chapter fifteen

45 1 0
                                    

A yau an wayi gari kwanan Ameetah goma a garin Kaduna. Tun tana dari dari har ta fara sakewa inda ta fuskanci nan gida ne da kowa ke da 'yancin kan shi aka kuma san darajar dan adam ba irin gidan mahaifin ta da ta baro ba. Nutsuwar ta da yadda take bawa kowa girman shi ne ya siyo mata soyuwa a wajen jama'an gidan sannan rashin kyuyan ta da iya girki ya sa Mamee ta soma sakin mata ragaman wasu abubuwa a gidan, haka daddy yake jin dadin nau'i nau'in ciman da take jera mishi na masu ciwon diabetes wanda ta saba girkawa matan baban ta mai diabetes da ya auro daga Chad wanda ko da Mamee ta tambaye ta inda to koyo su ta shirga mata karyan ubangidan ta da ta baro gidan shi a Maiduguri irin cimar shi ce a dalilin yana fama da ciwon.

A safiyan yau litinin ta tashi cikin rashin kuzari a sabili da kewan Ajus da Raniya da ya addabe ta wanda suka wuce makaranta ran asabar. Tun da ta tashi da asuba bata koma bacci ba dan dama jikin ta ya riga ya horu da hakan. Tasalla ta taya shirya breakfast din su Muhammad suka sallame su dan zuwa makaranta, sannan ta koma taya Halima mai kula da tsaftan gidan gyaran gida, sai da suka kalkale gidan tas Haliman na hana ta saboda su duk a zaton su 'yar uwar su Mamee ce ita din suka taho da ita daga Maidugurin, dan Mamee bata ce da kowa komai ba in ban da Tasalla da ta kira a asirce ta ce ta dinga saka mata ido akan tarbiyan ta da wasu abubuwa idan ta fita aiki, ita din ma kuma ba dogon bayani ta yi mata ba. Ita dai Ameetah an ajiye ta ne a dakin da ke tsakanin sashen Mamee da dakin Raniya Wanda ta tabbatar shi din ma an yi ne dan ajiye ta kusa a ga irin Kamun ludayin ta to ita ko Karen hauka ne ya cije ta tayi displaying wani mugun Hali ne bayan ta ga gurin zama, balle ma bata da shi? Sannan tun da suka zo su Raniya ke ta kokarin Jan ta a jiki sai ita ce ma dai da bata da sakawa da mutane tun ainahin ta take baya baya. Duk inda zasu je sai sun ja ta ta raka su a yar karamar jar motan Raniya da ke matukar bata sha'awa. Hatta saloon da suka je Ana gobe zasu koma da ita suka je  itama aka gyara mata dogon gashin kan ta yayi kal kal da shi gwanin sha'awa , sannan da suka tashi suka biya wani shago karasa siyayyar su suka tarkato mata kayan shafa da na gyara gashi itama. Ai ko ba karamin dadi Mamee ta ji bada suka dawo, barin ma da ta nuna mata kayan sakawan da suka bata kafin su tafi. Shi yasa yau duk ta tashi sukuku da ita cikin kewan su duk da ba yawan saka musu baki take yi ba tana jin dadin yadda suke sakawa da ita a cikin hargowan nasu. Sai da suka turare gidan tas da turarukan wuta masu dadin kamshi (check out @sapphire_treats_n_perfumery on instagram in kina bukatan turarenwuta'yar Maiduguri da sauran kayan kamshi na jiki da na gida) bayan gyara ko ina na gidan ta wuce kitchen daura abincin daddy Wanda aikin Tasalla ne take Neman kwacewa tun da ta zo sai kuma ta tuna yau litinin ne jama'an gidan azumi suke yi, don haka sai ta hada shayi kasancewar ba ta fiya cin abinci da safe haka ba, Tasalla na ce mata ga abun Karin ta ta amsa da tea din ma ya wadatar ta fita ta bar ta tana mitan yarinya sam bata son cin abunci. Library din gidan da ta ji Raniya na