A lahadin da ya gabata Jamal Kurfi bai iso Abuja ba sai wajajen karfe biyar na yammacin ranan, amma sabili da kananan holdup din da ya riska bai iso gidan shi da ke unguwan wuse 2 Buchanan crescent ba sai daf da ana kiran sallan magrib. Duk da wutan da Ado direba ya bawa motan bayan yayi parking kafin ya kashe ta a haraban gidan, wacce ke nunawa duk wanda ya kwana ya hantse a cikin gidan cewa oga fah ya iso lafiya daga tafiyan shi, abun haushin babu wanda ya fito taryan shi, ba matan ba ba ya'yan ba dan babu kowa a gidan sai tarin yan aiki. Masu gadi ne suka zo da gudun su tun da suka garkame gate din bayan shigowan su suka bude mishi kofan ya sauko suna mai mishi barka da zuwa. Ran shi a cunkushe ya ansa musu ya doshi kofan gidan kai tsaye inda kafin ya karaso kofan ta bude daga ciki, Anty Umma ce tsaye fuskan ta fal fara'a tana ta lale marhabin da shi, dole ya dan kirkiro fara'a shima yana ansa mata har da zama bakin kujerun falon suka gaisa sossai yana tambayan yanda ya same su. Hope, wata jibgegiyar christian din Wukari na garin Taraba wacce ta kasance ita ke kula da tsaftan cikin gidan su da kuma Michael suma suka fito suka kwashi nasu gaisuwan daga bisani ya mike ya hau sama inda Hope din ke biye da shi dauke da luggage din shi.
A parlour din shi na sama da ke manne da dakin baccin shi ya tsaya inda Hope kai tsaye bedroom din ta nufa ta ajiye luggage din ta fito ta same shi still a tsaye a tsakar parlour din. Rusunawa ta yi ta ce "na kai kayan ciki sir, should we serve your food here or downstairs?" hannu ya daga mata in dismissal sannan a hankali ba tare da ya kalle ta ba ya furta "ba yanzu zan ci ba". Sai da ya ji ta rufo mishi kofn tukunna ya cire hulan kan shi ya ajiye bisa centre table din da ke tsakiyan parlour din sannan a hankali ya taka zuwa bakin sliding windows da yayi covering tun daga kusan ceiling har almost floor din, bayan ya sa hannu ya dan yaye labulen da ya rufe su. A zahiri kallon motocin da ke wucewa jefi jefi bisa titi yake yi daga wajen amma a badini tunani ne fal zuciyan shi, yana mai tambayan kan shi da kan shi shin irin tarban da ya samu a yanzu shine tarban da kowani magidanci yake samu a gidan shi bayan dawowa daga tafiya, ko kuma a'a shi ne kawai yake dawowa nashi gidan ya samu masu aiki na layi layin yi mishi barka da zuwa kaman zaman su yake yi? A take kuma ya bawa kan shi ansa a'a naka gidan ne dai da kuma gidajen wa'anda kaddara ta hau kan su irin ka in ba haka ba ko mu nan mun horu ne da tarban daddy mu mishi sannu da zuwa ko da daga office ya dawo balle daga tafiya sannan har yau ba'a bar wannan al'adan ba a gidan su daga kan matan har yaran in dai suna gida ya dawo. Amma shi yayi imanin ko da Khadijah na garin ya dawo babu abun da zai canja a tarban da ya samu a yanzu dan ya tabbatar ko keyer ta ba zai gani ba bare kuma ita, sai dai in shi ya leka in da take, in har bai je gare ta ba kuma to sai ko can anjima tukun zata leko. Da ma dai ya'yan shi na gidan ne to da dama dama, dan Umma zata fito da su su tare shi.Wayan shi ya ciro a aljihu yana mai lallatsa number din Mamee dan ya shaida mata ya iso gida lafiya, a fili ya furta "dadin abun ma dai I'm not an orphan". Sai da suka gaisa ya shaida mata ya iso gida lafiya ya tambaye ta gajiyan biki da