chapter nine

203 23 2
                                    

      A hankali ta bude idon ta, bakin ta dauke da salati, in ka dauke karan agogon da ke bada tik tik a kowani dakika babu wani kara a dakin dan ko AC din da ke ta aikin ta irin lafiyayyen nan ne da bai fitas da sautin komai sai bala'in sanyi. Kallon tsab tayi wa dakin inda ta fuskanci asibiti ne dai wajen. A hankali kwakwalwar ta ta fara tariyo mata abun da ya faru tamkar a majigi. Tabbas mota ce ta buge ta a kokarin ta na gudun hijran ta. Wani irin radadi ne ke addaban kan ta da ke barazanan tarwatsewa ga hannun ta na hagu na wani irin zogi. Salatin da take yi ne, a'ah hannun ta na dama mai dauke da karin jinin da ta motsa ne ya farkar da sister Kubli? Da shike sistern na rike da hannun ne bacci ya kwashe ta, Allahu a'alam. Sistern dai ta farka daga baccin da ya kwashe ta tana daga zaune bisa kujeran jinyar su sai faman zabga mata sannu take yi, a ran ta kuwa hamdala take yi da matron on duty bata leko ta gan ta tana bacci ba, wai! Da yau sai ta gayawa 'yamtar wala' sarkin baburawa. Nan da nan Kubli ta duba agogon dakin da ya nuna karfe uku saura minti goma sha bakwai na dare, ta tuno Dr Folorunsho ya ce in ta farka komai dare a nemo shi dan haka ta dau kan waya ta saka nurses din da ke nurses station su nemo shi. A take ya shigo ya duba ta ya tabbatas komai na tafiya yanda suke so, bayan ya dan yi mata tambayoyi ta ansa ta bukaci shan ruwa, kublin ce dai ta nemo mata a nurses station din kasancewan ba komai na ci ko sha a dakin. Bayan ta sha ta koma bacci sakamakon alluran da Dr Folorunsho ya danna mata.

