Abuja, friday morning 6:05 am. Tsaye yake gaban dressing table da comb a hannun shi yana mai taje kanannadadiyar bakin gashin da ya mamaye kan shi, a lokacin daya kuma tunanin doguwar tafiyan da ke gabanshi yake, duk da cewa ya Saba da yawan tafiye tafiyen ba kuma wahala take mai ba, karewa ma 'born to travel' shine sunan da dayawa cikin abokan shi ke tsokanan shi da shi, Amma a wannan safiyan ji yake kaman ya fasa tafiyan kwata kwatan shi ya zauna yayi spending weekend din tare da iyalin shi. Amma me? A zahirin gaskiya ya San ba zai iya ba Dan in yayi haka bai kyautawa Zanna Abba kyari ba, shekara da shekaru suna fama da zans yayi aure ya ki, ba ma Dan ya San abokin nashi is a womaniser ba da ba abun da zai Hana shi rantsuwa kan aminin nashi bai da lafiya ne, daga bisani kuma ya Fara tunanin ko dai wata iska ta aure shi ne Amma bayan dogon bincike ya gano lokacin ne kawai bai yi ba. Toh yau Allah ya yi zannah zai yi auren shi kuma at the last minute ya tsinci zuciyan shi cikin wasu wasin zuwa Maidugurin. Firgigit yayi ya juyo dalilin banko mai kofa da yaji an yi, kaman yadda ya zata ko hakan ne, yar ikon tashi ce Tsaye, rike take da hannun kofan tana sanye cikin pink pyjamas cotton wando da riga mai gajeren hannu da light blue flowers a jiki, dogon gashin kan ta a hargitse alamun daga bacci ta tashi, sai da ta kalleshi tsaf tukun ta tsaida idon ta kyam bisa yar kyakyawan trolley din da ke kan gadon tace "haba Jamal, yanzu Dan rashin adalci zaka kama hanya kayi tafiyan ka bayan ni ka Hana ni tafiya wai wani baka son a tafi a bar maka yara su kadai, meye amfanin Umma a gidan nan?" Ya rausayar da kan shi yace "khadijah kenan, i thought gaisuwa ne ya kamata ya shiga tsakani na da ke at this time of the day ba dogayen maganganu ba" comb din hannun shi ya ajiye a kan dressing table ya dauko turaren Burberry touch for men sai da ya bincire hancin turaren ya cigaba "yanzu da ke mai hankali ce khadijah ai cewa zakiyi mu tafi auren zans tare saboda kin San waye zans a Gare ni Amma sai kika tsiri tafiya Yola sunan kawa bayan kin korar ma yaran nan nanny din su Na shekara da shekaru, ita anty umman baiwar ki ce? Duk ayyukan da take yi a gidan nan?" Tace "oh! Dan Na ce zani Yola sunan suwaiba shine zaka ce Banda hankali? Zuwa auren zanna dai baza ni ba Dan Ina da sabga a gaba Na, Na kuma yi wa suwaiba Alkawarin zuwa sunan ta Dan haka zuwa Yola kaman Na je Na gama" ba tare da ya Kara kallon ta ba yace "Umma ta gaida Aisha Amma ki Sani ba da yawu Na kika tafi ba" bai Kara bi ta kan gunagunin ta ba ya Ciro rafar kudi ya jefa a kan gadon ya dau hulan shi Na Zanna tare da akwatin shi ya zura wani takalmin fata Navy blue mai kama da Baki Baki kirar Davina. Sai da ya kai daf da ita ya rage tsawon shi tana shakan fitinannen kamshin da ke tashi jikin shi ya manna tattausan lips din shi a kan goshin ta yayi pecking din ta yace "ga kudi bisa gado ko zaku bukata, ni Na tafi" daga haka bai Kara waiwayon ta ba yayi gaba abun shi. A kule ta juyo tana kallon shi sai de meye ita kan ta ta San duk rashin kunyan ta da masifan ta da balain ta, so daya dai kam Jamal Kurfi take yi wa. Cikin sassarfan takun kasaita ya iso dinning table din Dake falonshi Na sama, inda ya samu kukun su Michael ya shirya mai lafiyayyen breakfast, cappuccino kadai ya iya sha mug daya kasancewan bai Saba cin Abu da sassafe haka ba ga kuma bacin ran khadijah. Dakin yaran shi ya shiga ya samu dukkan su biyu bacci suke yi ya sumbace su ya gyara musu kwanciya sannan ya fito. A matakalar bene suka hadu da anty umma tana hawowa shi kuma yana sauka. Anty umma tsohuwar ma'aikaciya ce a gidan iyayen shi Dake Kaduna, Dan shi kan shi ya taso ne ya budi ido ya gan ta a gidan nasu, kusan duk su ma ita tayi rainon su. Bayan sun gaisa yake shaida mata Maiduguri ya nufa daurin auren Zannah, kasancewan ba Wanda bai San shi tare da Zannah ba. Tayi mishi fatan Allah ya kiyaye hanya tare da sakon gaisuwa da fatan alheri ga Zannan, yace "Anty Umma Dan Allah in yaran sun tashi a musu wanka a shirya Sani ya ajiye su gidan sameera duk da kayan su suyi weekend can, Dan Na ji matar gidan Na cewa Yola zata duk da Na Hana" tayi murmushi ta ansa da toh, a ran ta ko tana mamakin Hali Irin Na Khadija da ba'a isa a saka ta ba balle a Hana tare da Na jamalun shi kuma da yake biye Mata namiji har namiji da shi. Ita ma rafar kudin ya hada ta dashi kaman yadda ya Saba in zai yi tafiya Dan hidiman gida da kuma Wanda zata sallami masu aiki. Ya fito ya shiga motar shi range Rover masu gadin gidan Na mai daga mishi hannu Ado direba ya dau hanyan yerwa Na Shehu larabawan bidi'a.
YOU ARE READING
AMEETAH
RomanceA Nigerian based hausa story, let's follow Ameetah on a journey of finding and redeeming one's self.