Haleematu (42)

56 3 0
                                    

***Na: Reedahmz
***42

Inna Larai tashirya tsaf don zuwa gidan tasallah kunsan abinka da idan shaidan yayi kira ko yabuga gangi sai tafiya Baba Laraba tace itama baza'a a barta a baya ba kunji lalacewa ko sukace da Shamsu gaisuwa da ziyara zasuje yace shima jirgin shida zaibi sukayi sallama dashi bayan ya ajiye kayan abinci bayan suntafi ya siyowa Amira Ummi waya kananu yabasu yace sai bayan sungama waec zaidawo in sha Allah suka mashi fatan alkhairi

Inna Larai sun dira gidan mai magani don cimma mummunan kuduri  bayan isarsu Malamin yace meke tafe daku tasallah tace Larai yi magana Inna Larai tace dama malam dana ne yakeson auren wata yarinya dabamuyi zaman arzi da uwarta ba nikuma banason Auren Amman yaki har yahadani da Yaya na kaji rashin tsoron Allah tama manta diyar yayanta ne yarinyar humm yace yanzu mekike so ayi tace inaso kar ayi auren yace to akwai qa'ida sannan so kike asa yarinya tadaina son shi kokuma shi yadaina sonta kokuwa a haukatata ko kina son a kashe ta kawai kokuma asamu tsanar junan su tace malam banda kisa inaso ace shida kanshi yafasa auren kuma a rufe bakin kawun su da Yaya ta yace bani suna Umar da Shema'u sannan ita Haleematu asamata bakin jinin a idon samari yace angama tadauki kudi da Shamsu yabata tabawa malam suka fito yace tajira tagani kawai..

Yau su Haleematu da Amira suka fara neco don shi aka fi ci a yanzu sai Shamsu ya biya masu shi kawai yayinda a wani bangaren Haleematu tanaji a ranta babu dadi Kuma tana mugun mafarkai akan Yayanta Shamsu shikuwa ta wurin dasauki dai don ma antura shi wani course a ibadan yakan kira haleematu time to time suna hira amma dai hirar tasu tafi karkata ta duniya dakuma exams dinsu hardai suka gama neco lfy tayi hamdala bayan sungama da kusan wata ne Kawu Umar yadawo da magana ta aure amma wa Mu'azzam yace yaya ake ciki inason ganinku wannan satin don mu tattauna zankira su Shema'u duk a gidana Mu'azzam yace zanfadawa Shamsu din yawwa Allah ya maku Albarka.

Juma'a take yau Kawu Umar ya shirya taron ganin su duka a gidan shi Mu'azzam yazo lfy Shamsu yace dasu Yana hanya sai wurin azahar yasauka lfy Haleematu tayi abinci sosai don tarbar su  duk suka tafi harda Umar bayan bude taro da addu'a Kawu Umar yafadamasu dalilin Kiran Mu'azzam yace toh Kawu ai bakomi yazanje inturo asa Rana kawai inyaso karatun saita fara shi gidana yace toh shikenan Shamsu yace Kawu inada magana Aure tsakanina da Ummi inaso a barshi Mu'azzam Rabi'a Amira da Umar sai da sukayi mamaki balle ita Haleematu Kawu Umar yace miye dalili yace abubuwa da dama kowa yayi shiru Haleematu ta mike anan tafadi sumammiya....

Haleematu Where stories live. Discover now