*      *      *       *       *      *       *       *      *
      Agogon Raymond Weil din da ke hannun shi ya dada kallo, yana jin kaman Ado baya sauri kaman ya karbe ya ja motan, tunanin shi duk yana kan yarinyan, ko yaya ta kwana? oho! Ya so zuwa asibitin da wuri amma a bisa dole sai da ya fara zuwa aka daura auren Zans da shi tukunna dan ana shafa fatiha bai ma bi ta kan reception din maza zalla da ake ta kokarin zuwa a pinnacle ba yayi gaba abun shi. A sukwane ya doshi cikin asibitin Ado na bin shi a baya rike da basket din da ke shake da tarkacen breakfast da Mameen ta sa Halti Hamrah ta shirya musamman dan marar lafiyan yana mai adduan Allah dai ya sa ta farfado.
      Wata jikakkiyar wagambari ce a jikin shi mai karshen tsadan kalan ta ash sai daukan ido take yi, ya sha aiki irin na kasaitatun mazan Maiduguri. Zaman hulan shi na Zanna Bukar Dipcharima kadai zaka kalla bisa goshin sa ka san tabbas 'Adi Mallam Nasaraye' inji bare bari ga wani lafiayyen slippers din Russel and Bromley da ya bi ya lafe kafan shi da ya sha pedicure ya koma tamkar na jariri sabon haihuwa. A nutse ya murda kofan VIP 1 cike da isa da ginshira tamkar wani jinin sarauta ya karaso bakin gadon cikin takun girma. Hamdala ya fara jerowa cikin ran shi ganin tana zaune bisa gadon da nurse zaune gefen ta a kan kujera ga kuma TV tana aikin ta on a very low volume. Dara daran idanuwan ta ta dago ta aza mishi wanda shi ma ya dago nashi idanun kaf a nata. A hankali ta saukar da nata saboda zuciyar ta da ta shiga bugawa ba kakkautawa. Muryan nurse din ya tsinkayo tana gaida shi a hankali ya amsa tare da tambayan ta mai jiki ta amsa "da sauki" sai faman washe baki  take yi tana fari da ido tana jujjuyawa a ran shi ya ce "kin kama aiki". Mikewa tayi tana mai cewa "yallabai bismillah mana,ga kujera, zauna, bari na dan zagaya nurse's station" ta juya ta fita sai karye karye take yi. Ado ma ya gaida ta da jiki sannan ya ajiye basket din ya fita dan komawa mota zaman jiran uban gidan shi. Sai a lokacin ya samu maido hankalin shi gareta, tana zauta ne dai still da kan ta a sadde a kasa ta bi ta takure a jikin gadon, a hankali ya soma magana "don na buge ki da mota jiya doesn't mean I'm a monster, ba dodo bane ni bana kuma cinye yara da kika bi duk kika takura kan ki" bata san sanda ta dago ta dube shi a mamakance ba, ya sakar mata da wannan million dollar smile din nashi tare da furta "better, ko ke fah? To yanzu yaya jikin?" cikin wata yar kankanuwar murya mai kama da ana busa sarewa ta amsa "da sauki" ya ce "ina kike jin ciwo yanzu? " ta ce "kai na" tana shafa inda aka nade da bandage a kan, ya ce "da ina kuma?" ta ce "sai hannu" ya ce "wannan dole ne ganin irin buguwan da kika yi a kan, hannun kuma Dr ya ce zasu yi fixing yau, sai dai a garin yaya kike tafiya kan hanya tamkar wata makauniya erm...., ashe ma baki gaya mun sunan naki ba" ta ce "Ameetah" ya ce "nice name, so how come kike tafiya bisa titi Ameetah?" Har a kwanyan ta ta ji kiran da yayi ma sunan ta, sai ta ji nan duniya kaman shi kadai ya iya hada syllables din nan uku su fito sak. Ta yi rau rau da ido kaman zata yi kuka ta ce "nima ban sani ba" ya ce "to sai ki bani phone number ko address din gidan ku a sanar wa iyayen ki koh, I'm sure duk sun damu warhaka, kila ma har an fara cigiyan ki gidajen radio da tv stations" a take ta ji wani irin tsinkan zuciya, hawayen da take ta kokarin maida su suka ballo shar shar. Ya ce "ki ce dai shagwababbiya ce ke, daga ambaton iyayen ki har kin fara kuka, yi hakuri yanzun na Za'a nemo su, kiyi shiru please" amma inaa, tamkar kara zuga ta ma yake yi.
      Juyin duniyan nan yayi amma bata ce da shi kanzil ba sai kuka, daga karshe ya gano maganan ne ma bata so kwata kwata, dan haka ya rufe chapter din ya lallabata tayi shiru. Ya ce "to saura abinci, shi kam in kika mun kuka Dr zan nemo ya tsikara miki allura, ko kina son allura?" da sauri ta girgiza kan ta a'ah, ya ce "toh, sai kiyi harama" Da kan shi ya janyo basket din ya soma zubawa, dankali ne aka dafa a saukake irin na marar lafiya tare da hanta da tarkacen su carrots da peas sai farfesun zallan koda da ya sha kayan kamshi sai kuma tarkacen kayan tea. Sai da ya zuba mata komai, ya ce "oya, bismillah!"
       Wannan karon a gefen ta ya zauna bisa gadon ya tsare ta da ido ya kuma cika mata hanci da kamshin turaren shi na Creed Aventus. Ita dai ta san ba wai rashin iya girki bane yake damun ita ko mataan baban ta, ta san kuma ba wai mai maikon bane ba'a dafawa a gidan su ba, duk da dai a kullum wanda aka ci aka ragen shi ne rabon ta, amma ita dai ta rasa meyasa ta ci abincin nan sosai, walau yunwan da ke nanike da ita ne, koko dandanon abincin ne, a'ah idanuwan da wannann bawan Allahn da ko sunan shi bata sani ba ya tsare ta da su ne Allahu a'alam, ita da ta cinye tas. Yana cikin clearing kayan ne sister Kubli ta shigo tare da wani Dr, tana shigowa ta fara "haba yallabai, wannan ai duk aiki na ne, da ka kira ni na zo nayi ay" ya ce "ba komai sister, i don't mind, wanda kike ta yi tun jiya ma Allah ya saka da alheri" ta dada yin fari da ido ganin an yaba mata ta ce "Ameen, wannan Dr Grema ne,shi zai yi gyaran hannun" ai ko Mutuniyar ku na jin haka ta zabura ta hau zaro ido, dukkan su ta basu dariya. Dr Grema ya ce "haba kanwa ta, ke da nake ganin kaman zaki yi hakuri da dauriya din? Kawai ki saka a ran ki ba zafi and ba zai yi miki zafi ba" Ai ko kusan rabin asibitin nan sai da suka san ana gyaran hannu dan kuka ne har da majina Ameetah ta sha, da kyar Jamal ya matse ta jikin shi aka gyara hannun alluran sannan sister Kubli ta danna mata wani alluran pain killer mai dauke da maganin bacci a cikin shi. Tana nan kwance a jikin nashi yana aikin shafa kan ta zuwa bayan ta, sai hawaye take zubarwa tana sheshekar kuka tamkar wata yar baby har bacci ya kwashe ta tukun ya gyara pillown ya kwantar da ita a hankali yayi wa Kubli sallama ya tafi.

     A late update for all my fellow insomniacs,where art thou? I know this is the longest I've gone without updating but sannu sannu baya hana zuwa sai dai a dade ba'a je ba, we'll surely get there in sha Allah, please bear with me...jazakumullahu khayran...

AMEETAHWhere stories live. Discover now