Haleematu (20)

97 6 0
                                    

** Na: Reedahmz
** page 20

Sannu Sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba'a zo ba an wayi gari su Rabi'a da Umar angama ssce anyi jamb lafiya sunbar Haleematu cikin makaranta Inna Larai babu wanda yakaita farin ciki yayanta biyu sungama Sakandire sai jami'a.

Shamsuddeen dama yahanasu sauraran samari yace sai suntafi makarantar gaba da sakandire shikuwa Umar anturashi wurin koyon dinki kafin fitowar jarabawa Rabi'a da Haleematu akace kowa ya zabi Sana'a inji Yayansu sai Haleematu tace ita tana shaawar koyon yin su snacks don dama Shamsu yazo ne daga Ibadan don ya tabbatar yasamar masu abinyi kafin yakoma shine yanemo form guda biyu daya na koyon kwalliya daya na girke girke da snacks toh duk suna gaban Baba Laraba da Inna Larai caraf Rabi'a tace wato saboda kinji nace inaso ko Haleematu tace Adda Rabi'a nibanji ba kawai nafadi abinda nikeso ne Sai Baba Laraba tace rufe mana baki ja'ira ba ita ce gaba dake ba kibari tazabi abinda take so mana Inna Larai tace ina kuwa zata yi shiru tunda yanzu taga kansu daya da Rabin Haleematu tace ayi hakuri nayi laifi Shamsuddeen yace karbi kicika Rabi'a kifara zuwa wurin koyon girke girke da snacks din kekuma kije koyon kwalliyar bakomi takarba tace Nagode Yaya ta mike takoma dakin dayake shine aka bata matsayin gadon mahaifinta ta kwanta tayi kukan daya zamo mata jiki kowani dare tayi addu'a wa iyayenta tace watarana sai labari komi sai anmaka fin karfi na tabbata da Mahaifiyata na raye koba komi zanji dama dama Amman haka Allah ya so dani yake kuma son ganina a cikin tunanin har bacci yadauketa.

Da Asuba ta tashi tafara sharar tsakar gida bayan tahada murhu tadora ruwan zafi ta debo kamun yin koko tahada ta ajiye takama wanke wanke tana sauri gudun kartayi latti shamsuddeen yana kallonta yafito yace jeki shirya kitafi Rabi'a zata karasa tace um um Yaya inna zatamin duka yace ni nace kitafi tace tohm ta shiryawanta ta tafi batareda sallama ba.

Haleematu Where stories live. Discover now