chapter six

269 22 3
                                    

      Ai kuwa sai da ta bari bayan kwana biyu, yana fita a makaranta ta bi bayan shi da nata motar, sai da suka kai dai dai junction din Lagos street ta zo a guje ta hada gaban nata motar da bayan nashi ji kake garammm. Nan da nan kuwa hankalin kowa yayi kan su aka fara taruwa, shi ma saukowa yayi don ganin ko mahaukacin ina ne ya zo ya buga mishi mota yana tsayen tsayen shi.
      Ai kuwa mutumiyar taku nan da nan tayi pretending she's in shock, don maganan duniyan nan anyi mata amma bata tanka kowa ba sai bin su take da wani Irin kallo. A nan wasu daga cikin 'yan kawo daukin, ko in ce 'yan gulma, 'yan bani na iyan suka fara gulman ko dai kurma ce. Wasa wasa fa abun ya Fara bawa Jamal tsoro, inda ba shiri ya rufe motar ta ya jefa ta da 'yar handbag din ta a tashi motar da shike bayan ce ta bugu yayi UMTH da ita. Kafin su karasa ya Kira Shettima cousin din shi yayan Zans a waya da shike Dr ne a asibitin, ya ce su hadu a accident and emergency.
      A hankali Drs din suka samu ta Fara musu magana, sannan suka ce babu wani serious abu shock ne kawai don haka ta samu ta huta sossai suka dan bata sedatives. Ita ta yi mishi kwatancen gidan kanwar baban ta da suke zama ita d Surayyah a barracks. Sai da yayi parking motar shi a kofan ya juyo a hankali yana kallon ta, ita din ma kuwa shi take kallo, a ran shi yana mai jinjina tsantsan kyau Irin nata, a hankali ta bude bakin ta tace
"nagode da taimakon da kayi mun" shima cikin wani dan murya can kasa ya furta "Don't mention" ta ce "and I'm sorry about the car, in ka kai wa mechanic din ka ya gyara ka turo mun da bill din please" murmushi ya yi ya ce "Kar ki damu da wannan, makullan motan ki ma na hannu na zan yi kokarin ganin an kawo miki motan gida."
      Har ta bude motan zata fita ya ce "kin yi mantuwa" tana juyowa ko ta gan shi rike da ledan magungunan ta, ta kai hannu zata karba Amma ya ki sakin su, cikin husky muryan sa da ke juya mata kwanya ya ce "I hope dai baki cikin masu kin shan magani" itama ta langwabar da kai cikin salon shagwaba ta ce "ba abun da na tsana Irin magani" ku ji fa, wacce aka raba da drugs da kyar ke fadin haka. Bai ansa ta ba illa hannu da ya mika bayan motan ya dauko roban ruwan faro ya bincire marufin ya ballo magungunan sannan ya mika mata su ya ce "to yallah" sai da ta yatsina fuska a dole bata so tukun ta karba ta hadiye. Ba tare da neman izini ba kawai sai sa hannu yayi ya dau handbag din ta da ke bisa cinyar ta ya zuge zip din ya hau dubawa, "ba fa a duba jakan mata" ta ce da shi a raunane, sai da yayi wannan munafikin smile din nashi tukun ya ce "and what do you expect zan gani da ban taba gani ba a cikin jakan naki" shirun da ta yi ne ya sa shi cigaba "kayan kwalliya ko  kuma sanitary towels" still kin kula shi ta yi har ya karaci dube duben shi ya samo abun da yake nema watau wayan ta ya samu ya dau number din ta tukun ya maida ya zuge zip din ya ajiye mata jakan inda ya dauka wato kan cinyar ta ya ce "ki shiga ku ci abinci ki kwanta ki huta I'll call you in lokacin maganin ki ya yi" ba tare da ta kara bi ta kan shi ba ta sauka ta tasamma cikin gida, sai da yaga shigewar ta tukun ya tada motan shi. yana mai mamakin kan shi da kan shi. Straight up wajen mai gyaran shi ya je ya bada motan shi ya kuma tura yaron da zai je ya dauki motar Khadijah zuwa wajen gyaran sannan ya dau drop zuwa gidan kawun shi kuma aminin baban shi watau Brigadier Abba Kyari Kukawa (rtd) da yake zama.
      Yammacin washegarin duk suna gidan Aunty Hajjo ita da clique din nata suna ta hira da mamakin encounter din ta da jamal din kuwa wayan dan halak din ya shigo yana mai shaida mata yana gate din su if she wouldn't mind. Dan a zahirin gaskiya kwana yayi, ya kuma wuni yana makale da ita a ran shi, sai kuma da ya hada da tsantsan dauriya dan tun da ya bar ta babu abun da yake so illa ya kara ganin kyakyawar fuskar ta, ba karamin yaki yayi da zuciyan shi ba ya iya ya jira aka gama gyaran motocin su aka kawo mishi da yamman nan dan ya samu excuse din zuwa wato kawo mata motar ta. Shi kan shi mamakin kan shi yake dan mace bata taba shiga gaban shi ba. A ganin shi ba wani abu bane face distraction, su kuma hana maka focus. Yanzu haka cousin din shi Teemah kanwar Zans ta bi ta tada mishi hankali ita a dole son shi take ga shi Mamee ta goya mata baya har tana ikirarin ta yi wa dan ta mata 'yar wan ta kuma takwarar ta.
