***Na: Reedahmz***
***59***Hashim, Ilyas, Sunusi capacity da Sagir sun iso garin Jos sun doshi masauki da akayi Masu don suci abinci su huta kafin zuwa dinner Hamza yayi waya dasu yace suyi hakuri aiki yadan mashi yawa ne kuma yanakai abokan maigida masauki Hashim yace toh bakomai Ilyas yace ikon Allah toh bari dai mujira Sunusi yace saurin me kakeyi tunda kazo? Kuma gaskiya ne fa inji Ilyas sukayi dariya Sagir yace wannan kaji haka ai sai in manta kaina anan lokacin daya bude kulolin abinci da aka kawo masu da isowarsu duk suka baje suna diban girki kawai.
Mikel tareda Hamza yace Man yadda ka mugun boye kanka yau zamu sha kallo idon jama'a, Hamza yace kabari kasan wa nagani dazu a cikin gida Mikel yace aa Husna Mana Ashe wai itace yarinyar Abokin Abban mu daya taba cewa inje akayita sabani nazo muka hadu by accident a matsayin mai aski Mikel yace shege gaskiya ka iya taku Hamza yace kasan bata taba ganina ba a gida kuma inadan bata kammani sannan ni nasanta lokacin da Abba yafara suggest ai cemashi nayi yabari tukun karya fadawa Babanta saina gwada ingancinta suka fashe da dariya lokaci daya yace goga..
Inna Larai tasha mamakin ganin Aljannah ta duniya a gidan diyar data tsana a rayuwarta, tace tasallah hummmmm lallai tsugune bata kare ba, tasallah tace Ina kuwa don idan munkoma dole a sake sabon aiki Baba Laraba suna dayan dakin ita da Mama shema'u. Rabia tace hmmm Inna wai nan gidan surukan Ummi saita kama baki tace shikenan Allah ya kyauta amma Inna saikin tashi tsaye Amira da gefe taje jinsu tun shigowar ta tace haba ku kuwa yanzu bazaku barta duk wannan isharar? Inna Larai tace rufemin baki Zainab kanwar Mu'azzam tace Amira tashi mukoma can wurin Amarya kawai.
Haleematu duk damuwa da mamaki sun cika ta, nan Nadiya tashigo tace me makeup tazo aka kaita wani daki inda za'a yi mata kwalliyya Nadiya ce kawai da kannen ta su Sorayah tun kafin a fara makeup suke yaba kyaun Haleematu, Sorayah tace sister Ashe dai bros ya zallar Madara Nadiya tayi murmushi suka tafa tace aini nasan Bros bazaiyi zaben tumun dare ba Fauza tace ai kunsan Yaya bada ganan ba duk suka sa daria wayar Nadia ke Kara tadaga Bro ankusa agama kayi hakuri don Allah ba yanzu zaka kaganta ba ok toh shikenan ltr ta ajiye wayar.
Husna suna sashen Soraya Hajiarta kuwa ta iso tana sashen manya ganin hoton Imam yasa ta matsa kusa tace kai guy dinan yayi kyau kodai shine bros sai Sholy da Sofy suka matso duba hoton caraf sai Sholy tace kinsan Allah Suna kama da Mai Babing saloon dayace yana sonki? Sofy tace ji wani iskanci miye wani kama anan wannan kina ganin Smart dashi handsome wancan da Rana ta bigeshi Husna tuntsirewa tayi da dariya tace Rabuda Sholy batasan kama ba banza kawai. Dubi kimgashi fa kya hadashi da mai barbing lallai Sholy nan suka shirya don tafiya dinner din..
An kawata wurin dinner tsaf irin na masu hannu da maiko komi yaji a wurin, anfara zuwa an zuba matakan tsaro na mussaman a kofar shiga da kewaye ankawo su Inna Larai duk suka rude aka nuna masu teburin sun na dangin Amarya suka zauna duk jiki yayi sanyi dole..
Wuri yayi kyau yacika Ilyas da Hashim Sunusi da Sagir duk suna kofar wurin Hamza yace su Shiga ciki akwai table din abokai su zauna don yana tare da maigida Alh Inna mota Nadiya ta rako Haleematu, sukuma suka shiga mota suka wuce. Hamza duk ya rude saboda kyau dayaga Amarya tayi yace uhm Amarsu murmushi kawai tayi mikel /Ribadu Sune a mazaunin driver dame zaman banza sai motar baya Faisal da Harith Sune manya wadanan 4 din nan suka isa harabar wurin event MC yanata bayani yace to a yanzu zaku saurari jawabi daga shi uban taro Alh Muhammad Inna (CEO Inna foundation) Alh Inna ya tashi yayi dogon jawabi sannan yace yau zai gabatar da Ango kuma Babban danshi me IMAM TEXTILE ,IMAM YOUGHURT da Amaryar shi wato Hamza Imam Inna, Security suka fara shigowa sai Nadiya da Amarya da ango sai Kallon yakoma kansu Hamza yarike Amarya gam.
Husna ce tamike zumburr! Sofy tace Lafiya shiru kawai tayi baki a bude Hashim ne ya damko Ilyas Sagir ya dubi Sunusi suna zare ido don mamaki wai dagaske Hamza ne kokuma dai yane duk suka rude a wurin zuciar su ta cika fal da mamaki shikuwa Hamza sai murmushi yakeyi suka zauna aka sake bude taro da addu'a sannan MC yafito yace za'a ji tarihin ango daga bakin best friend dinshi Mikel Nan mce ya bawa mikel mic don bayani...
Mikel yace da farko dai Hamza wanda akafi kira da Imam haifaffen garin Jos ne yayi karatun primary da secondary duk a cikin garin Jos kafin yatafi Oxford University inda ya karanci International relations degree na biyu kuwa Business administration yayi sannan yayi Msc dinshi a fannin political science yanzu haka ya gama PHD dinshi kuma shine Mai Imam textile da youghurt mutumin kirki ne Amarya dafatan zaki rike Mana Abokin mu hannu biyu wannan shine kadan daga cikin tarihin ango amini na ooops namanta ban fadamaku ba Yana 200lv a Abu Zaria Kuma yanada shagon aski,duk wurin yadauki tafi da dariya... Sunusi yace what lallai na kwafsa yayin da Sholy tace kunce bashi bane Kuna musu.. Mikel yakoma ya zauna yace goga yau buri yacika murmushi Hamza yayi yace injiwaye kaifa ko Haleematu tace uhmm Hamza kenan yace minene tace kaine kuwa yace nine. aka ci aka sha wurin dinner akayi Komi lfy aka gama nan aka fara watsewa Husna Sholy da Sofy sukazo inda su Hamza suke Imam yace Ranki yadade kallo ta watsa mashi irin na ashe mayaudari ne kai Mikel yace shiga mutafi Amarya tagaji, Hamza yace muyi magana a gida Husna nan yashiga mota suka wuce suka barsu anan Husna tace tabbas saina mallaki guy dinan kota wani hali bazan hakura ba!
YOU ARE READING
Haleematu
RandomRayuwar Karamar Yarinya data Rasa iyayenta Biyu A lokaci guda bayan haka rikonta yakoma wurin dangin mahaifinta da yadikonta ....