chapter seven

240 24 4
                                    

Borno, maiduguri. That same friday 7:30 pm. Damboa road.

      Kwance take a kan wani tabarmar eni da yaga duniya dan duk robar ta zazzare daga gefe gefe sannan kuma a huhuje take ke kya ce reza aka sa aka yanke guraren, shi kan shi pillown da take kwance a kai dunlop din ciki zazzagowa yake sakamakon yagewan da rigar fulon tayi. Babu komai a dakin in ka dauke shimfidan ta da ke dandaryan simintin dakin sai bagcon kayan ta dake can lungu sai kuma fankan dake ta gudu a saman dakin tana aikin ta na bada iska da ta kura wa ido. Kallon farko zaka zaci fankan ta ke kallo amma a zahirin gaskiya tunani ne fal a zuciyan ta, wanda bai rasa nasaba da auren dolen da mahaifin ta ya dau alwashin daura mata a washegarin ranan da dan dakin matar baban nata, wanda a gaban ta mahaifin nata ya rantse cewar mutuwan ta ne kadai zai hana daurin auren nan a goben. Ita a da ta dauka aure shine tsanin da zata taka dan saduwa da farin cikin rayuwa da ta dade tana burin samu, ta dauka shine zakin da zai raba ta da dacin gidan mahaifin ta ya raba ta da ukuba gami da wahalan da take fuskanta a hannun matan uban ta, ta dauka shi ne means din da zai sada ta da mahaifiyar ta, sai gashi ya zamanto wani hanya na dada tabarbarar da rayuwar ta. Tabbas auren ta da Mala hatsari ne babba dan wulakancin da zata fuskanta a wajen shi ta tabbata sai ya zarce na gidan mahahaifin nata.

      A take wani tunani ya fado mata, tabbas in ba'a gan ta ba ai ba za'a daura auren ba, da wannan ukuban ai gwanda ma ta shiga duniyan, me kuma zata gani ma da bata riga da ta gani bane? Kaman an tsikare ta ta mike, sai da ta shiga bandaki ta kama ruwa ta dauro alwala ta yi sallah raka'a biyu, ta dade tana rokon Allah ya sa abun da take niyyan yi alheri ne ga rayuwan ta, ya kare ta ya kuma tsare ta daga sharrin dukkan abun ki. Ta mike ta cire hijabin sallahn ta, doguwa ce sambal da irin tsayin dogayen matan bare bari, sannan tana da hasken fata tare da kyaun da wahalan da take ciki bai hana bayyanuwar shi ba. Riga da zanin atamfar Nichem ta ciro daga bagcon nata ta sauya zulumbuwar jar rigan dake jikin ta da ta yini tana aikin gida dashi ta daura hijabin ta mai kalar furannin jikin atamfar watau kore a kai. Sai da ta jira aka shiga sallahn isha a masallacin da ke kofar gidan tukun ta fito, as usual tsakar gidan ba kowa, duk yan matan gidan na can tare da iyayen su mata ana koya musu annamimanci mazan kuma an tafi masallaci, sai can anjima zaki ji ana Ameetah dafa mun indomie wannan na hado mun shayi wannan na wa zai ci jagwalgwalon miyan yakuwan ki, ta ce a ran ta duk yau kwa san mai yi muku ai. A bakin gate ta hadu da Ba Ari maigadi zaune kan bencin sa yana kokarin saito tasha a rattattakakiyar rediyon shi ta shekara dubu annabi dada cikin barbarci ya ce "yanyi, nda ro lenemin" watau uwa ta ina zaki ne? Ta ce "Ba Ari Ya'ajja ce ta aike ni gidan aunty Yasato" cikin hausan shi mai cike da accent in barbarci ya ansa "a dare wannan? Shi hajja ba zai bari sai gari ya waye ba, to sai ka dawo" ta ansa shi da to. A ran ta tana mai cewa zaku ga wanda zai dawo muku wannan gidan ai. Da sauri sauri ta fita daga layin gidan su ta bi titi ta mike sambal tana tsoron kar a farga bata gidan a biyo sawun ta. A son ran ta ta bar garin gabadaya toh amma a daren nan ina zata nufa? Ai ko meye ma dai cikin hasken rana ido na ganin ido ya fi, to ko dai ta tafi wajen Kaltume Algoni kawar ta ne ta kwana in yaso in gari ya waye ta shiga motan wani garin ta kara tunanin to wani gari ma zata tafi ne, wata zuciyar ta ce mata katsina mana da ina zaki? Ta yi tunanin kuma to ai za'a iya zuwa neman ta gidan su Kaltume din tunda an san kawar ta ce. Bata san ma tana tafiya a tsakiyar titi ba tsabagen tunani sai da ta ji an birkita mata kwanya da wani mahaukacin horn amma kafin ta ankara babu gaban jibgegiyar motar ta banke ta.

*      *      *      *       *      *      *      *      *

Ran shi bace yake sakamakon wayan da ya iddasa da Anty Umma, yana tambayan ta Lafiyan gida a nan ne yake dada tabbatar da cewa Khadijah tayi tafiyar ta duk da jadadda matan da yayi kar ta tafi. Fitowan shi kenan daga Emperial guest inn da yayi masauki zai je su hadu da su zans a gidan shi kafin su dunguma wajen wushe-wushen da ake gabatarwa a gidan su amaryar. To wai shi wani irin aure ne ma yake yi ne ya ce a ran shi, a ce mace sam baka isa ka saka ta ba baka isa ka hana ta ba. And the most annoying part is that bata girmama kowa nashi, ba iyayen ba, ba 'yan uwan ba, duk da dai ya san basu cika gaya mishi rashin mutuncin da take musu ba ai still ya sani dan ya lura Hadiza yanzu ta gwammace ta same shi office ko suyi magana a waya da ta je gidan shi har ya yi korafin rashin zuwa gidan da take yi har ya gaji amma sai dai ta ce ai zuwa gidan gayun ku dinne Ya Jamal sai an shirya. Shi dai ya san ba sakaran namiji bane dan haka zai yi putting a stop to abun. Bai ankara ba ya ga an sha gaban shi, mace ce dan yana ganin koren hijabin ta ta hasken fitilun motar, hasbunallah wa ni'imal wakeel ya ambata tare da danna mata horn amma ina duk wani kauce kaucen shi sai da ya bige ta.


      Hello lovelies! Barkan mu da juma'a, here's a short update. we finally meet Ameetah. And what's with Jamal and car accidents? We'll find out soon in sha Allah.

AMEETAHWhere stories live. Discover now