Jamaludeen Dalhatu Kurfi ya kasance da namiji kwaya daya da Hajiya Amna (Fatima) da tsohon soldier General Dalhatu Kurfi suka mallaka a cikin 'ya'yan su shida, duk da shi General Kurfi yana da wasu 'yan samarin daga amaryan shi Hajiya Nana wanda ita nata 'ya'yan duk maza ne guda biyu.
Ainihin Dalhatu Kurfi bakatsine ne dan asalin garin Kurfi, malunta shi ne gadon gidan su dan mahaifin shi Mallam Mamman Kurfi tsohon malami ne da ya gaji malunta kaka da kakanni, Mallam Mamman yana da kanwa kwaya daya tak da ke ansa sunan Asiya wacce itama a nan cikin Kurfi din take auren wani malamin makarantan boko. Dalhatu shine da daya da Mallam Mamman da matar shi Mairo suka haifa, Dalhatu ya taso ne cikin karatun muhammadiya inda yayi sauka yana da shekaru goma sha daya kacal a duniya, burin Dalhatu a duniya shi ne karatun boko amma Mallam Mamman rufe ido yayi ya ce shi Sam bai San wannan ba, akidun yahudu da nasara ba'a gidan shi ba. Da nufin Allah da kuma taimakon Mallam Sidi mijin Gwoggo Asi Dalhatu ya Fara karatun boko, inda bayan ya kammalla secondary school din shi a wani government college Dake Enugu, mijin Gwoggo Asi da ke commissioner din ilimi a cikin jihar Katsina a lokacin Wanda a lokacin kuma yake ansa Alhaji Sidi ya nema mishi makarantan hoton sojoji a Kaduna da Dalhatu ya nuna shi yake sha'awa, inda bayan shekaru uku ya fito da aninin shi na farko a aikin soja aka kuma yi posting din shi warri.
A warri Allah ya hada 2nd lieutenant Dalhatu Kurfi da Abba kyari Kukawa wanda shi ma matsayin su daya a lokacin wato 2nd lieutenant. A nan Allah ya hada jinin su, lokacin da aka turo su Maiduguri ne aiki bayan shekaru hudu a warri basu yi masauki a ko ina ba sai gidan su Abban, kasancewan shi dan asalin jihar borno ne, a nan ne soyayya mai karfi ya kullu a tsakanin Amna kanwar Abba da Dalhatu. Ganin hankalin shi da kuma sanin cewa he has a very bright future ahead ya sa Allah ya jikan rai mahaifin Abba Alhaji Kyari Kukawa yabawa Dalhatu Amna da sharadin zata yi karatu har sai ta budi baki da kan ta ta ce ya ishe ta. Dalhatu ko ya zama dan halak dan ya cika burin Alhaji Kyari duk da Allah bai bashi nisan kwanan da ya gani ba don Amna ta yi karatun da har take da title din Mrs Fatima D. Kurfi (SAN) wato senior advocate of Nigeria a yanzu haka, infact har Babcock university ta tsallaka da miji da 'ya'ya da Komi ta tafi ta bar su a hannun amintaciyar mai aikin ta wato umma ta dauko kwalin LLM din ta a law a wancan zamanin bayan ta samo LLB a ABU Zaria.
Jajircewa da sadaukar da kai ga aikin shi, shi ya siyowa Dalhatu Kurfi matsayi daban daban a aikin shi, inda ya Riki mukamai da dama kaman su military governor Lagos State, da kuma chief of defence staff a mulkin soja daban daban. Namiji ne Irin sauran mazan jiya, kainuwa dashen Allah ba na mutum ba.
General Kurfi ya yi ritaya ne a shekaran da ya gabata inda ya tsunduma harkan kasuwanci na zallan fatan nan mai amfani wato moraco leather da yake exporting fatun zuwa kasar Italy ya kuma yi importing din products din su bayan an sarrafa gida Nigeria da kuma sauran kasashe, sai kuma harkan noma. Gida ne Na gani a fada yake zaune da a ciki da matan shi biyu da 'ya'ya a unguwan rimi, Ja Abdulkadir Street.
Auren shi da amaryan shi Hajiya Nana aure ne da ya faro kaman wasa. Dan Nana Aisha kanwa take ga Dalhatu dan 'yar Gwoggon shi Asi ce, Nana kyakyawar bafulatana ce da kyau kaman ita ta yi kan ta. Ta kuma taba auren da bata so ko da wasa ana tuna Mata shi inda ta haifi 'yar ta daya a can Maiduguri da wani abokin baban ta. Bakar wahala kam ta sha shi a hannun kishiyoyi, dama kuma dole aka Mata ta auri mutumin, dan haka ne ma da suka kulla mata munafurcin da ya hada ta da takardan sakin ta guda uku kwarara ya kuma ce kada ta kuskura ta taba mishi 'ya itama ta dangwarar mishi abun shi tayi gaba abun ta.
A haka ta dawo gidan mahaifin ta a Katsina duk ta rame ta kode ta jeme, kai baka ce Nana ba ce 'Katsina beauty' inji samarin garin a zamanin budurcin ta. Alhaji Sidi ji yayi kaman ya nemo bindiga ya harbe kan shi, a ganin shi duk shi ya jawo wa 'yar tashi, duk da shi ma ba wai ya so bane a lokacin, dan SK Gubio daure shi yayi da jijiyoyin jikin shi har ya aura mishi Nanan shi dan bai yi niyyan aurar da ita a lokacin ba, a Dan shekarun ta Na goma sha bakwai da ta kammalla karatun secondary, Amma sheriff Kachalla Gubio ya tattaro mai mutanen da yake Jin nauyi tare da kunyan su har ya aura mai Nana da sharadin zata ci gaba da karatun, gashi yau bayan shekaru uku ya sako mishi 'yar tashi ba tare da ta koyo ko alif a gidan shi ba, har kuma da cewa bai yarda ta dau mai 'ya ba. In ma ba kaddara ba meye ya kai 'yar shi hada zuri'a da SK. A haka Nana ta hau zaman idda a gidan su cikin iyayen ta da kannen ta Safiyya da Sa'ada. Tana kammalawa mahaifin ta ya samo mata admission a university of Leicester da ke UK inda ta fara karantar petroleum engineering. sai da ta shafe shekaru biyar a can ta hado har da masters din ta tukun ta dawo gida Nigeria, ta goge ta murje ke ba kya ce Aisha Sidi bace, ta zama kaman wata balarabiyan Iraqi.
A Lagos tayi service din ta inda ta zauna gidan yayan ta Dalhatu a shekaran da yake military governor a Lagos din. Nan da nan maza suka shiga tsirtuwa suna fito Mata, samarin da zaurawa, yara da kanana, daga ciki har da abokanan Dalhatun, amma ta rufe ido ta ce Sam bata San wannan ba Dan maza sun fice Mata a rai
YOU ARE READING
AMEETAH
RomanceA Nigerian based hausa story, let's follow Ameetah on a journey of finding and redeeming one's self.