chapter five

337 56 15
                                    

      Jamal Dalhatu Kurfi, a yanzu haka dan matashi ne me kimanin shekaru talatin da daya da 'yan watanni a duniya, kallon farko ka mishi Dalhatu Kurfi ne sak, dan wannan ginannen jikin da kuma faffadan kirjin gami da kasaitaciyar takun duk na tsohon sojan ne, amma a fuska ba abun da ya bari na mahaifiyar shi. Kama daga lumsassun idanun, da dogon hancin, har Jan tattausan labban, zuwa bakikirin gashin da ya saisaye kan shi. Farin kalan Hajiya Amna ne ya hadu da bakin General Kurfi ya bashi wani unique color din da ba zan iya kiran shi chocolate ba sai dai in ce caramel color.
      Tabbas wadannan features din su suka yi attracting khadijah Bello Numan ko da ta fara daura idon ta a kan shi, suka kuma saka ta take Jin har yau babu namiji Irin shi. Jamal ya hadu da ita ne a university of Maiduguri inda yake degree din shi a business management a lokacin.
      Asalin khadijah watsatsiya ce, Dan mafarin zuwan ta Unimaid ma a dalilin korar su da aka yi a wani university da ke Kuala Lumpur din kasar Malaysia ne ita da cousin din ta Surayyah akan drugs. Bayan mahaifin ta yayi rehabilitating din su ne ya turo su Unimaid. Ta yi kukan, ta yi fushin, ta yi lallashin akan mahaifin ta ya raba ta da wannan jami'an Amma ya sha alwashin ba ita ba karatu a kasan waje kuma sai hutu, amma daga wani ranan Tuesday ne a 2nd year din su tayi hamdalan zaman ta a Unimaid din.
      Ranan ta faro ne kaman ko wacce rana, Dan sun fito ne daga lecture ita da clique din ta wato Surayyah, Suwaiba Jada da Zubaida Gumel. Dai dai sun fito bakin SMS building inda tayi parking motar ta suka ga taron students suna kallon wasu 'yan Mata biyu suna dambe. Kallo daya ta yi musu ta dauke kan ta kasancewan bata fiya shiga abun da bai saka ta ba sai Surayyah ce ta tanka "su kuwa wadannan meye ya musu zafi, dambe a zafin ranan nan" Zubaida ta ansa "Jin dadi" har sun kai motan, Suwaiba 'yar giringidishi ta janyo Surayyah tana cewa "ai kuwa yau sai na ji kwaf" tare da nufan wurin taron, Zubaida ta ce "Allah dai ya sauwaka da gulma' khadijah koh dan haushi ido kawai ta zuba musu. Minti kadan bayan nan sai ga su sun dawo, Suwaiba ta kalli Zubby ta kwashe da dariya ta ce "guess meye cause din fadan?" Ta kalle ta a kaikaice cikin jin haushin dariyan da aka yi mata ta ce "ni Allah musuru ne? Yaya za'a yi in Sani?" Ta ce "haba 'yar uwa maida wukan, mutumin ki ne JD Kurfi and the annoying part is wai babu wacce ma ya San tana yi a cikin su" Zubaida ta Ja wani tsaki ji kake tsuuu... ta ce "Dan iska, wai shi JD din nan da meye yake ji ne?" Surayyah ta ce "meye kuma ya hada Zubby da da shi zaki ce wani mutumin ta, and who is this JD da bana rabo da Jin sunan shi in this school?" Suwaiban ce dai still uwar Baki ta ansa "Zubby ma ta taba falling victim din masoyan nashi daga bisani na raka ta muka gaya mishi amma kiri kiri ya nuna he's not interested" sai a lokacin uwar Jan ajin khadijah ta yi magana "zan so ganin wannan JD din" Sury ta ce "ai informant din namu ya ce yana nan  wajen restaurants din nan, da aka je aka gaya mishi abun da ke faruwa ma cewa yayi sun ga zasu iya ne." A take aka yanke shawaran su je a ga Jamal.
      Daidai student centre suka yi parking a sabili da opposite yake da jerin restaurants din da ke complex. Suwaiba ce ta tsegunta musu shi ne a dai dai bakin kofan peace and love restaurant, inda abokan shi Zannah Abba kyari da Umar Agid ke zaune kan wasu kujerun roba daga gefe. Kallon farko da khadijah ta mishi sai da ta ji wani abu dam a kirjin ta tsaban cikar zati, kwarjini da kamalan Jamal din. Dariyan da yayi a dalilin wani abu da abokan nashi ke fada Wanda ita din ba ji ta yi ba ne ya Kara kidima ta a sabili da pure white teeth din da suka yi mata sallama suka kuma karawa fuskan shi Dake kunshe da wani bakin saisayayyen gashi da ya taso tun daga kan shi, ya bi gefen fuskan shi har zuwa haban shi kyau. Tsaye yake haikan a daidai kofan restaurant din sanye da Levi's jeans da bakin t-shirt samfurin Giorgio Armani mai dauke da jan rubutu kaman haka 'Danger! Stay 50 feet away from me'. Karan sigari ne a hannun shi na hagu yayin da gwangwanin power horse ke rike a Na daman. Har suka ratsa shi suka shige restaurant din bai ko lura da su ba sai hiran shi yake yana kwasan dariyan shi hankalin shi kwance.
      Bayan sun bada order din su ne Sury ta kalle su ta ce "tirkashi! Ai da ban San halin shi ba nima babu abun da zai hana ni falling for him, Gosh! He's handsome!" Suwaiba ta ce "umh umh, he's unique!" Khadijah ta yi dariya ta ce "Kar ku damu, we will know how to handle him" dukkan su ido suka zuba mata, ta lumshe idon ta a hankali ta gyada kan ta ta ce "zaku gani ai"

Yayyy! Double update! I know, goron juma'a Na baku. Hope nima zaku Bani with lots of votes and comments. I'll seriously like to know what you people are thinking about the story duk da ba nisa muka yi ba, yay or nay? it's only my dearest haphsertu that is commenting, abi Na only she dey read the book ne? Yau ba rowa both pages are for you my darling. Next chapter we find out what khadijah means by 'handle him', in ji ra'ayoyin ku please before the next update.

AMEETAHWhere stories live. Discover now