A razane ya fito yayi kan ta inda take kwance flat bisa kwalta da ghana must gon ta a yashe can gefe guda ga kuma jama'a 'yan kawo dauki har sun fara taruwa. Wasu daga ciki ma tambaya suke ko ta mutu ne sakamakon rashin motsin da take yi. A razane ya durkusa yana neman heartbeat da pulse din ta, babu abun da ya dada gigita shi irin wani jini dake kwarara a goshin ta dab saman idon ta tamkar lalataciyyar famfon da ta ki rufuwa. A gigice ya sa hannu ya ciccibe ta ba tare da ya kula jama'an da ke ta surutu kowa na fadin albarkacin bakin shi ba ya jefa ta a bayan motan shi, wani bawan Allah ya miko mishi bagcon nata ya hada ya jefa ciki ba tare da sanin inda zai nufa da ita ba bakin shi dauke da addu'o'e yana mai rokon Allah ya sa kada ta mutu a sanadiyyar shi.
Tafiya yake ba tare da ya san inda zai nufa da ita ba, sai can hanyan NTA ya ga sign board din wani private hospital, a take ya karya kwana ya shiga cikin asibitin yayi parking ya zagaya ya dauko ta a bayan mota kaman yar babyn roba still bata ko motsi ga wannan jinin yana dada bulbula, ko rufe motan bai yi ba ya doshi main entrance din da azama yana mai hada matakalan bibbiyu wadda zai sada shi da cikin asibitin. Saurayin da yake bayan kanta a reception din ne yayi saurin fitowa tare da kiran wasu nurses din aka amshe ta da sauri sai emergency room din asibitin inda suka mai nuni da ba'a shiga dan haka tare suka juyo da receptionist din zuwa reception, inda ya dau kan waya ya kira doctor on call yana mai shaida mishi emergency aka kawo. Yana nan tsaye dai doctorn ya zo ya wuce shi ya shige ER din. Ya shiga kaiwa da kawowa a harabar reception din zuciyan shi cike da fargaba bakin shi dauke da addu'o'e yana mai rokon ya rahmanu ya rahimu da ya tashi kafadan 'yar mutane. Daya daga cikin masu gadin asibitin ne ya shigo yake cewa "yallabai ka bar motar ka a bude" fita yayi ya gyara parking din tare da rufe motan ya dawo, inda sai a lokacin ya samu kujera daidai ER din ya rage tsawon shi tare da zaran karan taban davidoff daya cikin kwalin ta da ya fiddo cikin glove compartment din motar shi ya zaro wani lighter mai shegen kyau daga aljihun shi ya kunna ta ya hau zukar abun shi ba tare da ya bi ta kan 'No smoking' warning din da ke manne ta ko ina a reception din ba. Receptionist din ne ya tunkaro shi da wata 'yar file a hannun shi, a mamakance ya tsaya a gaban shi yana mai kallon taban da Jamal din ke zuka yana fesar da hayakin cikin gwanancewa amma cikar zati irin na Jamal din ya hana shi cewa komai sai ma gabatar da abun da ya kawo shi wato tambayan shi suna da sauran abubuwa a kan patient din dan bude mata folder da kuma shaida mishi sai yayi depositing 50000 naira dan kula da lafiyan ta wanda daga bisani asibitin zasu bukaci kari daga baya ko kuma su su baka canjin ka dangane da cigaban da aka samu. Kallon tsab Jamal yayi masa wanda sai a yanzu ya lura da nametag din dake a sagale a jikin rigar shi mai dauke da sunan Ola, ya ce a ran shi shi wannan Ola din damuwan shi kenan? Amma a zahiri sai ya nisa ba tare da ya ce uffan ba ya mike ya koma motan shi ya dauko mai rafar Zik ya dire gaban shi tare da cewa "ban san sunan ta ba, ban kuma san komai a kan ta ba, sai dai ka jira in Allah ya tashe ta ta gaya maka da kan ta." Daga haka ya juya ya koma mazaunin shi na farko Ola kuma ya bi shi da ido zuru.
