PAGE FIVE

74 8 1
                                    

🅿️5️⃣











__________________________📖 Fitowa tayi daga motar tana faɗawa sale yaje masallaci in ta tashi tafiya zata kira shi, da toh ya amsa mata ya juya mota yayi gaba.

Kallon gidan tayi ta sake kallan number gidan dan tabbatar wa, tana confirming ta nufi gidan ba tare da damuwa da yadda za'a ɗauki zuwan nata ba.

Ƙaramin gate ɗin ta tura tare da shiga compound ɗin da bashi da wani girma dan be fi ya ɗauki babur biyu ba, ƙofa ɗaya dake compound ɗin ta shiga tana doka sallama, ɗan tsayawa tayi jin ba'a amsa ba kafin ta kuma yin sallama da ɗan ƙarfi, wata dattijuwa da ta fito daga wata ƙafa hannun ta riƙe da buta ce ta amsa mata tare da faɗin

"A shigo mana".

A hankali ta shiga takawa har ta shiga tsakar gidan me matsakaicin girma tana sake ƙaramar sallama matar ta kuma amsa mata tare da mata sannu da zuwa.

D fara'a Deeyerh ta amsa mata tana zama kan daddumar da ta shimfiɗa mata kafin ta sauke jakar ta tana gaida matar

"Barka da rana Umma, ya gida?".

Itama da sakin fuska dattijuwar ta amsa mata da

"Lafiya lau alhamdulillah, sedai ban gane ɗiyar tawa ba".

Ɗan shiru Deeyerh tayi kafin ta fuskanci Umma sosai tana karyar da kai

"Baki sanni ba Umma, dama ƙara na kawo miki".

Da mamaki Umma ta maimaita kalmar ƙara tana tunanin ƙarar wa za'a kawo mata ita da bata da ƙaramin yaro a gaban ta, dan haka ta sake duban Deeyerh sosai

"Ƙarar wa kenan yarinya?".

Se da ta tura baki gaba kafin ta shiga zubawa Umma dalilin ƙarar

"Ƙarar ya Haydar na kawo Umma, nasan kin san wayar sa ta faɗi ko, to nice na tsinci wayar sedai na riga na taka ta har ta fashe shine fa se aka siyan masa irin ta a gidan mu dan kinga ai be kyautu in Bashi fasasshiyar ba bayan nice na fasa ko, to shine yace baze karɓa ba dan kawai na ɗan tsokane shi nace waya ta ce, kuma ma shekaranjiya yasa na ƙware amma duk na yafe masa saboda ashe sunan yaya Aliyu ne dashi, jiya kuma yace min mummuna nima nace shima ai mummuna ne amma ma na bashi haƙuri daga baya duk dan ya karɓi wayar amma yaƙi shine na zo na faɗa miki dan nasan zaki sa ya karɓa, ai yana jin maganar ki ko?".

Da kallo kawai Umma ta dinga binta tun da ta fara magana har ta ƙare, tunanin inda Haydar ya samo ta take se kuma ta tuno tace a makaranta ne, lallai wannan yarinyar daban ce dan bata taɓa ganin me hali irin nata ba, haɗiye mamakin ta tayi ta buɗe baki dan yin magana se kuma wayar Deeyerh ta shiga ƙara hakan yasa ta yi shiru dan ta sami damar picking call ɗin.

Ɗan ware ido tayi kamin tayi picking wayar tana kaiwa kunne, cikin ladabi ta shiga gaisar da Maah sedai tuni ta dakatar da ita

"Barka da rana Maah".

"Hold on dan bashi na kira ki ji ba, sale ya koma gida babu ke yace kin sa ya kai ki wani gidan cikin phase two, faɗa min wane gida kika je kuma me kika je yi and wajen waye kika je, kar ki kuskura ki fara min ƙarya dan kin san ranki se ya ɓaci".

Rawar da hannun ta ke yi yasa ta cire wayar daga kunnen ta ta saka ta a speaker tare da ajiye ta kan laps ɗin ta ta fara wa Maah bayani

"Mutumin da na faɗa miki ya yarda waya na tsinta a school ne na kawowa wayar gidan su saboda yaƙi karɓa kuma tasa ta ainahi ta fashe shine fa Mama gaji tace in Bashi irin ta Kuma ya ƙi karɓa shine na kawo ƙarar sa wajen maman sa, Allah ina gidan Maah ba inda naje yanzu ma na gama yi wa Umman bayani gata kuma a zaune".

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now