Haleematu (32)

80 5 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 32

Shamsuddeen yana gama fadar haka yayi waje don tafiya gidan Malam Umar wanda shine babban Yayan Malam Iro Baban Haleematu kuma shine Yayan inna larai tunda cousins suke shi kadai inna larai ke tsoro harda Baba Laraba.  Yana zuwa yasameshi gida kuwa suka gaisa Kawu Umar wurinka nazo yace toh toh soja yane tasamu ne yayi dariya yace Kawu ta samu Amman mamana Tana son hanawa Kawu Umar yayi gyaran murya yace ita yarinyar tana sonka yace eh kawu yawwa kabarni dasu duka zan maganinsu ita da Laraba tashi kaje Allah ya maka albarka Ameen yayi tafiyarshi.

Cikin daki mu'azzam yayi tagumi yana tunanin shikenan yarasa abinda zuciyarshi ke so wallahi inba don mahaifiyarshi tayi mugun baki ba ai da an wuce wurin saboda son dayake mata ya share hawayen shi kamar ba soja ba saikuma ya tuna ai dan uwanshi Amininshi ne zai sameta idan yadage toh nan yaji dama dama yadaga hannu sama yace Allah duk zabin dakamin nagode  yashafa tayi sallama ya amsa ba yabo ba fallasa tace Yaya ga abinci yace Nagode tazauna a kasa tace Yaya miyasa ni baka sona yace Rabi'a please jeki banson wata magana yanzu kiyi min list din abinda kikeso zankoma gobe in sha Allah tace angode tafi ta.

Haleematu zaune tabuga tagumi halin tsaka mai wuya datake ciki tadaga hannu sama tace Allah banda zabin daya wuce naka kazabamin mafi alkhairi Inna Larai tafito tace ke zo in aike ki gidan Yaya tace toh tazo ta durkusa tace gani Inna Larai tace ki kaimata wannan kice da ita jibi zanzo in sha Allah toh tace saiki bi gidan sahura mai wara kice ya maganar dana mata nan Haleematu tace Mama don Allah ki aika umar wallahi Dan tala idan naje tareni yake a zaure Inna Larai tace toh munafuka ke zakije tafara hawaye nan Inna Larai tadau mahici ta jefeta dashi tashi kiwuce tafita tana kuka nan taci karo da shamsu yadawo zai tafi yace ya ne tafada mishi yace wuce muje tare inga ta yadda zai tareki nan suka fara zuwa gidan Yaya shema'u nan shamsu ya zayyana mata shirin shi tace hakan yayi kuma bawanda ya isa yahana aurenan tamusu addu'a suka wuce gidan sahura suna tafiya suna hira yace takara hakuri tace Yaya Shamsu ai tarbiyyar kenan bakomi yace zan tsaya anan kishiga idan har yana nan yatareki kisa ihu zanzo tace toh tawuce shikuma yazauna daga nesa kadan yana hango soron gidan tana shiga bataga kowa ba tawuce ciki tayi sallama shiru ashe sahura tafita bakowa cikin gidan sai Dan Tala yafito yafara mata mayen kallo jikinta na rawa tace dama mama ce ta aikoni ga sako ka ajiyewa Baba sahura yace toh dakin ta na bude shiga ki ajiye mata tacee aa yabude ido yace ki ajiye nace tace tohh tana shiga ya datse kofar gida yabiyota tafito dakin da gudu yana binta nan ya cafko tasa kara da karfi Shamsu da gudu yazo yadaki kofar bata bude ba nan Dan Tala ya yage mata riga..........

Haleematu Where stories live. Discover now