Na: Reedahmz
Page 28Haleematu ta dukufa ta kwaba danwake tayi maikyau ta daka barkwano suda suke gefe suka wahalalliya tagama tsaf ta tsantsameshi tasa a kwano ta ajiye kafinsu fito taje wanka.
Shamsuddeen yana shiga daki yace kai tashi mana kana ta bacci mu'azzam yayi salati yace kasan akwai gajiya fa hakane cewar Shamsu nan kowa yayi shiru sai daga baya Shamsu yace waini wacece kace kana so ne baka bayyana wasu mama ba mu'azzam yayi murmushi yace zanfadama ka yaushe zaka wuce yace gobe kasan ansake min transfer zuwa Anambra ohhh haba Allah yayi jagora Amman Shamsu kasan yarinyar danikeso bata sani ba haba dai miyasa yace nafiso tagama school tana Sakandire ne shamsu yace mutumina kafada mata oooo kar ayi maka wufff garin kallon ruwa mu'azzam yace aa in sha Allah nayi bincike kanta bata tareda kowa Shamsu yace Allah ya dafa.
Rabi'a tace Mama wai me yaya mu'azzam yace ne baku fadamin komi ba inna larai tace Ashe wai yanada wacce yake so kuma sunyi magana nan ta fashe da kuka Baba Laraba tace aa karkiyi kuka diyata bari yagama tashi shawarar.
Haleematu tayi wanka tasa kayanta dogon riga yayi mata kyau sosai maroon kala tafito tadau dan wake tayi sallama dakin yayunta suka amsa tagaida Yaya mu'azzam tunda sun hadu da shamsu dasafe tace Yayana ga Danwake don wani lokaci haka take kiran shamsu nan dai mu'azzam yace to tashi kije mungode tafita.
Shamsuddeen yafito yace Haleematu gobe zankoma kinada wani Abu ne dakikeso tace aa Yaya komi akwai yace to kidinga kula da karatunki banson wasa banda kula samari kinji tace toh tana murmushi yace kanwata akwai sako dazan ajiye miki saina tafi kibude tace angama Yaya.
Mu'azzam yagama tunani yace zai fadamasu bayan kowa yahadu banda Shamsu dayaje siyayyar tafiya yace mama nifa dama wacce nikeso bakowa bace face sai yayi shiru yana shafa kai yace Haleematu zumbur! Inna Larai tamike
YOU ARE READING
Haleematu
RandomRayuwar Karamar Yarinya data Rasa iyayenta Biyu A lokaci guda bayan haka rikonta yakoma wurin dangin mahaifinta da yadikonta ....