**Na: Reedahmz**
*Haleematu 64*
Bayan an yayyafa mata ruwa tamike tafara kuka Imam yasata a mota zuwa gida Shamsu da Mu'azzam aka bari sai Umar dayazo daga baya don daukar gawar Inna Larai zuwa gida.. dama Shamsu ya fadawa Baba Laraba a gida nan Haleematu tashigo suka hadu bamai rarrashin wani har su Shamsu suka dawo akayi komi dama Imam yakira Jos yafada masu suma sunzo akayi Komi dasu suka koma Alh Inna yace Imam yabar Haleematu tayi kwana bakwai yace dama tunanin shi kenan gabadaya Shamsu ya zama wani iri yaji kamar an warware mashi wani kulli akan shi.Husna ma taji labari tazo tayi masu gaisuwa ita dasu Sholy da Sofy Mu'azzam yace mungode Sosai Allah yabar zumunci sai munzo gaida family in sha Allah, tace Allah yasa.
Kamar wasa Abdulhalim yafara aiki a company sosai ya canza layin wayar shi yazama baida lokaci saina kamfani abubuwan kuma sai Kara habaka yake wanda yasa wa Mikel tsananin kaunar shi saboda ya iya tafiyarda abin Abdulhalim kuwa baya wasa da aikin shi yayi riko da gaskiya babu hainci ko kadan..
Kwana bakwai bayan rasuwar Inna Larai komi ya tsaya cak Imam yazo don komawa da Matarshi tunda tafiyar su wata sati aka sa tayi bajinta don saida ta ajiye masu kudade sannan Imam ya jingeni masu kayan abinci Shamsu da Mu'azzam sukayii masu rakiya har jikin mota Haleematu tana hawaye sukayi sallama sai jos..
Mikel ne ya nemi Abdulhalim ya rakashi Jos dan yin ta'aziyya wa Matar Aminin shi Imam Abdulhalim yace toh babu komai ranka yadade ai saimu tafi nan suka shirya Abdulhalim yaja motar suka hau tafiya..
Haleematu kwance tadora kanta bisa cinyar Imam suna hira a hankali yace kinga rayuwa ko yadda Allah ke ikon shi tace hakane.
Imam yace yauwa Mikel fa yana zuwa zaizo yamana gaisuwa tace Ayya friend dinka yanada kirki sosai Allah yace ai Mikel akwai Amana tace nikam wai miyasa ake cemashi Mikel? Kasan farko nayi tunanin aljihun baya ne Imam ya fashe da dariya yace Wallahi tun school kinsan sunan ai Mika'ilu ne toh shi yana Jin wayayye ne shi baison sunan shine fa ko tambayar shi akayi sai dai kije Mika'il mukuma muka miyar mashi da mikel tun baiso har ya hakura tace lallai kuwa bikin shi sai mun shirya Imam yace ai shike son Nadiya sosai
Haleematu tace a tuwo na mai na sai mushirya kenan Imam yace sosai kuwa suna cikin hira mikel yakira yace gashi sunshigo gari Amman bari suje masauki Imam yace aa kuzo kufara cin abinci zaifi toh shikenan in sha Allah muna karaso wa.Mai aiki tagama hada abinci bisa dinning ta sanar masu komi yazama ready Haleematu tace toh bari ta watsa ruwa ta shirya shima Imam yatafi sashin shi don shiryawa.
Kawu Umar ya zauna dasu Shamsu Rabi'a da Amira sai Umar yamasu nasiha sosai mai ratsa jiki duk sukayi godiya yace ga Laraba zatacigaba da zama daku sukace sunji dadin haka sukayi mashi godiya yawuce.
Mu'azzam ya shirya don komawa bakin aiki shida Shamsu wanda suka nemi transfer da kudu, wanda dama Mu'azzam bayan course din shi a mashi posting zuwa Nassarawa state shikuwa shamsu shiya nema yadawo Abuja da zama.
Husna ta rame tarasa sukuni takira wayar Shamsu ring uku yayi kafin yadaga, tayi sallama suka gaisa takara mashi ta'aziyya sukayi hira sama sama tace dashi gwarzo inasonka dayawa yace kibari zamuyi magana nagode yace sukayi sallama yashiga tunanin toh me ma Husna tarasa ne yake wulakantata Haka? Indai Kyau ne ba'a magana nan ya ji zuciar shi tayi Sanyi alamun zai iya amsar tayin soyayyar ta tunda shida Ummi har abada sun rabu.
Daidai kofar gidan suka tsaya sunyi hon maigadi ya leko yaga Mikel ne yabude suka shige ciki sukayi parking suna fitowa ya tsaya kallon tsarin gidan har Mikel yatabashi suka shiga cikin falon da sallama...
YOU ARE READING
Haleematu
RandomRayuwar Karamar Yarinya data Rasa iyayenta Biyu A lokaci guda bayan haka rikonta yakoma wurin dangin mahaifinta da yadikonta ....