Kira da study ta nufa, Wanda cike yake da takardu babu nau'in da babu, Kama daga novels, memoirs, biographies , autobiographies, har zuwa islamic books. Tun ainahin Ameetah ta tashi da sha'awan karance karance ko dan bata da Abokin hira ne mafi akasarin lokaci, sai dai rashin samun lokacin kan ta ya sa ala dole ta hakura da karance karancen. Da kyar ta zabo wani takardan Chimamamda Ngozi Adichie mai suna purple hibiscus Wanda synopsis din ya ja hankalin ta har ta ji shi zata soma karantawa. Da shi ta nufi dakin ta ta dulmiya cikin karatun shi, wunin ranan sallah kadai ke daga Ameetah daga karatun nan dan ko abincin rana Tasalla har daki ta biyo ta da shi tsaban yadda ta hakikance akan karatun. Sai ta rinka jin tam kar ita ce Kambili, don duk wani abun jin dadin rayuwa Allah ya hore musu sai dai duk da haka babu jin dadin Saboda tsaban son Kai irin na uban su Wanda shi a hakan in a ka bar shi gata yake musu. Bambancin kawai ita nata takuran ba a wajen uba kawai ya tsaya ba har da matan uba, sannan ko ba komai ita Kambili na da dan Uwan da ya fahimce ta tare da uwar da ke kokarin kare martabar ta a tare da ita, duk da su din ma shakkar uban suke yi. Kiran sallar la'asar ne ya dakatar da ita daga karatun ta tashi ta shiga Bandakin da ke manne da dakin nata  dan dauro alwala, bayan ta idar ta shafa addu'o'en ta ne ta nufi kitchen dan taya Tasalla hada kayan buda baki. Tana shiga kitchen din ta hango ta tana fitowa daga store da bokitin nikakkiyar gyada a hannun ta ta ce "Mama Tasalla su meye kike shirya wa ne haka gida ya kauraye da kamshi" Tasalla cikin murmushi ta ansa "Ho Ameetah! Wani kamshi kika ji in banda tsokana? Farfesun Kayan ciki ne da Mamee ta bar sallahun a daura sai kuma gyada da nake niyyan damawa dan yin kunu, ay kamshi sai girkin ku manya" tayi murmushin itama ta ansa ''ni na isa uwar tuwo, ba dan kar in yi karambani ba da na ce yau a bar gyadan nan mu canja zuwa kunun mardom zai fi yi wa daddy amfani a jiki, amma ban San ko 'yan gidan basa son shi ba" Tasalla ta ca "tabbas suna shan shi, ko ba wannan da ake yi da nono ba, ay kafin Aunty Sameera tayi aure tana yawan yin shi, sai dai fah bamu da kindirmo cikin freezer" ta ce ko yogurt babu mama Tasalla? "Ai ko babu, sai dai in Hamisu Za'a bawa ya siyo tunda yanzu zai Kai nikan waken da Za'a yi kosai, sai ya biya tunda Akwai kudi a hannu na irin Wanda Mamee ke bayarwa ko Za'a bukaci wani abun ta fannin kitchen bata gida" Ameetah ta ce "Toh amma dai kar ya siyo flavored one ya siyo plain" Tasalla ta harare ta ta ansa "ni kuma ina na San wani flain da plebo balle Hamisu, sai dai ki yafa mayafin ki ku je tare'' Ameetah ta kyalkyale da dariya ta ce "Toh dan baki sani ba sai ya zama shima bai sani ba? Haba Mama Tasalla yaya da mummunan shaida haka?" Ta ce "bana son surutu ke dai je ki dauko mayafi ku je kawai, wani bagidajen Hamisu ne ya San miki abun da kika lissafa? Shi da aike daya sai yayi kafa biyu zuwa uku dan tsaban gidadanci? Sai an yi magana ya ce shi yayi boko, koh Halima da bata wuce ta filin makaranta ba ta fi shi tabuka abun kirki in gaya miki" har ta je ta dauko mayafin ta fito Tasalla na surutan ta, ta amshi kudin ta kuma suri bokitin nikan ta yi waje tana dariya.

