PAGE ONE

314 14 4
                                    

                               🅿️1️⃣






BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM!!.

Dukka yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki, Ubangijin sammai da ƙassai, Ubangijin talikai, Ubangijin Al~arshi me girma.

Dubun salati su tabbata ga shugaba kuma fiyayyen halitta, Annabinmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.

Wannan littafin mallakar Ouummey (khairert) ne, ba yarda wata ko wani su juya min littafi ba ta kowace siga bata reda yardata ba, duk wanda yai gangancin yin hakan kuwa zai haɗu da fushin hukuma.

Wannan labari ƙirkirarren labari ne dana ƙirƙireshi bisa fasaha da baiwar da Allah yai min, kamanceceniyar suna ko halayya akasi ne kuma arashi ne, fatan za'ayi haƙuri da hakan.

Gareku masoyana masu bibiyar rubutuna da nuna min ƙauna da soyayya, to gani na kuma dawowa gareku cikin salon rubutuna da ya bambanta dana kowa.

Littafin ABOTA CE KO SOYAYYA ya zo da salon da yasha bambam da duk littattafai na na baya, zaku nishaɗantu kuyi farin ciki har ma da dariya a cikin sa, i promise you'll enjoy it kamar ko ma fiye da yadda kuka yi enjoying SARAKI da izinin Ubangiji.

Kindly add to your library, vote, and comment on every page for your comment is what keeps me going till I reach the extreme end😍😂.



NOTE:
_FREE BOOK NE_.









____________________📖 Da sauri sauri take taka steps ɗin benen har tana haɗa bibbiyu, bata san ya akayi bacci yaci ƙarfin ta har ta makara haka ba bayan yau ɗin ce ranar da zata fara cikakken aikin ta da bata san yin wani kuskure a cikin sa balle har ta samu matsala da Maah dan se da ta nanata mata fiye da yadda zata iya tunawa kan ta kula.

Cikin wani medium falo da ya tsaru gwanin sha'awa ta bayyana bayan steps ɗin sun ƙare, girgiza kanta tayi ganin yadda falon yake kaca kaca alamar be ga gyara ba yau sedai ba wannan ne a gaban ta ba, gaban ƙofa ɗaya tal dake cikin falon ta ƙarasa ta shiga ƙwanƙwasawa sedai tsayin lokaci ba amsa hakan yasa ta murɗa handle ɗin kawai ta shiga.

Kamar yadda ta tsammata kwance ta same ta kan gado rungume da ƙaton teddyn ta ta bararraje se sharar baccin ta take hankali kwance, hannu ta sa ta shiga tapping santala santalan cinyoyin ta dake waje sanadin tattarewar da rigar baccin jikin ta tayi dan har ana ganin guntun wandon baccin jikin ta, juyi tayi tana turo baki alamun an dame ta kafin ta cigaba da baccin.

Wannan karon da ɗan ƙarfi matar ta ke tapping ɗin ta tana kiran sunan ta

"Pretty, prettyn papi".

A hankali ta buɗe kyawawan sleepy eyes ɗin ta ta zuba kan matar kafin a hankali ta furta sunan ta

"Mama Gajiiiii".

Ta ja sunan alamun fa bata ƙoshi da baccin ba, da sauri Mama gaji ta saka hannu cikin son taimaka mata ta tashi daga kwancen da take tana mata magana

"Naam prettyn papin ta, daure ki tashi kinga mun makara bayan kamata yayi ki fita tun nine gashi yanzu haka har da minti biyu".

Zama tayi sosai kan bed ɗin tana kallon mama ta shiga magana in a pleading tone da muryan ta dake cike da bacci

"Kice mata na tafi kawai, Allah baccin be ishe ni ba, pleaaseeee mama".

Zaro ido mama tayi kafin ta maza ta sa hannu ta rufe mata baki sannan ta fara magana cikin yin ƙasa ƙasa da murya

"Kin san halin Maah ɗin ki fa, tana jin baki je ba zata hana ki komawa Boston, ko kin manta tace mana akwai cameras a ko ina na gidan nan, kinga zata san ƙarya muke, maza tashi muje kiyi wanka muna ta sake ɓata lokaci kinji".

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now