Eight

780 20 1
                                    


Da sauri Saude ta dafe ƙirji tana zare ido kafin tace.

"Ke Salame ba ruwana wallahi, daga ganin Mutumin nan ƙarfi zai ba kamar ƴan garin nan ba, nidai Allah ba ruwana"

Wata uwar harara Salame ga makawa Saude kafin taja tsaki tare da sanya hannunta ta dungure kan Saude tace.

"Shegiya mai zubin munafukai, Allah idan baki zo munyi ba na daina kulaki banza daga taimako sai abu ya zama abin magana, ba kiga abinda yay min bane? To gaba ke zaiwa gwamma mu bashi tsoro tun yanzu yasan cewa munfi ƙarfin sa"

Da sauri Saude ta girgiza kanta tace.

"Dan Allah kada ki daina kulani, zanyi duk me kikace Kinji"

Washe baki Salame tayi tace.

"maza jawo dutsen can, bari Ni kuma na fara ɗauko ƙadangaron kinji ƴar Saude ɗita"

Haka akai Salame ta nufi wajan tarin ƙadangaron kafin Saude ta jawo wani ƙaton Dutse ta ajjiye dai-dai wajan tagar Banɗakin.

Salame na zuwa ta sanya hannu ta damƙi wani ƙaton Jangwale  wanda yaci abinci ya ƙoshi sai fasa kai yake yana numfarfashi.

Da ɗaya hannunta ta ƙara damƙar wani tana zare ido ta nufi wajan Dutsen yana faɗin.

"Saude maza ɗauko wasu ai yau sai ya gane Allah ɗaya ne, ɗan butar uwa mai suffa irinta inyamurai"

Ta faɗi hakan tana hawa kan Dutsen a hankali ta leƙa.

Lokaci Zannur ya zame farar singlet ɗin jikinsa yana ƙoƙarin zame trouser jikinsa yaji wani ya sauka saman wuyansa, a hankali kuma abin ya fara maƙale masa saboda santsin fatar Zannur na ƙoƙarin yarda Jangwalen.

Wani irin runtse idanunsa Yay a kiɗime cikin gigita yace
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"

Ya faɗa lokacin da faratan Jangwalen suka shiga kartarsa, nan da jikin Zannur ya fara rawa idanunsa suka firfito.

Saboda wata iriyar tafiya da Jangwalen yake masa, da ƙarfi yaci gaba da tafiya zuwa kan Zannur shima tsoro duk ya cika masa zuciya.

Wata razananiyyar ƙara Zannur ya saki tare da fashewa da kuka lokacin da yaji wani Jangwalen ya faɗo masa a tsakiyar fuskarsa hakan yasa cikin gigicewa yace.

"Lizard!!!! Lizard!!! Help!!!!! Somebody help me!!!!!"

Ya faɗa yana ƙara sakin wani ihu gaba ɗaya ya fice a hayyacinta tsoron da yay masa yawa ne kuma yasa Numfashinsa fara ƙoƙarin ɗaukewa.

Allah ya gani yana matuƙar jin tsoran Lizard har cikin ransa hakan yasa gaba ɗaya ya zauce ya fita hayyacinsa.

Cikin Sabon tashin hankali da kuma yadda Lizard ɗin guda biyu suke kartar masa farar fatarsa jikinsa yasa ya ƙara buɗe baki tare da faɗin.

"Is Anybody here??? Help ba Wanda zai taimaken ne??? Innalillahi Ummi!!! Abba!!!!! My Sunainerh!!!!! Zan mutu Lizard zasu kashe niiiiiiii Wayyoooo Ummina"

Salame da daɗi ya isheta yasa ta kwanta a wajan tana dariya tare da birgima, hadda riƙe ciki, ta miƙe da niyyar ɗaukan wani taji an riƙe hannunta.

A firgice ta juya da nufin kallon wanda ya riƙe ta, zaro ido waje tayi ganin saboda idanunta da suka sauka akan.

  *Bana sonki!!!!!! Har abada, akan ki a cikin rugar ku akai min bulala guda 30 saboda tsabar mugunta, memahhh ake kiran abun??? Ahhha SHAƊI, to wallahi I'll never ever loving you!! Na yarda na amincewa amma zan mayar dake Hadimata a cikin Masarautar Kanzaf, zan ɗan ɗana maki kalar nawa rashin Imanin, tunda mutanan rugar Mahinjo masu san girma da mutuncin ɗan Adam ba, haka kawai daga hanya ta kami nabi ta Rugar ku sai a liƙa bamin wata Makauniya mai warin baki da hammata God forbid! I'm professional footballer, I'm the King of Alaafin Kanzaf, Ni Jalaluldeen Tunde Muhammad Jalal ABU MALEEK idan ina da rai da lafiya sai dai ki zauna da gangara jikina ba dai Ruhina ba🙆🏾‍♀️*

_Abu Maleek An Kammala book 1 muna 2, salonsa daban yake hanzarta sabon naka domin yin karatu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali it's 500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616🔥🔥_

Inna dake tsaye tana zare ido kafin tai magana Inna taja hannunta da ƙarfi cikin sauri tace.

