chapter eleven

103 10 2
                                    

       A zaune suka same ta a kasa bisa sallaya da dan karamin Qur'anin ta a hannun ta tana karantawa yayin da sister Nse ta maida hankalin ta kan kallon wani TV program da daga gani ta saba bi ne, tun da ta ga Nse ta maida hankalin ta kan program din ne ita ma ta dauko quranin ta cikin jakar ta ta dukufa karantawa a sabili da ita tun can ma ba maabociyar kallon TV ba ce. To ina ta isa ta shiga inda TV din yake ma balle ta kalla? A ce ma dai an bar ta ta kalli TV din, toh ina ta ga lokacin kallon tana can tana fama da uban aiki?
       Da sauri ta kai aya ta rufe Quranin jin suna gaisawa da sister Nse tare da tambayan ta yaya mai jikin? Ta ansa da sauki sannan ta yi excusing din su ta fita ko dan su gana da yar uwar su cikin sirri ne ko kuma dan ta koma inda zata kalli program din ta with full concentration ne oho. A hankali ta dago kan ta suka hada ido da mutumin da ya kade ta daren jiya a take zuciyan ta ya buga da karfi, a ran ta tace "Al-khaliqu gwani, wannan mutumin ba dai kyau ba" dan gani tayi yanzu har ya fi dazu kyau, a hankali ta juya ta kalli matar da suka shigo tare mai kama da shi sak wacce da gani mahaifiyar shi ce ko kuma yar shi ta jini, ta kara cewa cikin ran ta "ashe ga inda ya samo kyaun". Da sauri ta duka ta gaida matar, ta ansa mata cikin fara'a da sakin fuska Tare da tambayan ta jikin ta ansa da sauki sannan ta juya ta gaishe shi shima ya ansa yana mai kokarin janyo kujeran da ke bakin gadon ya ajiye a gaban matar tare da cewa "ga wuri zauna Mamee" sun cigaba da tambayan ta yanayin jikin ta da kuma yadda suke kula da ita a asibitin, ta tabbatas musu komai na tafiya amintace tukun daga bisani yayi mata umarnin ta tashi ta dawo kan gadon magana zasu yi na sossai. Ta mike sambal looking so pale and innocent ta zo ta haye kan gadon yayin da yake tsaye haikan a bakin gadon tamkar magen da ya rutsa bera a lungu yana mai kare mata kallo a ran shi ko yaba kyaun ta tare da innocent looks din ta yake. Yayi gyaran murya sannan a hankali but sternly ya ce "Ameetah, kin ga ni ba'a gari nake zama ba, bikin amini na ya kawo ni an kuma gama so zan koma inda na fito a gobe in Allah ya kai mu dan haka kiyi hakuri ki gaya mun number din wani naki in mika ki kafin in tafi". Kukan dai da baya so shi ta saka, walau dan ritsatan da yayi ne, a'a ganin kukan ya karbe ta dazu ne ya sa ta yi yanzun ma sai Allah. Shiru yayi kawai cikin takaici yana kallon ta sai Mamee ce ta mike daga inda take zaune ta wuce shi zuwa bakin gadon ta zauna sannan ta kwanto da Ameetahn a kafadun ta tana mai bata baki gami da cewa "yammata hakuri zaki yi kiyi magana in ma kun samu sabani ne da iyayen ki ay sai muje a daidaita ku, ay shi komai na duniya dan hakuri ne"
      Ameetah dai kuka take yi a jikin Mamee, kuka ne na rashin makama da rashin abun fada, a wani gefen kuma kukan dadi ne na yau ita ake rarrashi haka ana gayawa kalamai masu dadi wai dan ta ji sanyi a ran ta? Ashe akwai ranan da za'a lallashe ta itama kaman mutum ba hantara? Abun mamakin ma wai wata mata ce da bata taba gani ba a rayuwan ta sai yau dinnan ke rarrashin ta. Wannan mata fara sol, yar gaye da ba abun da ke tashi jikin ta sai kamshi ne ke rarrashin ta? Shi kuwa Jamal tun yana jin haushin Ameetah har ya koma jin tausayin ta. Bai san a garin yaya ba sai ji yayi babu abun da baya son ji irin kukan nata dan wani irin sukan zuciyan shi kukan nata yake yi, ji yake yi tamkar Mameen ce bata iya lallashi ba, kaman ya karbe ta a hannun Mameen ya lallashe ta da kan shi, amma a hankali a cikin hikima da dabaru irin na Fatima Kurfi (SAN) Ameetah ta sassauta kukan ta fara basu labarin da itama da kan ta bata san ta ina ya fito ba bata kuma san ta iya karya ba sai yau dinnan kaman haka...




Assalamu alaykum everyone! Eidukum mabarak wa ayyamukum sa'eda wa kulli aamun wa antum bi khayr. Taqabbalal-allahu minna wa minkum. Da fatan duk mun yi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana yasa ibadun mu karbabbu ne ya biya mana bukatun mu na alheri ya kuma nuna mana karshen wannan annoba. Short chapter? I know, i promised you goron sallah so i decided to deliver no matter how little. Honestly, kuna kashe mun jiki na difference din da nake gani tsakanin yawan readers da kuma votes da comments din ku, let's make this interactive please, in son jin ra'ayoyin ku. How many of you ke son jin labarin Ameetah? Na fara typing next chapter but ku zaku kara mun kwarin guiwan posting muku shi da wuri. Plus i told you guys I'm an avid reader koh? meaning i have a stack of good books both on and off wattpad, in ga ruwan comments ku ma in yi muku ruwan reccomendation din hadaddun littafai ku yi chilling da su a lockdown din nan. Deal?

AMEETAHWhere stories live. Discover now