Wani irin tattausan kida ne ya shiga tashi daga aljihun shi tabbacin wayar shi ce take kara. Fiddo wayan yayi ya zuba ma screen din ido yana kallon sunan Zans da ya fito baro baro a kai. Shaf ya manta da wani Zans, da wani jiran shi da suke yi dan a tafi wani wushe wushe. A hankali ya danna answering button din ya kara a kunnen shi amma bai ce komai ba ya cigaba da zukan sigarin shi. Muryan Zans din ya tsinkaya yana "haba JD! Wai wani irin iskanci ne haka yake damun ka, bayan ka san kai nake jira ba kuma zan iya tafiya wajen nan ba tare da kai ba, where the hell are you? " Tamkar mai ciwon baki ya furta a hankali "asibiti" yace "wani irin asibiti kuma, anya ma lafiyan ka kuwa? ya naji muryan ka haka, ko ka fara buga slow ne ban sani ba JD, tell me are you stoned? Menene? coke?heroine?..."a fusace ya katse shi "oh shut up Zans, i had an accident " "Hasbunallah wa ni'imal wakeel" Zanna ya fadi da iyakacin karfin shi kafin ya cigaba "a ina? Yaushe? Ta yaya?" ya ce "calm down ba ni bane wata yarinya na buge a kan titin Damboa road gashi tana nan rai a hannun Allah an shiga da ita emergency room and basu ce mun komai ba haryanzu" ya ce "wani asibiti ne gamu nan zuwa yanzu ni da Agid" ya ansa "a'ah ku dai karasa wajen bikin kada mu zama kananan mutane mu bar amarya da jira, i'll be fine" ya tambaya "ka tabbata?" ya ansa "sure" suka yi sallama da zummar ana tashi a wushe wushen zasu tsaya su duba shi. A irin wannan yanayin babu abun da Jamal ke so irin ya samu inda zaa rike shi a gaya mishi maganganu masu sanyi dan shi namiji ne mai son petting, sai aka yi rashin saa wacce ya kamata ta bashi wannan kulawan Khadijah ce, wacce da zai iya da ya lalubo ta a waya ya gaya mata komai, to amna a zahirin gaskiya ba zai iya ba, dan in zai gaya ma kan shi gaskiya ma haushin ta yake ji saboda a ganin shi duk ita ta ja mai don da bai shiga bacin ran da ta haddasa mishi ba da bai yi loosing control har haka ba. Don haka sai ya lalubo number din Mameen shi yayi dialing. A lokacin Hajiya Ammuna na zaune ne a tsakar dakin Hajiya Toma matar wan ta kuma uwar angon da ita da kannen ta mata biyu Halti Hamrah da Halti Hamziye suna hada kayan gyauro da za'a kai gidan su amaryan a washegari bayan daurin aure ta ji karar wayan ta ta ce Hamziye ta miko mata. Bayan sun gaisa ne yake gaya mata abun da ya faru ta ce "Assha! Subhanallah! Ga ni nan zuwa yanzu, ka cigaba da ambaton mata as'alul lahul azeem rabbil arshil kareem an yashfiki, Allah zai bata sauki" Hamziye suka bari da karasa aikin suka nada laffayan su ita da Hamrah driver ya kai su asibitin a sabili da su iyaye ne basu tafi wajen wushe wushen ba sai su Raniya.
Sha daya da wani abu tukun Dr Folorunsho ya fito ER din ya nufo inda suke zaune, Mamee, Halti Hamrah da Jamal din. A sukwane ya mike ya karasa ya cimma Dr din inda ya fara mishi bayanin ta samu buguwa ne a kan ta a dalilin shi ne take unconscious haryanzu amma suna fatan farfadowan ta ba da jimawa ba dan babu wani ciwo ta ciki, sai kuma tsagewan kashin hannun ta wanda sai ta farfado zaa kira orthopedic doctor din su ya gyara sai kuma jini da ake nema ayi transfusing din ta saboda wanda ta zubar duk da an samu an tsaida. Nan take ya ce a duba nashi in yayi dai dai a diba. A nan su Mamee suka yi mishi sallama suka tafi da shike sun ji abun da dan sauki. Sai bayan an dibi jinin shi ne da aka samu yana group o+ universal donor an kuma yi screening bashi dauke da cutan HIV ko hepatitis da sauran cututuka da ke hana transfusion sannan aka maida ta daya daga cikin VIP rooms din asibitin aka daura mata jinin. Dr Folorunsho ya tabbatas mishi nurses din su zasu bata cikakkiyar kulawa a sabili da su ke jinyan mara lafiya a wannan sashi na VIP tukun ya samu tafiya da su Zans da suka zo bayan an kare wushe wushen.
YOU ARE READING
AMEETAH
RomanceA Nigerian based hausa story, let's follow Ameetah on a journey of finding and redeeming one's self.