chapter ten

114 9 0
                                    

      Ta kwashi tsawon awanni tana bacci tukun daga bisani ta farka ta tarar da wata nurse kyakyawa mai yawan fara'a a zaune a kan kujera tana duba mujalla, ta gabatar mata da kan ta as sister Nse ta kuma gaya mata ta canji sister Kubli ne. Ta nuna mata tana bukatan yin wanka da sallah inda ta taimaka mata zuwa bandakin dan haryanzu kan ta ciwo yake kaman zai tarwatse, sannan ta fito ta jawo mata kofan bandakin dan ta nuna mata bata bukatan ta kuma.
       Kallon tsaf tayi wa bandakin a ran ta tace Alhakimu gwani, bandakin asibiti kaman na wani hotel. Kan toilet seat din ta samu ta zauna tana tunanin wacce zata fisshe ta dan haryanzu bata san mai take ciki ba. Ta san dai ta baro gida ne da niyyan nesanta kan ta da garin Maiduguri gabadayan ta dan tserewa auren Mala, to amma ga abin da Allah ya dauro mata kuma. Gashi mutumin nan ya fara neman sanin wani nata dan ya mika ta gare shi ta san kuma ko karen hauka ne ya cije ta baza ta iya gaya mishi ga inda ta fito ba wallahi dan maidata zai yi, da ta koma wancan gidan kuma ta gwammace ta shiga duniya ay ta san na annabi basa taba karewa dole in wani ya ki ka wani ya tausaya maka ko aikin boyi ne dai a dauke ta ya fiye mata auren Mala kam. To amma yanzu yaya zata yi, haka zata cigaba da yi mishi kuka duk san da ya tambaye ta Koko? Kai abun da ya fi mata kawai ta tsere tun kafin ya dawo  ya kuma ritsa ta, to amma ay bata warke ba haka zata fita duk jikin ta bandeji, wa zai saurare ta? To amma in ta tsaya mutumin nan zai ritsa ta kar ma kuma ya je ya gano ta dan ta san in aka farga bata nan a gidan su wanda warhaka kam dole ne an gano ta san baban ta zai iya kai cigiya gidan radio ko talabijin kuma mutumin na iya gani.... Sister Nse ce ta katse mata tunanin ta ta hanyan buga kofan bandakin tana tambayan ta bata dai bukatan komai ko? Ta ansa ta da a'a sannan tayi hanzarin mikewa dan yin wankan.
      Bayan ta fito wankan ne ta shirya cikin wani dogon riga purple kiran Oman cikin irin kuncen da Aunty Yasato take bata, kan ta ba dankwali sabili da bandejin da ya zagaya kan, sai gashin ta da tayi kokarin tattarawa tayi wa tufka daya wanda ya sauko har gadon bayan ta. A nurses station sister Nse ta karbo mata sallaya tayi sallolin ta daga bisani sister din ta matsa mata sai ta zo ta ci abincin da driver din su ya kawo da take bacci, bata dai musa mata ba suka ci abincin tare dan cewa tayi in baza ta ci ba itama bata ci, suna ci sister Nse na mata hira kaman wasu kawaye a ran ta ko mamaki take yadda ta iya hausa sossai haka sai dan accent da ta kasa tantance na ina ne duk da dai tana ganin sister din kaman wata yar itsekiri ce ko kuma ijaw ko ta yanayin sunan ta.


