chapter two

327 45 6
                                    

      Sai da suka kai hanyan Akwanga tukun ya tuna ya ce a kai wa Sameerah su Abdul dan haka a take ya ciro wani lafiyayyen iPhone daga aljihun shi yana mai danna lambobin 'yar kanwar tashi dake aure nan Gimbiya Street a Garki. Sanin kowa ne Jamal ba wanda yake dasawa da a kannen shi irin Sameerah, wanda a zahirin gaskiya ma kannen nashi duk tsoron shi suke, tana dauka ta ce "JD, Ina kwana?" Sai da ya dan murmusa yace "Samee, me yasa baki da kunya ne, watau baza ki bar kiran sunan nan ba koh?" Ta ce "meye abun rashin kunya babban yaya, na ga sunan ka ne, ya kun fara shan bikin ne?" Ya ce "a'a nifa yanzu ma tukun nake hanyan Maid din, kin san sai jiya ma na dawo stock broker's forum din daga Johannesburg" tana dariya ta ce "ka ce bikin ya zama lami kenan babu babban abokin ango, gashi na san babes din Maid gabadaya suna can suna jiran the legendary JD Kurfi, kodayake su mamee da Raniya na can tun jiya" ya ce "to aku, ya ishe ni haka, har kin sa na mance why I called you na biyewa surutun tsiyan ki, su Abdul zan turo miki anjima weekend please dan khadijah ma won't be home" ta ce "oh tare zaku Maidugurin shine shekaran jiya da nazo nake tambayan ta yaushe zata ta ce bata Sani ba?" Ya ansa "umh umh ita Yola zata wai sunan kawar ta" sai da ta dan yi jim, a ranta tana mamakin halin wannan mata na ya Jamal, a ce duk yadda mijin ta su ke da ya Zans da kuma yadda ya tsaya tsayin daka a nasu auren ta ce zata sunan kawa har Yola? Kuma ta Sani Sarai ba wata kawar kirki ba ce, kuma in da rai ay ba daina haihuwan aka yi ba dai koh? Koh ita kan ta ba don cikin da take dauke da shi yana dan wahalar da ita ba ai ba za'a bar ta a baya ba. Ta daure ta ce "toh Allah ya kiyaye, sai sun zo din, Amma fa ka zo mana da hadaddiyar amarya daga Maid, dan na San akwai su da yawa can, ka ga nan gaba in matar gidan ta yi garin fulanin su muna da yar barebarin da zata kula mana da yaya da 'ya'ya ba sai an yi Gimbiya Street da su ba, gashi ka San sun iya kula da maza a garin." Dariya ya yi sossai, bai San dalili ba idan yana tare da Samee inji shi da fada koyaushe cikin dariya yake, sai da ya gama darawan sa yace "Allah ya sauwaka miki Samee, ai sai na gayawa khadi na, ke da kuke dasawan ma haka zaki mata? Kuma ai ni kawar ki na ce ki bani in kina son in yi aure amma kika hana ni ita" ta ce "wa kenan?" Ya ce "wannan 'yar former health minister din nan Bashir Zangon Daura" ta ce "wai Sha'awa Zangon Daura? Haba Oga JD ai ka San ta yi ma kankanta" ya ansa "ai baki san wani abu ba Samee, idan har zan Kara aure, mark my words idan har zan kara i am going to look for yar kankanuwar yarinya ne da zan iya tankwasata yadda nake so" ta ce "toh Allah yayi mana zabi na alheri yaya na" ya ce "Ameen my sister" da haka suka yi sallama ya kashe wayan shi. Ya lumshe sexy, sleepy eyes din shi da ke rikita yan mata ya jingina sossai da seat din motan, ji yake kaman ya ce da Ado ya juya su koma gida bai San meyasa ba.

Who is eager to find out more about Jamal? You? Yeah, me too... next chapter in sha Allah we take a trip back on memory lane, see ya...

AMEETAHWhere stories live. Discover now