"Na shiga uku Inna me nai maki, Wayyoooo jama'a ko kawo ɗauki wallahi ciki zata zubar min na shigo na"

Banza Inna tayi mata tana jin wata kalar haushin Salame daya nunku a ranta, a zuciye taji gaba da janta har suka isa gida.

Ganin hakan yasa da Sauri Saude tabar wajan tana zare ido.

Kawo yanzu Zannur ya gama ficewa a hayyacinsa daga shi har Lizard ɗin a wahalarce suke.

Wata karta Jangwalen yaywa Zannur hakan yasa Zannur ya buɗe dukkan muryarsa ya saki ihu nan take kuma Numfashinsa ya tsaya tare da sulalewa a wajan.

A wannan lokacin kuma Mai gari da wani mutum ne suka ƙaraso wajan suna Magana, suna zuwa Zannur na ihu hakan yasa gaba ɗaya suka nufi wajan ƙofar Banɗakin.

Domin a tunaninsu sun ɗauka Maciji, da sauri suka hankaɗa ƙofar tare da tura kansu, a kwance suka samu Zannur sai Lizard ɗin da suke yashe gefe guda da alamar kamar sun mutu ne ma.

A gigice suka ɗauki Zannur zuwa Asibiti, bashi ya farka ba sai cikin dare wanda shima mafarkin his Sunainerh ɗinsa ne ya farkar dashi..

Sosai yay mamakin ganinsa a cikin asibiti a sanyaye ya sallah kana ya koma ya kwanta.

Washe gari
Inna ce da Salame suka shirya kayansu tsaf cikin ganer basgo, kafin Inna ta kalli Salame tace.

"Maza tashi muje na gaji da halinki Yarinyar yau dangin Uwarki zaki kwana Ahhhah"

Ita dai Salame batai magana ba haka Inna  taja hannunta suka fita zuwa tasha bayan ta rufe gidan da kwaɗo.

Suna barin gidan kuma Zannur na zuwa a gigice dan banda Salame babu wacce zuciyarsa take buƙata domin samun nutsuwa,ganin gidan a rufe ne kuma ya sanya ya zube a wajan tare da.....


😂😂😂To me kukace?????


*FITATTU HUƊU*🔥
      _Takun Farko_

_Assalamu alaikum makaranta littattafan hausa_

_Shin ko kun san shararrun matasan marubutan nan masu tashe tare da kaifin ƙwaƙwalwa da nazari wajan tsaro labarai masu saka nishaɗi da farin ciki da annashuwa sun zo muku da fitattun littattafansu masu sanyi da tsayawa a zuciyoyin ku_?

_To albishirin ku waɗan nan matasa sun zo muku da fitattun littattafansu guda huɗu ciff wanda suka haɗe kansu da alƙalamansu waje guda domin su baku farin ciki a farkon wannan shekara mai zuwa ta 2022 da izinib Allah_

*NIMCY LUV* wadda ta baku farin ciki a cikin *ƘWAILA* da *ABU MALEEK* yanzu haka ta shirya tsaf domin ganin ta baku nishaɗi acikin *TSINTACCIYA*

*AUTAR MANYA* Wadda ta faranta muku acikin *KOBA SO* da kuma *RABON WANI* yanzu ma ta shirya tsab domin ƙayata muku *BAƘAR FATA*

*REAL LADINGO* kinsan ta na santa gwanace wajan sarrafa alƙalaminta wadda ta baku walwala cikin *MIJIN MAMY* da kuma *KAMAL NE* yanzu ma ta shirya tsaf zata baku farin ciki acikin *DATTIJON ARZIƘI*

*MSS FLOWER* Wadda ta baje basirarta acikin *S A R KI* da kuma *LAFAZI* Yanzu ta haɗa kayan aikinta domin ganin ta faranta ranku acikin *SULTAN*

_Zaku iya soma payment tun yanzu domin ganin ka zama lamba ta farko a jerin fitattu huɗu_🥰

*GUDA ƊAYA* 300
*GUDA BIYU*   400
*GUDA UKU*   600
*GUDA HUƊU* 800

6850917335
Na'ima shu'aibu sulaiman fidelity bank
Shaidar biyanka ta nan👇🏼
08142105218
Masu tura kati ta nan👇🏼
08167888934
Ga ƴan nijar mutanan mu zasuyi magana ta nan👇🏼
+22796515805
TEAM FITATTU HUƊU🥰🔥

*Iya masu siyan fitattu huɗune kaɗai zasu biya ta hanyar dake sama amman guda ɗaya kike so kai tsaye zaki nemi*👇🏼

*TSINTACCIYA*
   Nimcy luv
08119237616

*BAƘAR FATA*
  Autar manya
08142105218

*DATTIJON ARZIƘI*
Real ladingo
+22796515805

*SULTAN*
Mss flower
08167888934

*MUNA MARABA DA ƳAN AMANARMU TEAM FITATTU HUƊU*🥰🥰🥰

KWAILA CEWhere stories live. Discover now