, amma Malam Allah ya baka baki ina ruwan walawai"
Ta faɗa tana tintsurowa daga daman gadon marasa lafiyan saboda dariyar da yaci ƙarfinta, dariya take da dukkan ƙarfinta.
Dr Salman kam ransa ne ya ɓaci ganin yadda ya mai dashi sakarai, ga wata uwar ba'a data maka masa.
Hakan yasa cikin faɗa da tsare gida yace mata.
"Out!!!! Get out of my room shashaaaaa!!"
Ya ƙare yana jan wani numfashi, ganin yadda yayi mata tsawar ne kuma ya sanya ta miƙe tsaye tare dayin gaba da sauri kuma tai baya taɓa faɗin.
"Likita tazugenka ya faɗi"
Da wani irin sauri Dr Salman ya dafe gaban wandonsa yana zare ido, yana jin wani Fitsari na tawo masa.Sunkuyawa yayi da niyyar ɗaukan bulala, da sauri ta juya masa baya tare da tura bombom ta sakar uwar tusa ji kake Fuuuuuuuu dummmmm fittttftt.
Wani hantsilawa Dr Salman yayi nan da nan cikinsa ya juya saboda warin tusar tamkar mushe ya mutu.
Dariya Salame ta ƙara sawa tana Shirin fita daga room ɗin tace.
"Amma wallahi ba ba'a, kana da lafcecen baki uwayanka sun cuceka"
Ta faɗi hakan tana ficewa da gudu, da sauri Inno da Saude suka miƙe suna faɗin.
"Anyi maki? To yaushe ɗan zai Fito?"
Suka tambaya suna kallon cikin Salame.Sanin cewa bata ƙarya kuma bata iya ba yasa tace.
"A'a bai ba rabi da ɗan rainin hankali, da zarar nai bacci na farka ai zanga jaririn"
Haka suka ranka ya suna baƙin gate ɗin asibitin Salamd taja ta tsaya,
nan da nan kuma Jikinta ya hau rawa idanunta suka juye yayinda sukai jaa, bakinta ya buɗe ya
shiga fitar da Kumfa da wani irin gudu ta nufi kan wata mata da take tafiya da ɗan sauri hannunta riƙe da jaka,
da kuma kwali, tana zuwa ta faɗa kan matar nan ta shiga ihu da gurnani tana duka.Ihu matar ta sanya ta shiga kururuwa, kafin kace mai tuni mutane sun cika wajan, kowa ya tsaya kallo gashi gashi duk sun kwace matar a hannun Salame.
Saboda wani irin gurnani da Salamd take tana mimmiƙe wa, gashi sai dukan matar take, kawo lokacin tuni matar ta daina motsi Jikinta yay lakwas saboda ɗan ban zan dukan da tasha wajan Salame.
Wani daga can gefe ne ya ɗan yi ta maza tare da cewa.
"Ikon Allah, to me matar tayi har haka ne?"