**Na: Reedahmz
**53**Hamza can yadawo baima san Capacity yana ciki ba yayi sallama yana ya ganin capacity yace sannunku yasamu gefe ya zauna yana dan latsa wayarshi Yana jinsu.
Sunusi yace Ilyas dagaske nike fa Beb din tayi mugun haduwa kuma nafada kumin hanya kawai Hashim yace kai kadamemu mufa yarinya daya muke magana da ita Yar course dinmu yace yawwa toh ita Hamza dake kwance yamike Ilyas yamishi ido,
Alamun ya matse tukun, Sunusi yace zan iya komi Dan samun soyayyar ta Hashim yace Allah ya sa baka makaro ba... Yace ai late comer ake yayi yanzu kagane
Yana fita hamza yace Hashim kaga nifa ba shiri muke da guy dinan ba inba don ku ba bazan dinga kula shi bafa, kuma alamu suna nuna kamar akan Haleematu yake magana fah Ilyas yace ai itace ma, "Hamza yace chab" lallai kuwa za'a yi karamin yaki. Hashim yace aa bari dai muga ni tukun.
Haleematu tana zaune sakon Hamza yashigo game da batun Sunusi capacity tayi mashi reply itafa bata gane wanda yake magana akai ba yace ok gobe zai nuna Mata shi wurin lectures.
Inna Larai gabadaya jiki yayi tsami don ta samu karaya hudu da tsagewar Kashi. Karaya a cinya biyu kafar dama sai hannun hagu karaya biyu kafar hagu tsagewar kashi tasamu sai dinki da aka mata a goshinta sai su buguwa...
Baba laraba takira Mu'azzam yafadawa Rabi suzo da Umar sannan takira Shamsu take shaida mashi nan dai yakira Amira sannan yakira Haleematu tace toh Yaya a mata sannu kafin inzo in sha Allah nan da kwana biyu, yace what! Bakida hankali ne? Tace afuwan Yaya inada text ne masu zafi har uku shiyasa nace hakan.
Yace Allah ya kaimu yabada sa'a yakamo hanyar Bauchi cikin gaggawa ya iso ya tarar da Mu'azzam Dasu Rabia.
Hajia Sumayya zaune bisa sallaya Sorayah tashigo ta zauna tace Umma wai Yaya Miyasa bazai cire mata a cikin dangi ba? Hajia Sumayya tace Saboda ra'ayin shi kenan. Tace yi hakuri umma na toh bakomai Allah ya kaimu Sorayah! Sorayah! Sorayah! Tun kafin tashigo Sorayah tace Umma sister Nadiya zatasani gaba yanzu nikuma banson zuwa ko ina yanzu wallahi, Nadiya tashigo yawwa please tashi muje kirakani Sorayah tace ina? Kekam brother Imam ne yakeso a zaba mashi perfumes masu dadi wa Girlfriend dinshi, Sorayah tace wowwwww Abu zaibada citta Allah sa dai wise ce suka tafa, Umma tace koma micece...
Zayd ya shigo shida fauza sukace aisuma zasu je umma tace toh Nadiya gafa abokan tafiya kinsamu don haka kowama ya shirya a tafi Khalid kira Marwan da Saif duk suka tafi gabadaya suka bar gidan wa umma da Masu aiki..
Haleematu sungama test dinsu ta kamo hanyar zuwa gida duba Inna Larai
Ilyas yace nifa ko Ina Mamakin Hamza da wannan shagon askin gaskiya abin zucia ne, Hashim yace Allah kuwa mugamu muna biyewa kudin iyayen mu munkasa sana'a yaushe Hamza yazo amma har yasamu naasibi.. Kuma Munso hanashi yaki Ilyas yace Allah ya kyauta Amin gashi har yana shirin Aure fa hakane..
Haleematu tace Inna Yajikin naki tace dasauki sai yau kika ga daman zuwa duba ni tace Aa kiyi hakuri wallahi test muke tace ehhhh ai yafini muhimmanci ko? Baba laraba tace ai tunda ba uwarta bace yazata yi hanzari, Haleematu tace Aa Baba idan bazaki gyara ba Karki ce haka, Baba laraba tadaga hannu zata bige mata Haleematu ta kauce Inna Larai tace iyye Lallai kin riqa cikin haka saiga sallamar Kawu Umar yashigo yaduba jikin yace Allah yakara tsarewa Amin suka ce dukka..
Kawu Umar yace ke dama kuwa inaso inkiraki a waya don yayanki yasameni da magana wani dayake sonki a makaranta koh? Tace hakane kawu Umar yace toh dama tun wancan zuwan nasa shi Shamsu yayi bincike game da yaron toh Alhamdulillah an yabi yaron kuma yanada abinyi caraf Inna Larai tace minene sana'ar tashi? Kawu Umar yace ai yanada shagon aski a can Zaria din kuma iyayen shi suna Jos dan mangu ne Baba laraba tace ikon Allah toh yayi kyau Inna Larai ta tabe baki..
Kawu Umar yace idan kunyi hutu zamuyi magana amma yakamata yaturo manyan shi Haleematu tace in sha Allah kawu nagode ta mike ta rakashi zuwa zaure...
YOU ARE READING
Haleematu
RandomRayuwar Karamar Yarinya data Rasa iyayenta Biyu A lokaci guda bayan haka rikonta yakoma wurin dangin mahaifinta da yadikonta ....