A daidai lokacin ne kuma Hajiya Amna ta tadawa Dalhatu darun sai de ya kara aure, a cewan ta abubuwa sun mata yawa sabili da career din ta da take pursuing a fannin law, gashi ita ce first lady Lagos State, har ila yau kuma ga miji da 'ya'yan da suke neman attention, duk da cewa she gives ample time wajen ganin ta zamo mata da uwa ta gari. Ta dade tana tado wannan maganan Dalhatun na kashewa, amma a yanzu dagewa ta yi har ma kuma da kawo shawaran matan da take ganin za'a yi zaman lumana wato Nana. Da farko Dalhatun ya ki, amma daga baya da irin pressure din da Amna take hada mishi, gashi ya riga da ya bata ta da bata duk wani abu da take so, gashi kuma a hankali kyau tsantsa da kyawawan halaye Irin na Nana suka fara janyo hankalin shi, bai san lokacin da ya amince ba.
Ko a fuska basu nunawa Nana komai ba sanin halin ta tsab zata birkice musu ta ce bata yadda ba dan haka suka shirya wani weekend suka bi jirgi ya sauke su katsina, suka baro Nana da Umma da kuma yara a Lagos. Kai tsaye gidan Alhaji Sidi suka zarce, bayan murnan ganin juna da gaishe gaishe, aka kuma wadata su da abinci da abun sha ne Hajiya Amna ta kaskantar da kan ta cikin karamin murya ta shaidawa Alhaji Sidi abun da ke tafe da su na son a bawa Dalhatu auren Nana. Jimm Alhaji Sidi yayi yana mai jinjina abun a ran shi, tabbas yayi alkawarin bazai Kara yi wa ko daya daga cikin 'ya'yan sa auren dole ba sai in har su da kan su suka kawo miji suka ce suna so, dan ba shakka ya dau darasi auren Nana da SK. Toh amma wannan Dalhatu ne da yake gani kaman the son he never had, wannan Dalhatu ne da lokacin mutuwan auren Nana ya dau alwashin sai ya koya ma SK Gubio hankali ba dan shi Alhaji Sidin ya hana shi ba, wannan Dalhatu ne da yayi alkawarin sai ya dauko wa Nana 'yar ta da SK ya hana mata amma ita Nanan ta nuna bata sha'awan rike yarinyan, wannan Dalhatu ne da ya san ko bayan ran shi mai kula mishi da iyalin shi gaba daya ne duk rintsi ba wai Nana kadai ba ma, sannan wannan Dalhatu ne da ba zai iya hana shi wani abu ba in har yana da shi. Don haka ya nisa ya ce "haba Dalhatu, Ina kai mai bada auren Nana Aisha ne ga gyartain garin nan ma idan ka ga dama? Toh Ina dalilin da zaku baro aikin ku, da jama'a ku zo har nan dan gabatar da wannan bukata? Wannan ai zance ne da ko a waya ma sai mu yi ta, in dai Aisha ce na baka ita duniya da lahira, dama masu neman auren Sa'ada ma sati mai zuwa zasu zo daga Yola, dan haka in komai ya daidaita sai a hada gabadaya."
To masomin auren Dalhatu da Nana kenan, duk da bori da turje-turjen da tayi, inda Dalhatun ya maida kan shi dan yaro ya lallaba ta har ta gama ta sauko dan kan ta, bayan ta fahimci namiji ne irin every woman's dream da babu mace in her right senses da zata ki General Kurfi, dan namiji ne da iyalan shi sune kan gaba a komai na rayuwar shi. A yanzu haka Hajiya Nana, 'yar shekaru talatin da takwas ma'aikaciya ce a matatar mai ta Kaduna watau kaduna refinery kuma uwar 'yan samari biyu, Abba Sidi, da Muhammad da yake autan gidan General din, Dan Hajiya Amna ko in ce Mamee, a yadda 'ya'yan ta da Na 'yan uwa da abokan arziki ke kiran ta, ta daina haihuwa ne tun a kan Raniya yar shekaru goma sha takwas da ke karantar Accounting and Finance zallah a Middlesex university da ke Dubai.
Babbar 'yar General Kurfi da Hajiya Amna ita ce Maryam da suke Kira Ammabuwa a dalilin sunan mahaifiyar General da ta ci wato Inna Mairo, bi ma'ana Maman baban ta da Shuwa inda ita Mamee ita ke kiran ta da sunan a dalilin sunan surukar ta da ba zata iya fadi ba har kowa ya dauki sunan. Ammabuwa na auren wani ma'aikacin Nigerian Embassy inda a yanzu haka suna foreign posting ne a garin Zurich da ke kasar Switzerland. Jamal shi ke bin ta sannan Hadiza wacce medical doctor ce a National hospital a Abuja tana kuma aure ne a Gana street, Maitama. Rukayya ce ke bin ta sannan Sameerah Wanda shekaran da ya gabata aka aurar da su bayan sun kammalla nasu degree program din a Gwagwalada university a Abuja sai 'yar auta Raniya.
Rayuwan gidan tsohon sojan ya kasance rayuwa mai ban sha'awa ga kowa da ya shiga gidan, dan kullum cikin wasa da dariya, sakin fuska, raha gami da barkwanci suke kama daga mijin zuwa matan har 'ya'yan nasu, babu yanda zaka shiga gidan ka ce Mamee ba ita ta haifi Abba ko Muhammad ba, haka kuma duk inda kaji 'yan matan gidan General suna wani kus-kus din toh da Hajiya Nana ne, Dan ko wani matsalan suke da shi toh Anty Nana ake fara nema kafin ma Mamee ta ji shi. Wani lokacin har su yi su gama ma a tsakanin su ba tare da uwar ta Sani ba, haka itama Nanan komai zaka ji ta ce 'yan matan ta.Short chapter? I know, please bear with me, another one coming right up and it's all about how Jamal met khadijah... Mu je zuwa...
YOU ARE READING
AMEETAH
RomanceA Nigerian based hausa story, let's follow Ameetah on a journey of finding and redeeming one's self.