A gazebo din da ke gefe daya na haraban gidan ta hango daddy a zaune da Quran a gaban shi ya tusa yan kananan'ya'yan shi da zaka zata ma jikokin shi ne in ba ka sani ba yana Kara musu karatu. Tun da tsohon sojan yayi ritaya ya daurawa kan shi alhakin karatun'ya'yan nashi a duk yammaci ban da alhamis d juma'a. Dan haka Ameetah ta karasa ta durkusa har kasa ta kwashi gaisuwa bayan ta tabbatar ya Kai aya. Cikin fara'a da sakin fuska ya Amsa mata har yana tambayan ta yaya kewan su Raniya, Saboda kullum tare suke zuwa gaishe shi dan haka tun da suka tafi bata hada idanu da shi ba. Ya ansa da Alhamdulillah sannan ya tambaye ta ina zuwa, cikin kaskantar da Kai ta bashi ansa da cefane da nika domin girmamawa ce ba dan kadan ba tsakanin ta da tsohon, sabili da a dan zaman da tayi ta fahimci mutum ne da ke tsaye haikan a kan al'amarin gidan shi da na iyalin shi, inda shi ne babban turban da nata mahaifin ya Gaza daura kan shi a Kai Wanda har ya janyo wani gibi babba a al'amarin gidan su. Murmushin kamalan nan nashi ya jefe ta da shi, cikin son ta sake da su har su fahimci menene gaskiyan lamarin ta kasancewan ya San kan shi as a very good judge of character da a kankanin lokaci yake gano Sharri ko alherin mutum a mafi yawan lokuta. Ya ce ''a dawo lafiya, amma jiya Mameen ku ta Kai mun wani drink da na ji dadin shi matuka, kuma ta tabbatar mun yan N'Djamena da ke cikin gidan nan ne suka hada, it tastes all natural, I hope yau ma Za'a samu ragowa, Koko dai in Karo kudin cefane a Karo Kayan hadi?'' Murmushi ta yi sannan a kunyace ta ce ''in sha Allah Za'a samu daddy, Akwai komai a gida'' ta mishi sallama ta karasa suka fita da Hamisu.

Haka Mamee ta dawo ta same su dab magariba a kitchen sun ma kamalla komai tayi ta shi musu albarka dan ta saba ne in ta dawo a gurguje ta dan saka hannu dan hada ciman daddy din sai ta tadda Ameetah ta hada komai da yakamata ya ci tun daga kan fibre da lean protein zuwa veggies da fruits, domin Banda mardom din potato and beet salad ta hada a saukake da manyan black beans din da ta tsinto a Dalema da Hamisu ya Kai ta, sannan ta hada da irin smoothie din jiya na watermelon da mint da celery suka ji suka kuma taimaka wajen rage gafin watermelon din. Mummy Kaman ta rungume ta ta ji, a ran ta tana mai addu'an Allah ya sa dagasken haka take ba shigo shigo ba Zurfi take yi musu ba, bata kuma yi kasa a gwiwan nuna mata jin dadin nata ba. Toh ita kuma Ameetah haka take, nufin kowa take yi da alheri a ko da yaushe, balle kuma wannan family din da su ma nufin ta da alheri suke yi, ji take yi zata iya yin komai just to see smiles on their faces, duk kuma wani hanya da zata faranta musu zata bi don ganin tayi hakan Saboda duk abun da zata musu gani take yi bata biya su ba. Sai dai ta cigaba da bin su da addu'a Allah ya rufa musu asiri a duk inda su ke a kuma ko da yaushe Kaman yadda suka rufa mata itama.

Ire iren wadannan halayen nata Ne ya sa ta shiga ran kowa da ke gidan, babba da yaro, mace da namiji. Kai ba ma ga mutanen gidan ba, kyawawan halayen Ameetah ya sa an ji labarin ta gari daban daban. Dan wani zuwa da Gwoggo Asi ta yi ganin likita a nan Kaduna haka ta rinka hidima da ita babu kama hannun yaro, har ta koma katsina bakin ta cike da yabon kyawawan halayen ta. Haka mutanen Texas Aunty Nana kullum Abba da Muhammad a cikin gaya mata Ameetah ta taya mu assignment ko ta dafa mana kaza suke. Hatta Ammabuwa da ke kasar Switzerland ta samu labarin Ameetah a bakin mahaifiyar ta, balle kuma yan nan kusa Abuja.

Where are my fellow insomniacs? This page is for you, ku karanta tun da zafi zafin shi kafin ya huce. To all the sleepy heads that will read in the morning, Barka da Juma'ah I guess... don't forget to read suratul Kahf and send plenty salawaats upon our noble prophet...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 26, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AMEETAHWhere stories live. Discover now