Haleematu (16)

89 5 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 16
Kwanci tashi ba wuya wurin Allah kwanaki da Malam iro ya dibawa Amina da yaranta sunkare ya shirya tsaf don zuwa dauko su yayiwa yace akai mata aka kaimata suka gaisa yace toh gobe in sha Allah yana hanya sai sudawo lahadi tace Allah ya kaimu yace Ameen sukayi sallama.

Bayan yadawo daga kasuwa yayi sallolin shi kafin yashigo yasameta yace tasameshi a turakar shi takira Shamsu tunda zaikoma makarantar ran lahadi.

Sun shigo sun zauna yace malam shamsu adage da karatu a kula da kanne kaga yanzu kaine babba kaine zaka zama gatansu a gaba Inna Larai tanaji ta sunkuyar da kanta yace zanbaka dubu biyar kayi siyayya koh yace Nagode Baba yadauko yabashi yace dashi gobe in sha Allah zantafi katsina dauko su yadikon ku yace Allah ya kaimu Baba yace Shamsu ka kula da kannenka Amana yace toh yatashi yayiwa Malam iro sallama yafita.

Malam iro yadawo da hankali kan Larai yace toh kikula da gida banson bashi idan nayi tafiya tace toh mungode Allah ya kiyaye hanya yace Nagode yadauki dubu goma yabata yace ki ajiye wurinki banson kina tambaya ta kudi kullum tace angode yace Allah yayi albarka tace Ameen.

Haleematu Where stories live. Discover now