chapter thirteen

109 12 7
                                    

       Sai da Ameetah ta kara kwana hudu a asibiti tukunna Dr Folorunsho ya bata sallama. Bata ma san an sallame ta ba dan ko da ya zo duba ta during morning rounds bai yi zancen sallama ba sai wajen karfe sha biyun rana da ya shigo tare da wata farar yarinya da ba zata wuce tsarar ta ba yana mai shaida mata an sallame ta gashi har hajiya ta turo wacce zata dauke ta, cikin fara'a suka gaisa da yarinyan ta tambaye ta jiki da kuma zancen tattara mata kaya ta ce kayan ta a hade suke. Nan da nan ta dauko yar bagcon ta sannan ta yi sallama da nurses din da ke duty tana mai basu sakon gaisuwa zuwa ga su sister Nse da sauran su da basa duty sannan suka fita direba ya ja su zuwa wani gida a cikin old G.R.A.
       Babban gida ne da sashi kala kala, ita dai bin yarinyan take suna wuce parlour parlour har suka tadda wani dan matsakaici mai shegen kyau babu abun da ke tashi a ciki sai ni'imtaccen sanyin AC da kuma daddadan kamshin turaren wuta. Mamee ce a kishingide daga gefe kaman yadda ta gaya mata ta rinka kiran ta da taje dubo ta a asibiti yayin da wata mace mai yalwan fara'a ke zaune dirshan a gefe daya wacce daga gani matar gidan ce ko dan tangamemen hoton ta da ke maka sallama daga ka sawo kai cikin parlourn. Daga gani hira suke tabawa wanda sallamar su ce ta katse hiran, har kasa Ameetah ta durkusa ta  gaishe su suka amsa sannan suka mata barka da samun lafiya tare da Allah ya kiyaye gaba. Hajiya Toma ce ta kalle su ta ce "toh Raniya, sai ki kai ta daki tayi wanka ta ci abinci ta huta, gashi azuhur ma ya gabato" Raniyan ta amsa "toh yayya". Tafiya kadan suka kara sannan suka cimma wani daki da Raniyan ta dosa kai tsaye tare da sallama inda ita ma Ameetah tayi yadda tayi amma sallaman nasu bai samu amsawa ba sabili da yarinyan da ke kwance bisa gadon makale take da earpiece din wayan ta tana sauraron abun da ita kadai ta san ko meye, idanun ta kuma a rufe suke ruf in full concentration to abun da take sauraron. Raniya ce ta isa gadon ta daka mata duka inda tayi zumbur ta mike tare da zare earpiece din daga kunnen ta tana jin surutun da Raniyan ke yi. "baccin kenan? Kin yi kwance kwance kina aikin da kika saba, oya tashi lokacin sallah ya yi, kuma da kika ki raka ni dai gashi na je na dawo still whole babu wanda ya gutsura ni a asibitin". Ta galla mata harara kafin ta amsa "duk bakin cikin na ki raka ki din ne zaki zo ki firgita ni haka? Kin ji yanda zuciya na ya tsinke kuwa, Allah kin dau alhaki na kuma keep it in mind zan rama ne" ta karasa fada tana mai saukowa daga kan gadon. Sai da ta karasa saukowa suka yi ido hudu da Ameetah da ke tsaye a bakin kofa tana kallon su tun da suka shigo, a take ta kissima itama wannan din tsararta ce sannan da gani 'yan uwan juna ne da ita da Raniyan in aka yi la'akari da kammanin su sai dai ita bata kai Raniyan haske ba bata kuma kai ta tsayi ba. Juyawa ta yi ta kalli Raniyan  ta ce "to uwar iyayi, ke ma da kika je har asibitin kika dauko ta na ga a bakin kofa kika bar ta a tsaye, to ni bari in karasa ladan" ta saka hannu ta karbe bagcon da ke hannun Ameetah sannan ta riko ta har bakin gadon ta zaunar da ita a gefen Raniya cikin murmushi ta ce "I'm Ajus, yaya jikin" kafin ta amsa ta ta kuma cewa "rabu da Raniya duk haushin na ce bacci zan yi bazan bi ta asibiti dauko ki bane ya sa ta bar ki a bakin kofa" by then ta isa gaban dan matsakaicin fridge din da ke cikin dakin ta bude ta dauko roban ruwan mowa da gwangwanin fanta tana cewa "it's the only remaining fanta a fridge din because na san ba kowa ke shan coke iri na ba" kaman wacce aka tambaya ta zo ta dire a kasan carpet din kusa da kafan Ameetah tana cewa "sha ruwa kafin na yi alwala kema sai ki shiga ki yi, kodayake it will have been better ma ke kam in zaki hada da wanka dan ki ji dadin jikin ki" ta doshi kofan bandakin da ke manne a cikin dakin tana mai kallon idon Raniya tana dariya ta shige. Raniyan ko girgiza kai kawai tayi ta juyo ta kalli Ameetah cikin murmushi wacce itama murmushin take yi suka hada idanu sannan a hankali Raniya ta furta "that's Ajus for you!"



      Short chappy? I know, please bear with me. We met some new characters today, who's your favorite? Ajus or Raniya. Or maybe we should observe them some more for now... Next chapter coming soon in sha Allah

AMEETAHWhere stories live. Discover now