chapter twelve

151 13 4
                                    

"Ni ban taba ganin uwa da uban da suka kawo ni duniya ba, na taso ne a wajen kaka ta ta wajen mahaifiya ta, baba na babarbare ne dan asalin garin nan yayin da mahaifiya ta Baggara ce wato shuwan N'Djamena. Mahaifi na dan kasuwa ne wanda kasuwanci ne ya kai shi garin Mao da mahaifiya ta har suka hadu soyayya ta kullu a tsakanin su har ta kai ga aure da zummar bayan bikin zai taho da ita taga dangin shi sannan su koma su yi rayuwan auren su a nan N'Djamena. bayan bikin ne ya kamu da ciwo aka yi ta magani amma ashe abun ba na tashi bane, ya rasu bayan auren su da wata biyar ya bar mahaifiya ta da cikin wata hudu. A yadda Hajja kaka ta ta gaya mun tun rasuwan mahaifi na mahaifiya ta bata kara lafiya ba har watan haihuwan ta ya tsaya, wanda ta haife ni ne bayan tayi kwanaki tana nakuda, da ta haihu kuma ko sani a ido bata yi ba itama Allah yayi ikon shi a kan ta". Ta cigaba da shesshekan kuka yayin da Jamal ya mika hannu gefen gadon ya zaro tissue ya mika mata ta karba ta share hawayen ta sannan ta cigaba "a haka na taso a hannun Hajja kaka ta wacce itama ita kadai ce mijin ta ya dade da rasuwa bata da kowa dama sai 'yar ta mahaifiya ta sai kuma kannin ta Abu Amma da yake zaune a Kusri din kasar Cameroun dan haka can muka koma da zama wajen shi. Na taso a Kusri cikin gata da kulawa har na kai shekaru goma kwatsam Allah ya aikowa Abu Amma nashi ciwon ajalin. Bayan rasuwan shi ne da shike shima bai taba haihuwa ba Hajja ta tattaroni tayi Maiduguri da ni wai ta nemi dangin baba na ta danka musu ni kar na Allah ya kasance a kan ta a rasa mai kula da ni. A kwatancen da yayi musu yan uwan shi a unguwan La'an Bukar suke, mun zagaye gabadayan La'an Bukar da Hajja da sunan yan uwan shi da kuma na gidan su da na shi kan shi tare da abubuwan da ya bari amma bamu samu ko wanda ya san su ba har muka gaji, ga abun da muka zo da shi duk ya kare. A dole Hajja ta nemi aiki a wani gida a nan Damboa road tana musu aikin girki muna zama a gidan ta kuma saka ni a makarantan gwamnati ta Shehu Garbai da ke nan kusa da gidan. Maigidan na da kirki sossai wanda daga bisani ma ya canja mun makaranta zuwa na kudi da ya'yan shi ke zuwa wanda kanana ne duk na girme su matar ce dai ban san meye na tare mata ba ta kafa mun kahon zuka har mijin ya gane. Watanni biyu da suka wuce ne bayan result din mu na gama secondary school Allah ya yiwa Hajja rasuwa bayan yar gajeruwan jinya" dai dai nan ta kuma fashewa da kuka, babu wanda ya ce mata uffan har sai da tayi mai isan ta sannan ta cigaba kaman haka "bayan komai ya lafa ne matar gidan ta ce sai in maye gurbin Hajja in zama mai girkin gidan, maigidan kuma ya ce sam sai dai a nemo wata ni admission zai nemo mun in tafi jami'a ita kuma ta ce sam bata ga abun ta haka ba. Sun dade suna rikici a kan hakan sai jiya ne ya ce shi ya fasa aure na ma zai yi ay in na zama matar shi bata isa ta hana shi saka ni a makaranta ba. Ai kuwa haukacewa ta yi a gidan dan jarkan kananzir da ashana ta dauko ta ce sai ta hada mu duka biyun ta kona, da kyar aka hadu da masu gadi aka rufe ta a daki sannan ya fita dan dauko yayar ta da take garin nan wai ta zo tayi mata magana wanda dan bai sani bane kawai amma ita take kara zuga ta ma. Shine na hada dan abun da nake da shi a gidan nima, ana shiga masallaci sallan isha na bar gidan. Gwanda in shiga duniya da a salwantar da rayuwa na a banza. A garin haka ne ina tsaka da tunanin inda na nufa har ka buge ni". Dukkan su sun tausaya mata duk da ita Mamee the lawyer in her ya ki barin ta ta yadda da labarin hundred percent amma sai bata matsa ba ta kyale dan har ga Allah yarinyan ta bata tausayi tabbas dan akwai mishkila a rayuwan ta. Dan haka sai ta cigaba da tausan ta tana mai nuna mata ay da na kowa ne har ta sassauta kukan nata sannan Mamee ta kalli Jamal ta ce "taso mu je mu gana da likitan ta".