Taro yayi taro a cikin hall din forshams duk inda ka juya 'yanmata ne da samari kowa ya kure a daka, masu karancin kyau ma dai in ka kalle su yau baza ka gane su ba dan an sha hoda da jambaki an fito rangadau. Komai na tafiya a tsanake cikin hall din yadda in ka kalla ka san tabbas wayewa da boko ce ta zauna da gindin ta a wajen.
      Dinner ce ake gabatarwa in honor of Zanna Abba Kyari da amaryan shi Maryam Wahbi. Daidai lokacin da MC ke gabatar da item number 7 ne Jamal Kurfi wanda tuntuni dama hankalin shi ba a wajen yake ba ya daga hannun shi na hagu ya duba agogon dake hannun shi tare da jan dan siririn tsaki a ran shi yana mai Allah wadarai da yarinyan da ke gefen shi da ta ishe shi da surutu tun da ya zauna a gefen ta a matsayin ta na babbar kawar amarya shi kuma babban abokin ango da aka hada su  zama waje daya, a ran shi ya ce ay na yi haka gwanda dai in karasa in je in ga yar mutane tunda na gama biography din. Ya juya ya kara kallon yarinyan mai suna Huwaila da ke ta babatun wai speech din shi ya fi nata dadi da tsaruwa a hankali ya furta excuse me please ya mike ya tafi ya barta da baki bude sai kamshin turare da ya bar mata tamkar a tsakiyan teburin nasu aka yi rotsen kwalban turaren.
      Wajen Zanna ya karasa ya dan rankwafo daidai kunnen shi ya ce "Zans zan karasa inga yarinyan nan a asibiti ka san gobe very early zan bar garin nan dan ina da meeting Monday morning a office gwanda in je in yi abu daya."  Zanna ya ja tsaki ya kalli amaryan shi ya juya ya kalli Jamal ya ce "ni dai ban san wani irin bad luck ne da ni ba, ka rasa lokacin da zaka kade mutum sai a aure na? Kana nan kana mun komai rabi da rabi, kai haka na maka a naka auren?" Jamal yayi murmushi ya kalli Maryam ya ce "kanwa ta kina jin mijin ki koh? Yanzu abun da za'a yi shine zan koma in zauna amma da sharadin ana tashi kai zaka raka ni, ita Maryam mu nemi mai kai ta gida ta huta abun ta, ka ga watakila kafin ka dawo ma tayi bacci abun, or what do you say kanwata?" Ta yi wani siririn dariya tana mai kallon cikin idon mijin ta mischievously ta ce "haka ne yaya na" da sauri Zans ya ce "wallahi na yafe sauka lafiya JD ma yi waya anjima ko gobe da safe" Jamal da Maryam duk suka kwashe da dariya kafin ya ce "to kanwa ta sai da safe, a dai yi hakuri da mutumi na kin san tuzuru ne, kai kuma sauran in samu labarin ka ci mun zalin kanwa ni da kai ne" daga haka ya juya ya bar Zanna na mitan shi bai san ko aljana Jamal ya kade ba, yarinya duk ta bi ta damu rayuwan su. Jamal ya fito yana kokwanton maganan Zans, a ran shi ya ce toh wa ya sani ne yarinya duk ta hana mun sakat, yana tafe fuskan shi dauke da wannan milliin dollar smile din sabili da kallon da yammatan wajen ke bin shi da shi har ya fice a hall din.
      A kan hanyan shi na zuwa asibitin ne yayi tunanin mai zai hana ya dauki Mamee su tafi tare, watakila ita Ameetah ta gaya mata wani abu dan ya fuskanci akwai wani abu tattare da yarinyan da take boyewa dan haka yayi mata waya ya shaida mata komai ta ce ya karaso ya dauketa din.




Assalamu alaykum lovelies, hope kowa na cikin koshin lafiya? Yaya ibada? And lockdown? Allah ya amshi ibadun mu, ya bamu albarkan da ke cikin watan Ramadan, ya biya mana bukatun mu na alheri ya kuma nuna mana karshen covid lafiya, Ameen. I know its been ages na samu sakkonin ku na gode da adu'o'en ku na kuma ji korafin ku but ina mai dada baku hakuri, it's all due to circumstances way beyond my control, but in sha Allah daga an yi sallah zaku ji ni akai akai, yanzun ma gaisuwa ne da rokon iri yayi prompting ina this late night post please ku saka ni a adu'o'en ku Allah ya kawo mun sauki da afwa akan abun da ke damu na da sauran musulmai baki daya, jazakumullahu bi khayr.... Sai kun ga goron sallan ku in sha Allah.

AMEETAHWhere stories live. Discover now