Haleematu (24)

80 5 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 24

Tana fitowa tayi kicibis da Rabi'a tace Ashe yaya mu'azzam yazo a yatsine tace um nan ta wuce tabarta batareda tafadamata sakon mu'azzam din na ta mashi girkin data tabayi wani lokacin da yazo hutu

Ita kuwa baiwar Allah nan tashiga ta debo shinkafa ta barza tayi mashi dambu ta kwaba filawa tayi dan wanke ta kwashe lokacin yatashi yayi alwala yatafi masallaci ta debi girkin takai rumfa idan taga an adana wanda Rabi'a da Baba Laraba sukayi ta ajiye.

Tawuce taje tayi sallah tanaji yadawo itama tafito tasamesu da Rabi'a a zaune bisa tabarma ta kaba tazauna akan dutse dake gefe bata hau tabarmar ba tace Yaya Mu'azzam Barka da Sauka Ina wuni ya amsa Alhamdulillah kanwata nashigo kintafi makaranta ai tace nadawo kana bacci yace gajia ce kanwata tsantsa tace Allah yabada sa'a yace Ameen

Rabi'a takatsesu da cewa Yaya kaci abinci mana yunwa fa yayi daria yace Rabi hoo zanci ai Haleematu tayi murmushi tace barin dan kintsa cikin gidan Yaya kaci abinci yace Allah sa kinyi min abinda nike so tace nayi kabude zakagani yace toh jeki yi anjima zamuyi hirar tace to Rabi'a ta galla mata harara tawuce sum sum a zuciyarta tace kyaji dashi.

Kafin yabude abincin Haleematu tayi wuf tabude Macroni datayi da kifi tazuba mishi yaci kadan yace mikomin wadancan tace Yaya kodai baiyi dadi bane yace yayi ba laifi inadai so inci na gargajiya tahade rai dai yabude dambun shinkafa da Haleematu tayi yaji komi sai qamshi yake yafara ci yana zuba santi Kawai Rabi'a ta mike wato ita aikin banza tayi kenan wucewa tayi daki tana huci yana kiranta taki dawowa yakira Haleematu yace girki yayi kafin nakoma in sha Allah girkinki zandinga ci tace nagode Yaya na sallamar Shamsu takatse masu maganar su tayimishi barka da shigowa yasamu wuri gefen mu'azzam yazauna yace Dan uwa ya hanya Alhamdulillah kace zantafi kai kazo yace Wallahi Haleematu ta tashi barsu mu'azzam yabita da kallo har shamsu yataboshi.

Haleematu Where stories live. Discover now