      Daga nan suka fara da zamowa "friends" a cewar su duk da dai a zuciyan ko wannen su ba haka bane, dan duk inda ka ga Jamal to a nan zaka ga Khadi in ji shi da fada. Cikin unimaid kowa mamakin JD Kurfi yake. To ba'a dade ba yayi graduating bayan sun tabbatas wa juna son da kowa ke ma dan uwan sa. Ko service bai yi ba admission din shi ya fito a Warwick business school London inda ya je yayi masters din shi ya dawo yayi service sannan ya fara aiki da central bank of Nigeria a nan Abuja. Duk wannan shekarun suna tare da Khadijah on and off, dan wani lokacin in ta nuna mishi halin lalaci da rashin hankalin nata share al'amuran ta yake yi, amma da shike tana son abun ta a hankali zata lallaba shi su koma.
      A zahirin gaskiya Mamee bata so auren Jamal da Khadijah ba walau ko dan kin 'yar wan ta da yayi ne koko rashin tarbiyyan Khadijahn ta hango mishi, Allah masani, ko ma meye dai dole ta hakura tunda dan nata ya nuna shi fa abun da yake so kenan, sannan kuma uban shi ya bashi goyon baya dari bisa dari.
      Sai da zama ya hada su ne bayan bikin Jamal ya fahimci halayen Khadijah, da farko dai lalataciyya ce na kin karawa dan ko tsintsiya bata iya dagawa da sunan ta tsaftacce wuri ba, inda ta kwanta kuwa sai dai mai aiki ta gyara, gashi ko ruwan zafi bata iya tafasawa ba in ya wuce na tea a kettle balle a yi zancen girki, abun da za'a ce ta iya ta kuma gwanance a kai babu irin kwalliya da kyalle kyalle. Gashi ba ta son haihuwa ko na miskala zarratin, dan wadannan guda biyun ma da kyar da sudin goshi ta haifa mishi su bayan ganin bacin ran shi tsagwaro a cikin su na farko da ta zubar a cewar ta wai bata shirya haihuwa ba a lokacin. Daga nan ne suka yi yarjejeniyan ita 'ya'ya biyu kawai zata haifan mai, dan bayan haihuwan Aman dan ta na biyun ma cire mahaifan tayi kwata kwatan shi. Toh shi kuma Allah yayi shi mutum ne mai son yara, dan in ka gan shi a cikin su yana wasa da su kai ka ce shekarun su daya ne. Shiyasa ya'yan sisters din shi zaka ji kowa na uncle Jamal. Kalman raino kam Khadijah bata san shi ba, dan da ta haife ta gama nata kenan, sauran duk aikin nanny ne, cikin ya'yan kuma babu wanda ya taba dandana nonon uwar shi dan tsaban gayu, duk sun girma ne da imported kuma tsadaddun madara. Ganin hakan ne ya sa shi rokon Mamee alfarman daukan Anty Umma zuwa gidan shi dan kula da al'amuran gidan da kuma yaran da uwar bata tsaya ta kula da ba.
      Duk abubuwan da Khadijah ke yi ya samo nasaba ne da irin tashin da ta yi, dan ko a gidan su rayuwan turai da karya ziryan shi ake shiryawa. Bello Sayyadi Numan shi ne mahaifin ta, tsohon dan siyasa ne da aka dama da su jiya ake kuma damawa da su har zuwa yau a kasa, a zamanin da yake gwamna ne Gongola state tun ma kafin ya zama Adamawa ya auri mahaifiyar su Khadijah wacce asalin ta christian ce 'yar kasar Sierre Leone mai suna Nadine wacce daga bisani ya musuluntar da ita ta koma Nadia. Zunzurutun rayuwa da Nadia ta sa a gaba a ciki 'ya'yan suka tashi dan haka ne ma tarbiyya ko kankani basu tashi da ita ba.
      A yanzu haka shekaru shidda da auren su hakuri zalla yake yi da Khadijah. Duk da babu abun da ya ragu, sai ma wanda ya karu duk inda ya shiga dai 'yammatan na nan na bibiye da shi tunda ya hada komai da za'a so shin, kyau, cikar zati, nutsuwa da kamala ga uwa uba 'ya'yan banki. Dan stock broker ne babba a Abuja mammalakin shahararren Hallmark stock house dake Adetokumbo Ademola crescent a wuse 2.





Assalamu alaykum my darlings, barkan mu da sallah, da fatan an yi sallah lafiya? Allah ya sa ibadun mu karbabbu ne, Allah ya maimaita mana. A million appologies for the late update, it was due to some unforeseen circumstances way beyond my control. Duk na ga sakkonin ku na kuma gode da adu'o'en ku. Next chapter we go straight back to our story in sha Allah. We are meeting at some new characters, who is excited?
    

AMEETAHWhere stories live. Discover now