Haleematu (25)

88 7 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 25

Shamsuddeen yace Malam lafiya irin wannan kallo haka ya fashe da daria yakawo hannu suka tafa yace kai dai debi girkinan shamsu yace barin ci dan wake don nasan Haleematu ce tayi Mu'azzam yace itace suka debi girkin suna ta santi.

Rabi'a kuwa tasamu Inna Larai da Baba Laraba tace wai Yaya ya mata wulakanci gaban yarinya tayi ta mita Baba Laraba tace rabudashi zansameshi ne kinji mutumiyata nan dai suka lallabata tabar fushi tace bari tashiga makota tafito

Dab laasar Haleematu tagama hatta girkin dare duk tagaji tayi wanka tazauna tana karatun littafin ta shamsuddeen ya kalleta yace mi aka dafa dare tace Yaya Shamsu tuwon shinkafa ce miyar taushe nan taga yayi murmushi har abin yabata mamaki don tasan kullum cikin hada rai yake mu'azzam kuma yafara rabon kayan daya zo dasu Shamsu yawuce yana ta sake sake a ranshi da tunani
Nifa nafara ganin take take mu'azzam Anya bason Haleematu yake baa Ina gaskiya bazaiyuba bazan taba bari ya auri abinda nikeso ba ko kadan wata zuciya tace dashi to kasanar da ita ne? Kana ganin hakan meyiyuwa ne kuwa? Yayi ta sake sake dai  nima nafito nabarshi nace dasauran rina a kaba.

Mu'azzam yasiyo abaya da talkami yace na Haleematu ne itakuwa Rabi'a leshi da jaka yabata amman hankalin ta nakan abayar Haleematu kowa yayi godiya akan abinda aka bashi hatta inna larai yabata atamfa bayan Isha'i suna zaune ana cin abinci shamsuddeen yace Rabi'a da Umar jia anfadamin result dinku yafito don haka zamuje muduba nida Mu'azzam in sha Allah suka ce to .

Bayan kowa yatashi ya rage Baba Laraba da Inna Larai sai Shamsu da shi Yaya Mu'azzam Baba Laraba tace Yayana inason muyi wata magana Amman bansan ta yadda zaka dauke shi ba muna so a hadaku aure da Rabi'a zumbur yamike...

Haleematu Where stories live. Discover now