A zahirin gaskiya Mamee ta yi haka ne dan su fita su tattauna da dan ta cikin sirri a kan makoman yarinyan, inda Jamal ya nuna zai tafi da ita Abuja ta zauna gidan shi a hankali a cigaba da cigiyan yanuwan ta amma Mamee ta nuna sam ba zai yiwu ba saide ko ita ta tafi da ita Kaduna a hankali ta cigaba da binciken ta har su gano gaskiyan ta da kuma dangin ta dan haka a take ta ciro wayan ta ta kira mijin ta. Ringing daya na biyun Dalhatu Kurfi ya dauka yana cewa "Allah ya ja da ran uwargida, Mamee na Mameen yara" ta ce "Daddy baka yi bacci ba?" ya amsa "ay ko nayi dole in tashi in ansa wayan ki Fatima, in ce dai lafiya tunda an riga an ce mun good night" ta ce "lafiya lau daddy magana ce dai zamu yi da kai ni da Jamal, let me put the phone on speaker" ya ce "toh bismillah" A take suka labarta mishi komai har zuwa kan decision din Mamee tukun suka dan tsahirta dan jin abun da zai ce. Sai da tsohon sojan yayi tsam da ran shi cikin tunani tukun daga bisani yayi amanna da zancen a kawo ta Kadunan inda yake nunawa jamal shi fah dan adam ba abun yadda bane, sannan su yara ne da shi da matar shi gwanda dai can Kadunan inda Za'a saka mata ido. Dan haka Mamee ta ce zata jira sai an sallamo ta daga asibitin kafin su dawo, yayi murmushi ya ce "watau da ni da ya'ya na kadai zaku bari a gidan, kin san Nana ma gobe ne tafiyan ta" sai a nan ta tuna Aunty Nana ma tafiya zata yi zuwa Texas din kasan America course din tsawon wata shida da wajen aikin ta suka tura ta. Ta ansa "Hakuri zaku yi yallabai ay ta kusan warkewa".

Assalamu alaykum everyone, barka da Juma'ah! Decided to bless you with goron Juma'ah today. So Ameetah can lie? Chaiii! Anyway i don't blame her, desperate situations calls for desperate measures ay, yanzu ba gashi zata cilla garin kaduna ba bayan ko Benisheikh bata taba wucewa ba. Who's ready to follow her on her journey to KD? Oya tighten your seat belts, you're on for a wild ride just get your tickets from votes and comments dot com and you'll be joining us on the ride. I didn't forget my promise so here's a list of a few books you can read before the next update even though i didn't get enough votes and comments. I promise you won't regret reading any of them.

Maimoon, Aisha Humaira and Diyam by MamanMaimoon

Auren soyayya and Rikon sakaina by maryamtalba

Batul byphartiemarhk

Tazarar da ke tsakanin mu by Ummu-abdoul

Sawun barawo by Noorieyyah

Kundin kaddara ta by huguma

    All these 10 are completed stories but I'll give you a bonus one kina raina by sawwama14 she updates regularly.

AMEETAHWhere stories live. Discover now