Haleematu (48)

55 4 0
                                    

***Na: Reedahmz
***48***

Husna tagama shiri tsaff don komawa gida don sunyi passing out sungama ita da Aminanta tace da Sholy yau zamuje muci musha don murna ta wannan rana..

Sofy tace aidole ne Aminiya Alhamdulillah munsamu mun kamalla dakyar abubuwa Babu sauki sukayi dariya Duka sukace sai dai muyi fatan Allah ya hadamu da mazaje na gari Amin suka amsa..

Hamza yace Besty don Allah karkiyi man mummunan fahimta ko fassara,tace bakomai besty fadamin aini dakai Babu wani abu dazai sa musamu bacin rai yace Alhamdulillah dama wallahi nadade tun haduwa ta dake nike jinki a rai na..

Ma'ana Ina kaunarki kuma bawai karamin kauna ba so na gaskiya nike maki babu hainci..

Sai da gabanta ya Fadi yau shine karo na uku da ake furta Mata kalmar so a rayuwarta tace ya rabbi ka tabbatar da alkhairi... Ehem ehem yayi gyaran murya yace naji kinyi shiru tunanin mekike? Nayi laifi ko ta rufe ido tace aa tana murmushi yace to bani amsa tamike tace zanyi maka text tayi tafiyarta

Ganin hakan Hamza yayi dariya yace akwai alamun nasara in sha Allah nan yakoma ya sanar da Aminan shi abinda suke ciki sukayi murna matuka sannan sukayi fatan Alkhairi

Haleematu tana daki ita kadai don bata son kwashe kwashe kawarta daya white cikin tunanin saiga Sara tazo bayan sun gaisa tace yana ga kamar baki da lafiya? Tace lafiya lau gajia ce sukayi hira aka kira Sara ta fita..

Haleematu tadau wayarta ta turawa Hamza cewa ta Amince amma kar yaci Amanarta ita din marainiya ce.

Hamza yaga sakon ta farin ciki yagama lullubeshi yayi mata reply na godiya da nuna jindadi...

Komi nisan jifa kasa zai fado bikin Mu'azzam da Rabia yazo su Haleematu duk sun samu hutu sun taho gida biki.

Inna larai ta kalli Haleematu tace toh anyi gyaran gida dakinki natausaya maki nasa an gyara amma zaki biyani kudin komi, Haleematu tace haba Inna daga dawowa ta bazaki Bari in huta ba, Baba laraba ta cafe ke wato rashin kunya kika dauko tace Aa kawai Naga ko hutawa banyi ba ne.

Inna larai tace hutu ai sai dai randa kika bar gidanan nan zakiga hutu inma kinsamu mashin shini ne kigama ga aiki can cikin gida kiyi Haleematu tace toh a zuciarta tace da inada hali dana ki zuwa wannan biki hmmmmm...

Shamsu ya iso yasamu su Amira suna ta hira da ayyuka suka gaishe da shi ya tambayi kowa labarin karatu sannan yaje wurin Haleematu tace dashi yanzu kuwa nike Shirin fitowa yace bakomai dafatan komi lfy tace Alhamdulillah Sannu da isowa yajuya zuwa dakinsu..

Haleematu tafito tadauki buta sai taji shi empty can ta hango wani buta da ruwa jikin tagar Inna larai taje tadauka kenan taji kamar maganar Inna larai kasa kasa, caraf sai ji tayi ai Babu wanda zai sota nikam hadin jabanan yayi kinsan ai tunda na rabata da dana naji sakat baka karfa tundaga uwarta, Inna larai tayi ta zuba duk a kunnen Haleematu.

Harda Wanda tayiwa Mu'azzam da mahaifiyar shi wanda Babu wanda yasan da wannan kulli..

Tana mikewa tayi daki tace in sha Allah sai na ga karshen taki kafin kiga nawa...

Haleematu Where stories live. Discover now