sauran su, har zai tambaye ta jikin Ameetah kuma sai ya samu kan shi da kasa yin hakan sai sallama yayi mata sannan ya lalubo number din Dr Folorunsho cikin phone book din shi yayi dialing. Sun gaisa sannan ya bukaci sanin yaya patient din shi ta kara ji, ya tabbatar mishi duk da baya cikin asibitin a wannan lokacin komai lafiya lau yake sannan suka yi sallama. Yana kashewa wayan Zans na shigowa ya dauka yana "ango ka sha kamshi" ya ansa "Allah ja da ran JD, sarki na baturiya Dija, ka isa lafiya?" ya ce "lafiya lau, ban ma dade da shigowa ba, yaya kanwa ta?" "kanwar ka na can tare da baki" ya ja tsaki tukun ya cigaba "an zo an cika mana gida duk an hana mu sakewa, mangaribar Allah ma baza su watse ba, ba nawa yanuwan ba ba nata ba, wai meyasa gidan amarya yake da farin jini ne JD?" Jamal ya kyalkyale da dariya tukun ya ce "oho, tambayi matar ka, besides, kai ka manta lokacin da kuke zuwa gidan mutane ku saka su a gaba in the name of cin girkin amarya?" Haka dai suka cigaba da yan hirarrakin su, Jamal ya cigaba da kwasan Zanna yana dariya inda a take ya ji mood din shi yayi improving. Yana ajiye wayan yayi deciding wanka kawai zai yi da sallah ya je ya kwaso ya'yan shi a gidan Sameera. A ran shi ya ce gari dayawa ay maye ba ya ci kan shi ba duk tsiya dai an haife ni nima kuma na haifa.
A washegarin da aka sallamo Ameetah a asibiti, wato ran alhamis a safiyan ne Hajiya Amna ta tusa kan yammatan ta uku wato Raniya, Ajus da zasu koma makaranta tare da Raniya sai Ameetah sabuwar yar da Allah ya bata daga sama dan komawa gida, inda Hamisu direban ta na shekara da shekaru ya ja su tiryan tiryan har garin Kaduna inda suka shiga gida dab ana fitowa sallan la'asar daga masallacin gidan.
Ameetah da ke zaune a gidan baya tare da Mamee da kuma Ajus ware ido tayi tana kallon gari tun da Ajus ta ce mata sun iso Kaduna. Tun da take bata taba barin Maiduguri ba a can aka haife ta a can kuma ta girma sai yau din nan da Allah ya nufe ta, tana tsaka da kalle kallen ne Hamisu ya katse ta a lokacin da ya zo ya tsaya a bakin wani tangamemen gida mai hade da masallaci a jiki wacce jama'a suke ta tururuwan fitowa a ciki shaidan sallah aka idar. Gida ne da a girma ya kai gidan su na Maiduguri sai dai da gani an sha bamban a tsari da kayatuwa. Horn Hamisu ya danna inda wani soja ya leko dan tabbatar da wanene a kofar kafin aka wangale gate din suka shiga. Sauka suka yi daya bayan daya bakin su dauke da shukran isowa lafiya, Ameetah dai na kara kallon gidan da ko a ina ne a fadin duniya zaa iya kiran sa da sunan gida ya amsa kai tsaye. A lokaci daya wata mata mai yalwan fara'a ta bullo daga gidan tana ta lale marhabin da su, sannan wasu yan yara maza biyu da basu dara shekaru goma da goma sha biyu ba suka bullo ta kofan masallacin dake manne ta kofan masallacin dake manne ta cikin gidan da gudu suka iso suka rungume Raniya suna mata oyoyo sannan suka koma kan Mameen itama da runguma ta rungume su tana dariya ta ce "ni ku sake ni kar ku kayar da ni, bayan ma sai da kuka fara ganin yar uwar ku tukunna" A haka dai suka rankaya cikin gidan kowa cike da nishadi Ameetah na biye da su a baya.
YOU ARE READING
AMEETAH
RomansA Nigerian based hausa story, let's follow Ameetah on a journey of finding and redeeming one's self.